Mutuwar Buhari Ta Girgiza Buba Galadima, Ya Ce Ya Yafe Masa abin da Ya Faru a baya

Mutuwar Buhari Ta Girgiza Buba Galadima, Ya Ce Ya Yafe Masa abin da Ya Faru a baya

  • Daya daga cikin tsofaffin abokan Muhammadu Buhari, Buba Galadima ya bayyana alhini kan rasuwar tsohon shugaban kasar
  • Rahotanni sun nuna cewa Buba Galadima ya ce ya yafe masa duk wani abu da ya yi masa cikin sani ko kuskure a rayuwarsa
  • Baya ga haka, Buba Galadima ya ce ya karɓi sakonni daga mutane da dama da ke taya shi alhinin rasuwar tsohon abokin tafiyarsa

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Babban jigo a jam’iyyar NNPP kuma dattijo a siyasar Najeriya, Alhaji Buba Galadima, ya bayyana jimami da alhini dangane da rasuwar tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari.

Ya ce bai taɓa yi wa Buhari fatan mutuwa ba, kuma ya riga ya yafe masa duk wani abu da ya yi masa cikin sani ko ba tare da sani ba.

Kara karanta wannan

Mamman Daura: Bayanai sun fara fito wa kan rasuwar Muhammadu Buhari

Buba Galadima ya ce ya yi wa Buhari afuwa
Buba Galadima ya ce ya yi wa Buhari afuwa. Hoto: Bashir Ahmad|Kwankwasiyya Reporters
Source: Facebook

Buba Galadima ya bayyana hakan ne a wata hira da aka watsa a gidan rediyon DW da yammacin ranar Litinin wanda Imrana Muhammad ya wallafa a X.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Buba Galadima ya yafewa Buhari

Buba Galadima ya ce ko da sun saba da Buhari a siyasa bayan hawansa mulki, hakan bai hana shi yafe masa da addu’a ba, bisa dalilin haɗin gwiwar da suka yi a siyasa da kuma girmamawa.

Daily Trust ta wallafa cewa Buba Galadima ya ce a matsayina na wanda suka yi aiki tare, suka yi siyasa tare da shi, ya yafe masa duk abin da ya masa a baya.

A cewar Buba Galadima, ya samu labarin rasuwar Buhari cikin firgici da mamaki, amma a matsayin shi na Musulmi, ya san cewa kowa zai fuskanci mutuwa.

Ya kara da cewa:

"Wallahi ban taba kawo mutuwarsa kusa ba, amma a matsayinmu na musulmi, mun san mutuwa dole ce.

Kara karanta wannan

'Ina tausayawa Tinubu': Abin da Buhari ya ce kan mulkin Najeriya kafin rasuwarsa

Buba Galadima: 'Buhari dan ƙasa ne na gari'

Galadima ya ƙara da cewa tabbas Buhari yana da kishin kasa da fatan inganta Najeriya, duk da cewa sun yi sabani, ya jaddada cewa Buhari mutum ne mai kishin kasa.

Ya bayyana cewa Buhari ya yi ƙoƙarin yin nagarta a lokacin shugabancinsa, yana mai addu’ar Allah ya gafarta masa kurakuransa.

Jigon NNPP a Najeriya, Buba Galadima.
Jigon NNPP a Najeriya, Buba Galadima. Kwankwasiyya Reporters
Source: Facebook

Galadima ya kuma jajanta wa iyalan mamacin, da ‘yan uwa da dukan ‘yan Najeriya, yana mai bayyana rasuwar a matsayin babban rashi da ya girgiza ƙasa baki ɗaya.

Buhari: An yi wa Buba Galadima ta'aziyya

Buba Galadima ya ce rasuwar Buhari ta sanya mutane da dama cikin damuwa, inda wasu suka rika kiran shi domin taya shi alhini.

Ya bayyana cewa mutane da dama sun kira shi daga ciki da wajen ƙasa suna taya shi jimamin rasuwar tsohon abokin tafiyar shi.

Maganganun Buhari 12 da suka ja hankali

A wani rahoton, kun ji cewa tun daga lokacin da ya yi mulkin soja har zuwa dimokuradiyya, Muhammadu Buhari ya yi wasu kalamai da dama da suka ja hankali.

Kara karanta wannan

Tuna Baya: Kalamai masu ratsa zuciya da Buhari ya faɗa kan ciwon da ke damunsa

Daga cikin maganganun da tsohon shugaban kasar ya yi, Legit Hausa ta tattaro masu muhimmanci guda 12.

Daga cikin abubuwan da ya fada akwai lokacin da aka masa tambaya game da doguwar rashin lafiyar da ya yi a London.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng