Allahu Akbar: Gawar Tsohon Shugaban Ƙasa, Muhammadu Buhari Ta Iso Gida Najeriya
- A ƙarshe, gawar marigayi tsohon shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari ta iso Najeriya daga birnin Landan na ƙasar Burtaniya
- Tawagar gwamnatin Najeriya ƙarƙashin jagorancin mataimakin shugaban ƙasa, Sanata Kashim Shettima ce ta yiwa gawar rakiya tare da iyalan mamacin
- Ana sa ran bayan kammala duk wasu tsare-tsare, Mai girma shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinibu zai karɓi gawar sannan a wuce zuwa Daura a yi mata sutura
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Katsina - Gawar marigayi tsohon shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari ta iso jihar Katsina da ke Arewa maso Yammacin Najeriya.
Tawagar gwamnatin Najeriya ƙarƙashin jagorancin mataimakin shugaban ƙasa, Sanata Kashim Shettima ce ta yiwa gawar rakiya daga Landan zuwa Katsina.

Source: Twitter
Jaridar TVC News ta tabbatar da wannan labari a wani gajeren saƙo da ta wallafa a shafinta na X da tsakar rana yau Talata.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kashim Shettima ya iso tare da gawar Buhari
Sanata Shettima da iyalan tsohon shugaban ƙasa ne suka yiwa gawar Buhari rakiya tun daga Landan zuwa Katsina.
A bidiyon da Imran Muhammad ya wallafa a shafin X, an ga lokacin da jirgin rundunar sojin saman Najeriya, wanda ya ɗauko gawar Buhari ya sauka a filin jirgin Umaru Musa Yar'adua da ke birnin Katsina.
Ana sa ran shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, mataimakinsa, Kashim Shettima, gwamnoni, ministoci da manyan jami'an gwamnati da al'umma za su yi wa gawar rakiya zuwa Daura.
Tawagar gwamnatin Najeriya da ta ɗauko Buhari
Tun farko dai Sanata Kashim Shettima ya tafi birnin Landan ne bisa umarnin shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu domim cika duka wasu shaɗuɗɗa da ɗauko gawar Buhari zuwa gida.
Tsohon Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari, wanda ya rasu a ranar Lahadi a birnin London, za a birne shi yau Talata, 15 ga watan Yuli, 2025 a gidansa da ke Daura, Jihar Katsina.
Tawagar Mataimakin Shugaban Ƙasa Shettima ta haɗa da Shugaban Ma’aikatam fadar shugaban ƙasa, Femi Gbajabiamila da Gwamnan Jihar Borno Farfesa Babagana Zulum.

Source: Twitter
Sauran sun haɗa da Ministan Harkokin Waje, Ambasada Yusuf Tuggar, da Mataimakin Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Ƙasa Sanata Ibrahim Hassan Hadejia.
Wannan tawaga da Tinubu ya tura Landan sun yi duk abin da ya kamata har aka ɗauko gawar Buhaɗi zuwa gida Katsina cikin mutunci, ƙima da girmamawa.
Tawagar Shettima na tare da iyalan Bubari, wanda suka haɗa da mai ɗakinsa. Hajiya Aisha Muhammadu Buhari da wasu daga cikin ƴaƴan marigayin.
Adesina ya kare Buhari kan zuwa neman lafiya
A wani rahoton, kun ji cewa Femi Adesina, ya ce da Muhammadu Buhari ya dogara da asibitocin Najeriya wajen kula da lafiyarsa, watakila da tuni ya rasu.
Ya bayyana cewa likitocin da ke kula da lafiyar Buhari tun kafin 2015 sun san tarihin lafiyarsa sosai, don haka ba hikima ba ce a sauya su a tsakiyar jinya.
Tsohon kakakin shugaban ƙasar ya ce dole sai yana raye ne zai yi ƙoƙarin gyara harkar lafiyar ƙasar nan, yana mai cewa dama tun kafin ya hau mulki yana zuwa Landan.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

