Duniya kenan: Yadda Aka Binne Gawar Muhammadu Buhari a Daura

Duniya kenan: Yadda Aka Binne Gawar Muhammadu Buhari a Daura

  • An sada tsohon shugaban ƙasan Najeriya Muhammadu Buhari da makwancinsa na ƙarshe a ranar Laraba, 15 ga watan Yulin 2025
  • Gawar Muhammadu Buhari dai an bi4ne ta ne a cikin gidansa da ke mahaifarsa ta Daura a jihar Katsina
  • Jana'izar marigayi tsohon shugaban ƙasan ta samu halartar manyan mutane daga ciki da wajen Najeriya waɗanda suka zo don yi masa bankwana

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Katsina - An binne gawar marigayi tsohon shugaban ƙasan Najeriya, Muhammadu Buhari a mahaifarsa da ke Daura cikin jihar Katsina.

Marigayi tsohon shugaban ƙasan an birne shi a cikin kabarin da aka gina a cikin gidansa na Daura a ranar Talata, 15 ga watan Yulin 2025.

An sada Buhari da makwancinsa na karshe
An binne gawar Muhammadu Buhari Hoto: @MSIngawa
Source: Twitter

An birne gawar Muhammadu Buhari

Tashar TVC ta sanya bidiyon yadda aka gudanar da birne gawar marigayin wanda ya rasu a ranar Lahadi.

Kara karanta wannan

Buhari, Sheikh Abubakar Gumi da wasu jagororin Najeriya 5 da suka rasu a birnin Landan

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari dai ya rasu ne a ranar Lahadi, 13 ga watan Yulin 2025 a wani asibiti da ke birnin Landan.

Muhammadu Buhari ya yi bankwana da duniya ne bayan ya yi wata gajeruwar jinyar rashin lafiya wacce ba a bayyana ba

Buhari ya bar duniya yana da shekara 82 inda ya rasu ya bar mata da ƴaƴa tare da jikoki.

Tinubu ya halarci jana'izar Buhari

Shugaba Bola Ahmed Tinubu da mataimakinsa, Kashim Shettima, sun haɗu da dubban masu juyayi wajen kai gawar marigayi tsohon shugaban ƙasan zuwa makwancinsa na ƙarshe.

Sun kasance tare da shugaban ƙasar Chadi, Muhammed Déby, da takwaransa na Guinea Bissau, Umaru Sissoco Embaló, da kuma Firaministan Nijar, Ali Mahamane Lamine Zeine.

Haka kuma, mataimakin shugaban najalisar dattawa, Sanata Barau Jibrin, gwamnoni masu ci da na baya, ministoci da dama na yanzu da na baya da sauran manyan jami’ai sun halarci jana’izar.

Kara karanta wannan

Hoton yadda Aisha Buhari ta rungume tutar da aka lulluɓo gawar mijinta ya ja hankali

An gudanar da sallar jana’izar a wurin saukar jirgi da ke garin Daura, inda marigayin ya fito, ƙarƙashin jagorancin babban limamin Daura, Sheikh Salisu Rabiu.

Gawar Buhari ta iso Katsina da misalin ƙarfe 2:00 na rana, sannan aka tafi da ita Daura ta hanyar mota da misalin ƙarfe 3:40 na rana.

An yi wa Buhari jana'iza a Daura
An binne gawar.marigayi Buhari a Daura Hoto: @MSIngawa
Source: Twitter

An harba bindigar girmamawa domin karrama Buhari daidai ƙarfe 5:32 zuwa 5:35 na yamma, sannan aka binne shi daidai ƙarfe 6:00 na yamma.

Kalli bidiyon a nan ƙasa:

Karanta wasu labaran kan jana'izar Buhari

Allah ya yi masa rahama

Muhammad Auwal ya shaidawa Legit Hausa ya yafewa tsohon shugaban ƙasan har ga Allah.

"Mun yi rashin mutum mai kishin talakawa. A nawa ɓangaren na yafe masa dukkanin wani haƙƙi nawa da ke kansa."
"Ina yi masa addu'ar samun rahama a wajen Allah Maɗaukakin Sarki. Allah ya sa Aljannah ta zama makoma a gare shi."

Kara karanta wannan

Bayan suka daga 'yan Arewa, Peter Obi ya fadi dalilin rashin zuwa jana'izar Buhari

- Muhammad Auwal

An tafi da gawar Buhari zuwa Daura

A wani labarin kuma, kun ji cewa an wuce da gawar tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari zuwa garinsa na Daura a jihar Katsina.

An tafi da gawar marigayi Muhammadu Buhari ne zuwa Daura bayan ta iso Katsina daga birnin Landan na ƙasar Birtaniya.

Mai girma Bola Tinubu da kansa ya karɓi gawar daga wajen tawagar gwamnati ƙarƙashin jagorancin mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng