'Akwai Alaƙa Mai Kyau tsakaninsu': Bidiyon Haɗuwar Buhari da Tinubu na ƙarshe
- Wani bidiyo ya bayyana ganawar Muhammadu Buhari da Bola Tinubu a taron kaddamar da littafi a watan Janairu 2024
- Tinubu ya ayyana kwanaki na makoki tare da hutu a yau Talata 15 ga Yuli, yayin da za a binne Buhari a Daura da ke Katsina
- Bashir Ahmad da gwamnati sun jaddada cewa ganawar ta karshe ta nuna tarihi da kuma soyayya tsakanin shugabannin biyu
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
FCT, Abuja - An gano wani bidiyo da ke nuna ganawar karshe tsakanin tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari da Bola Ahmed Tinubu.
Hakan ya biyo bayan sanar da rasuwar Muhammadu Buhari a ranar Lahadi 13 ga watan Yulin 2025 a London.

Source: Twitter
Wannan na cikin wani rubutu da tsohon hadimin shugaban kasa, Bashir Ahmad ya wallafa a shafin X a jiya Litinin 14 ga watan Yulin 2025.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An dage taron ministoci na musamman saboda Buhari
Tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari ya rasu ne ranar Lahadi, 13 ga Yuli, yana da shekaru 82, bayan fama da doguwar rashin lafiya.
Ya rasu ne a wani asibiti da ke London, inda ya dade yana samun kulawa, kuma za a dawo da gawarsa Najeriya da rana a yau Talata.
Hakan ya sa aka dage taron majalisar zartarwa (FEC) da aka shirya na musamman da aka tsara ranar Talata zuwa ranar Juma’a saboda bikin jana’izar Buhari.
Ministan yada labarai, Mohammed Idris, ya bukaci ’yan Najeriya da su ci gaba da yin addu’a da kuma tunani a kan rayuwar Buhari.
Ya ce:
“Hidimar tsohon shugaban kasa, Buhari da sadaukarwa za su ci gaba da wanzuwa, gwamnati na kira da a girmama sa tare da yin addu’a domin sa.”

Source: Twitter
Bidiyon Buhari da Tinubu na karshe a Abuja
Bidiyon ya nuna ganawar tasu a wajen kaddamar da littafin 'Working with Buhari' da tsohon kakakin fadar shugaban kasa, Femi Adesina ya rubuta.
Faifan bidiyon, wanda Bashir Ahmad ya wallafa ya nuna ganawar ta karshe tsakanin Tinubu da Buhari a taron 16 ga Janairu, 2024.
A cikin faifan bidiyon, an ga sun rungume juna, suna gaisuwa cikin mutunci da zama tare yayin bikin nuna godiya ga shekarun Buhari a mulki.
Bashir Ahmad ya ce:
"Taron karshe a bainar jama’a da ya gudana tsakanin Shugaba Bola Tinubu da marigayi Shugaba Muhammadu Buhari ya kasance a ranar 16 ga Janairu, 2024 a Abuja, yayin kaddamar da littafin Femi Adesina mai suna “Working with Buhari.”
Bidiyon Buhari yana neman afuwar yan Najeriya
A baya, mun ba ku labarin cewa an yada bidiyon karshe da Muhammadu Buhari yana magana kafin barin mulki, inda ya roki gafarar 'yan Najeriya bisa kura-kuran mulkinsa.
Buhari ya ce ya san ya bata wa mutane da dama rai ta hanyoyi daban-daban, kuma yana fatan za su yafe masa har zuciya saboda dan Adam mai kuskure ne.
Ya bukaci duk wanda yake ganin an yi masa rashin adalci ko cin mutunci da ya yafe, yana mai cewa mu duka 'yan Adam ne wanda kowa zai iya yin ba daidai ba.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

