'Abin da Ya Sa Sarki Sanusi II Bai Halarci Jana'izar Buhari ba da Aka Yi a Daura'
- An gudanar da sallar jana'izar tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari a garin Daura da ke jihar Katsina
- Bola Tinubu, gwamnoni a Najeriya, yan siyasa da kuma sarakuna sun halarci jana'izar da aka gudanar da yammacin jiya Talata
- Wani na kusa da Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II, ya bayyana dalilin da ya sa basaraken bai halarci jana’izar Buhari ba
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
London - A yammacin jiya Talata 15 ga watan Yulin 2025 aka gudanar da sallar jana'izar Muhammadu Buhari a garin Daura da ke jihar Katsina.
Shugaba Bola Tinubu da mukarrabansa, manyan yan siyasa da sarakunan gargajiya sun samu halartar jana'izar da aka gudanar.

Source: Facebook
Wani na kusa da Sarkin Kano, Alhaji Muhammadu Sanusi II ya fadawa Punch dalilin da ya sa basaraken bai halarci jana'izar Muhammadu Buhari ba.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Aminu Ado ya samu halartar jana'izar Buhari
A gefe guda kuma, Sarkin Kano na 15, Alhaji Aminu Ado Bayero, ya halarci jana’izar tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari da aka yi a Daura da safiyar ranar Talata.
Mai magana da yawun Bayero, Abubakar Naisa, ya tabbatar da hakan, yana mai cewa sarkin ya samu rakiyar wasu sarakuna daga jihar Jigawa domin shaida ganin karshe ga tsohon shugaban kasar.
Ya ce:
“Eh, mai martaba Aminu Ado Bayero ya bar Kano da safiyar Talata zuwa Daura don yin bankwana, yana tare da Sarakunan Kazaure da Dutse.”
Basaraken ya isa Daura ne tare da mukarrabansa domin halartar birne tsohon shugaban kasar da ya rasu a ranar Lahadi a birnin London.
Hakan ya sa wasu ke tura tambayoyi kan rashin ganin Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II wanda ya tilasta makusantarsa yin bayani.

Source: Twitter
Musabbabin rashin halartar Sanusi jana'izar Buhari
Makusancin na sa watau Muhammadu Dallatu, ya shaida cewa Sanusi II yana halartar wani taro ne a London wanda shi ne dalilin rashin zuwa Daura.
A cewar Dallatu, Sarkin yana kasar Birtaniya ne kan wani aiki a hukumance kuma ana sa ran zai dawo Najeriya a yau Laraba 16 ga watan Yulin 2025.
Ya ce:
"Sarki ba zai halarta ba, Ma ba ya cikin kasa, ya tafi London kan aiki na hukuma, ana sa ran dawowarsa a ranar Laraba.’’
A ranar Asabar, Sarkin Kano Sanusi II ya halarci gasar 'Access Bank Polo' ta 2025 a Surrey, Ingila, inda aka gan shi tare da fitattun mutane ciki har da kocin kasar Ingila, Thomas Tuchel.
Jana'izar Buhari: Gwamna Radda ya zubar da hawaye
A wani labarin, kun ji cewa gwamnan jihar Katsina, Dikko Umaru Radda ya yi matuƙar kaɗuwa a wajen jana'izar tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari.
An yi jana'izar marigayi Buhari a mahaifarsa ta garin Daura da ke Katsina a ranar Talata, 15 ga watan Yulin 2025.
A lokacin jana'izar marigayin, Gwamna Radda ya gagara riƙe hawayen da suka taho masa lokacin da yake yi wa Buhari ganin ƙarshe kafin sada shi da Ubangijinsa.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

