Yadda aka Dauko Gawar Buhari a Jirgi daga London zuwa Katsina

Yadda aka Dauko Gawar Buhari a Jirgi daga London zuwa Katsina

  • An ɗauko gawar tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari daga London zuwa Daura domin jana’izarsa da misalin ƙarfe 2:00 na rana
  • Shugaba Bola Ahmed Tinubu da mataimakinsa, Kashim Shettima da wasu manyan jami'an gwamnati za su karɓi gawar a Katsina
  • An umarci ma’aikatu da hukumomi su buɗe littafin ta’aziyya domin girmama rayuwar tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja – Gawar tsohon shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, ta bar birnin London zuwa Daura, Jihar Katsina, inda za a gudanar da jana’izarsa a yau Litinin, 14 ga Yuli, 2025.

An shirya isowar gawar ne zuwa Najeriya da misalin ƙarfe 12:00 na rana, kuma za a gudanar da jana’iza a gidansa da ke Daura da misalin ƙarfe 2:00 na rana, bisa tsarin addinin Musulunci.

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu zai karɓi gawar Buhari da kansa a Katsina, ya tura ministoci 25 Daura

An dauko gawar Buhari daga London zuwa Najeriya
An dauko gawar Buhari daga London zuwa Najeriya. Hoto: Bashir Ahmad|Kashim Shettima
Source: Facebook

Hadimin marigayin, Bashir Ahmad ya tabbatar da dauko gawar a wani sako da ya wallafa a shafinsa na X.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Shugaba Bola Ahmed Tinubu da manyan jami’an gwamnati za su karɓi gawar a filin jirgin sama na Umaru Musa Yar’Adua da ke Katsina, daga nan ne za a kai ta Daura don jana’iza.

Shettima na tare da gawar Buhari

A cikin sakon da ya wallafa, Bashir Ahmad, ya yi karin bayani kan yadda aka dauko gawar tsohon shugaban kasar.

Bashir ya ce:

"Gawar tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ta bar London zuwa Najeriya.
"Mataimakin shugaban ƙasa Kashim Shettima na tare da gawar, kuma za a karɓe ta a yau a Katsina, inda Shugaba Bola Tinubu zai halarci karɓar gawar kafin jana’iza a Daura, bisa tsarin Musulunci."

Wasu rahotanni sun bayyana cewa tawagar ta haɗa da shugaban ma’aikatan fadar shugaban ƙasa, Femi Gbajabiamila, da ministan harkokin waje, Yusuf Maitama Tuggar.

Kara karanta wannan

Jerin sunaye: Shugaba Tinubu ya ba ministoci 10 muhimmin aiki kan jana'izar Buhari

Tinubu ya umurci buɗe littafin ta’aziyya

A wani mataki na girmamawa, Bola Tinubu ya umurci dukkan ma’aikatu da hukumomin gwamnati da su buɗe littattafan ta’aziyya a ƙofofin ofisoshinsu.

Rahotanni sun bayyana cewa za a yi haka ne domin ba ‘yan Najeriya su samu damar bayyana alhinin rasuwar tsohon shugaban ƙasar.

Tinubu ya bayyana Buhari a matsayin dattijon ƙasa wanda rayuwarsa ta kasance abar koyi wajen rikon gaskiya da sadaukarwa.

Shugabannin ƙasashe za su je Daura

Gwamnan Jihar Katsina, Dikko Umaru Radda, ya tabbatar da cewa ana sa ran wasu shugabannin ƙasashen waje za su halarci jana’izar da za a yi a garin Daura.

A kan haka, gwamna Dikko Umaru Radda ya roki jama'a da su ba jami'an tsaro hadin kai saboda manyan baki da za su halarci jana'izar.

Gwamna Dikko Radda tare da shugaba Buhari yayin taron APC a Katsina
Gwamna Dikko Radda tare da shugaba Buhari yayin taron APC a Katsina. Hoto: Ibrahim Kaulaha Muhammad
Source: Facebook

Buba Galadima ya yafewa Buhari

A wani rahoton, kun ji cewa tsohon abokin marigayi, shugaba Muhammadu Buhari, Buba Galadima ya ce ya yafe masa.

Kara karanta wannan

Shin ya kamata ƴan Najeriya su yafewa Buhari? Sheikh Aminu Daurawa ya roƙi abubuwa 2

Buba Galadima ya ce ya shiga matukar damuwa bayan jin labarin rasuwar shugaba Muhammadu Buhari.

Baya ga haka, Buba Galadima ya ce mutane da dama daga yankuna da dama suna kiran shi a waya suna masa jajen rasuwar Buhari.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng