'Da Yanzu An Mutu,' Tsohon Minista Ya Fadi Gatan da Buhari Ya Yiwa 'Yan Najerya

'Da Yanzu An Mutu,' Tsohon Minista Ya Fadi Gatan da Buhari Ya Yiwa 'Yan Najerya

  • Tsohon ministan ilimi ya ce tsohon Shugaba Muhammadu Buhari ya ki cire tallafin man fetur don kare 'yan Najeriya daga mutuwa
  • Chukwuemeka Nwajiuba ya jaddada cewa gwamnatinsa ta daidaita manyan sassan tattalin arziki duk da matsin da aka samu a duniya
  • Ya ce tattalin arzikin Najeriya ya farfado sau biyu kuma ya tsira daga COVID-19 karkashin Buhari, sannan ya rike Naira kasa da N500/$1

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Tsohon karamin ministan ilimi, Chukwuemeka Nwajiuba, ya bayyana dalilin da ya sa tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ki cire tallafin man fetur.

A cewar Chukwuemeka Nwajiuba, da Muhammadu Buhari ya janye tallafin man fetur a lokacin mulkinsa, da yanzu 'yan Najeriya sun mutu saboda tsananin wahalar rayuwa.

Tsohon ministan ilimi, Chukwuemeka Nwajiuba ya ce da yanzu 'yan Najeriya sun mutu da Buhari ya cire tallafin mai
Tsohon shugaban kasar Najeriya, Muhammadu Buhari a wata rana ta tunawa da 'yan mazan jiya. Hoto: @MBuhari
Source: Twitter

Gatan da Buhari ya yiwa 'yan Najeriya

Kara karanta wannan

Sheikh Pantami ya yi kyautar ban mamaki da aka yi wa Buhari takwara a Bauchi

Nwajiuba ya faɗi haka ne yayin da yake tattaunawa da gidan Arise News, inda ya kare matakan tattalin arziki na Buhari da kuma shugabancinsa gaba ɗaya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cewarsa, duk da rudanin tattalin arzikin duniya, gwamnatin Buhari ta samu nasarar tafiyar da manyan sassan kasar ba tare da tangarda ba.

Chukwuemeka Nwajiuba ya bayyana cewa:

"Tsohon shugaban kasa ya ci gaba da biyan tallafin ne saboda kada 'yan Najeriya su mutu.
"Yawan mutuwar mutane a cikin shekaru biyu da suka gabata ya zarce adadin da suka kaɗa kuri'a daga mutanen da suka mutu sakamakon hatsarin tankar mai, ko kuma kawai saboda tsadar rayuwa."

Ya ci gaba da cewa:

"Duka ya yi tunanin irin wannan, har ma ya gaya wa BBC cewa yana son kare rayukan 'yan Najeriya farko, kafin sauran abubuwa su biyo baya."

Yadda Buhari ya daidaita tattalin arziki

Tsohon ministan ya kuma buga misalai da alkaluman tattalin arziki a karkashin gwamnatin Buhari, inda ya bayyana cewa Najeriya ta tsallake manyan jarabawowi a wancan lokaci.

Chukwuemeka Nwajiuba ya ce:

"Kar a manta, Buhari ya farfado da tattalin arziƙi bayan durkushewarsu har sau biyu, kuma ya kare shi daga annobar COVID-19.

Kara karanta wannan

An fara fito da bayanai kan 'cabal', Gambari ya fallasa yadda aka mamaye gwamnatin Buhari

"Gwamnatinmu ta tabbatar da cewa darajar Naira ba ta haura N500 kan dalar Amurka, kuma har lokacin da ya bar mulki haka take. Ya yi matukar kokari ta fuskar tattalin arziki."

Nwajiuba ya kuma kawo alkaluma daga kungiyar masu kera kayayyaki ta Najeriya (MAN), wanda ya nuna cewa akalla kamfanoni 183 suka daina aiki a cikin shekaru biyu da suka gabata.

Buhari ya inganta tattalin arzikin Najeriya a lokacin da yake kan mulki
Tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya rasu a ranar Lahadi a London. Hoto: @MBuhari
Source: Instagram

Fannonin da Buhari ya inganta a mulkinsa

Ya ce wannan ya bambanta da irin abubuwan da suka faru a lokacin gwamnatin Buhari, yana mai cewa a lokacin an ga karuwar kamfanoni ba raguwarsu ba.

