Bidiyo: Yadda Gwamna Radda Ya Zubar da Hawaye wajen Birne Buhari a Daura
- Gwamnan jihar Katsina, Dikko Umaru Radda ya yi matuƙar kaɗuwa a wajen jana'izar tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari
- Marigayi Muhammadu Buhari dai an yi jana'izarsa a mahaifarsa ta garin Daura da ke Katsina a ranar Talata, 15 ga watan Yulin 2025
- A lokacin jana'izar marigayin, Gwamna Radda ya kasa riƙe hawayen da suka taho masa lokacin da yake yi wa Buhari ganin ƙarshe kafin sada shi da makwancinsa
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Katsina - Gwamnan jihar Katsina, Dikko Umaru Radda, ya samu halartar jana'izar tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari.
Gwamna Radda ya zubar da ƙwalla lokacin da ake shirin birne gawar tsohon shugaban ƙasan na Najeriya.

Source: Twitter
An birne Buhari a Daura
Tashar TVC ta sanya bidiyon yadda Gwamna Radda ya riƙa hawaye lokacin da ake shirin sada Muhammadu Buhari da makwancinsa na ƙarshe.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari dai ya rasu ne a ranar Lahadi, 13 ga watan Yulin 2025 a birnin Landan na ƙasar Birtaniya.
Marigayin ya rasu ne a wani asibiti bayan ya yi fama da ƴar gajeruwar jinyar rashin lafiya wacce ba a bayyana ba.
Gawar marigayin ta iso Najeriya da misalin ƙarfe 2:00 na rana, inda ta sauka a filin jirgin sama na Umaru Musa Yar'adua da ke Katsina.
Mataimakin shugaban ƙasa Kashim Shettima da wasu daga cikin iyalan Buhari ne suka yi wa gawar rakiya daga birnin Landan.
Mai girma Bola Tinubu da kansa ya karɓi gawar a filin jirgin daga hannun tawagar gwamnati ƙarƙashin jagorancin Shettima.
Bayan nan an wuce da gawar marigayin zuwa mahaifarsa da ke Daura.
Gwamna Radda ya zubar da hawaye
A lokacin da aka zo da gawar Muhammadu Buhari gaban kabarinsa, Gwamna Dikko Radda ya riƙa zubar da hawaye.
Gwamnan ya zubar da hawaye ne yayin da yake yi wa gawar tsohon shugaban ƙasan kallo na ƙarshe kafin a sada shi da makwancinsa.
Jana'izar Buhari ta yi jama'a
Ɗumbin mutane ne dai suka samu halartar jana'izar tsohon Muhammadu Buhari wacce aka gudanar a mahaifarsa ta Daura.
Shugaban ƙasa Bola Tinubu na daga cikin mutanen da suka halarci jana'izar marigayin.

Source: Twitter
Mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima, mataimakin majalisar dattawa, Sanata Barau Jibrin, gwamnoni masu ci da na baya na daga cikin waɗanda suka halarci jana'izar.
Hakazalika shugabannin ƙasashen waje sun samu halartar jana'izar tsohon shugaban ƙasan na Najeriya wanda ya rasu yana da shekara 82 a duniya.
Sarkin Saudiyya ya yi ta'aziyyar Buhari
A wani labarin kuma, kun ji cewa Sarkin Saudiyya, Sarki Salman bin Abdul'aziz Al Saud ya aiko da saƙon ta'aziyyarsa kan rasuwar tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari.
Mai kula da masallatai guda biyu masu tsarkin ya jajantawa mai girma Bola Tinubu kan rasuwar magabacinsa wanda ya bar duniya a ranar Lahadi, 13 ga watan Yulin 2025.
Sarkin ya bayyana cewa ya bayyana cewa ya kaɗu matuƙa bayan samun labarin rasuwar Buhari.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