Sassa kamar hakar ma'adinai, fitar da kayayyakin da ba mai ba, da samar da mai, inji shi, sun ga gagarumin ci gaba, tare da ambaton takamaiman manufofin da suka shafi samar da sinadarin condensate da dabarun fitar da su.

Nwajiuba ya kammala da cewa:

"Za a iya ganin dukkan abin da muka yi a harkar ma'adinai, ci gaba a fannin fitar da kayayyaki wanda ba mai ba da kuma gyare-gyare a fannin mai, saboda suna a rubuce.
"Alkaluman suna nan don tabbatarwa. Ba lallai ne a ce Buhari ya magance kowace matsala ba, amma kokarinsa ya haifar da ci gaban kasa da kare rayuka."

Kara karanta wannan

'Yadda Buhari ya yaƙi Bankin Duniya da IMF domin kare talakan Najeriya'

"Ya yi nasa kokarin" - 'Yan Najeriya

Yayin da ake ci gaba da jimamin rasuwar Shugaba Buhari, Legit Hausa ta ji ta bakin wasu 'yan kasar kan kin cire tallafin man fetur da ya yi a lokacin da yake kan mulki.

Mukhtar Sagir Danbatta ya shaidawa wakilin mu cewa tsohon shugaban kasar ya yi iya bakin kokarinsa a mulkin kasar, sai dai ba za a rasa shugaba da nasa kuskuren ba.

"Kowane dan adam ajizi ne, muna yin laifi ko a sane ko a rashin sani. Kowa ya shaida Buhari mutum ne mai gaskiya kuma mai kaunar talaka.
"Kin cire tallafin mai da ya yi ya isa ya tabbatar da hakan. Ai yanzu mun ga halin da kasar take ciki da aka cire tallafin. Amma a lokacinsa, litar man fetur ba ta haura N300 ba.
"Har ya sauka daga mulki, gidan man NNPCL yana sayar da litar fetur kan N210, idan ban manta ba. Amma yau fetur ya doshi 1,000, a hakan ma wai ya sauko.

Kara karanta wannan

Kalaman Buhari 3 da har yanzu suke tayar da jijiyoyin wuya duk da Allah ya masa rasuwa

"Muna godiya ga Buhari, muna yi masa fatan alheri, muna rokon Allah ya gafarta masa, ya yi masa Rahama, ya amshi ayyukansa na alheri,"

Surayya Lawal Musa kuwa ta ce:

"Kamar ba jiya ne ya ke neman takara ba, muka rika tura masa kati don tara kudin yakin neman zabe, ya zo ya ci zabe, ya sake tsayawa takara karo na biyu, muka zabe, ya sake komawa, har ya yi shekaru takwas, to yanzu Allah ya karbi kayansa.
"Gaskiya Sani duniyar nan abar tsoro ce. Shi ya sa yake da kyau shugaba ya rika mulki yana tuna akwai ranar haduwa da Allah. Yanzu shi tashi ta kare, saura haduwarsa da Allah.
"Maganar kin cire tallafin man fetur kuma, muna godiya da bai cire ba, ko ba komai, lokacin rayuwar da dan sauki ba kamar yanzu ba.
"Amma dai, ba za mu manta abubuwan da suka faru a mulkinsa ba. Tun daga kan rufe iyakokin Arewa, canja kudi, karuwar matsalar tsaro, ba za mu manta ba. Amma muna yi masa addu'ar Rahamar Allah."

Kalli tattaunawar a nan kasa:

Kara karanta wannan

Ana ci gaba da bayyana ayyukan alheran Buhari, Malami faɗI abin da ya sani

2025: Manyan da suka rasu a Najeriya

A wani labarin, mun ruwaito cewa, a 2025, Najeriya ta yi babban rashi na manyan mutane da suka taka rawar gani a fannin siyasa, kasuwanci, ilimi da sarauta.

Daga cikin waɗanda suka riga mu gidan gaskiya har da tsohon Shugaban Kasa Muhammadu Buhari da babban Attajiri, Aminu Dantata.

Legit Hausa ta jero fitattun mutane biyar da suka rasu a tsakanin watan Yuni da Yulin 2025, ciki har da Sarki Sikiru Adetona na kasar Ijebu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com