'Masoyin Lagos ne: Tsohon Gwamna Ya Faɗi Alherin Buhari bayan Rasuwarsa
- Tsohon gwamnan Lagos, Akinwunmi Ambode, ya yi jimami rasuwar Muhammadu Buhari, inda ya bayyana shi a matsayin shugaba mai tsoron Allah
- Ambode ya ce Buhari ya mara wa jihar Lagos baya sosai, inda ya amince da manyan ayyuka kamar gyaran hanyar filin jirgin saman MMIA
- Ya roki Allah ya gafarta masa, ya karɓe shi a Aljanna Firdaus, tare da jajantawa iyalan marigayin da daukacin ’yan Najeriya
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Ikeja, Lagos - Tsohon gwamnan jihar Lagos, Akinwunmi Ambode, ya yi jimamin rasuwar tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari.
Ambode ya yabawa Buhari inda ya fadi kyawawan halayensa tare da yi masa fatan samun rahama a lahira.

Source: Twitter
Alherin da Buhari ya shuka a jihar Lagos
A cikin wata sanarwa da TheCable ta samu a ranar Litinin 14 ga watan Yulin 2025, Ambode ya bayyana Buhari a matsayin jagora kuma mai kishin kasa.
Ambode ya ce marigayi Buhari ya yi mulki da tsoron Allah da adalci da kuma kishin ci gaban Najeriya a zuciyarsa.
Ya ce:
“Shugaba Buhari tsohon shugaba ne wanda shugabancinsa, hidimarsa, da kishinsa ga manufofin kasarmu sun ajiye tarihi mai muhimmanci.
"Ya yi shugabanci da mutunci, gaskiya da natsuwa, yana jagorantar ƙasa a lokutan da suka dace tare da kare ƙimomin haɗin kai, adalci da cigaban ƙasa.
“Shugaba Buhari mai kishin jihar Lagos ne, kuma a lokacin da nake gwamna ya bayar da dama da yawa wanda ya nuna muhimmancin jihar.”
Ambode ya tuna cewa a zamanin Buhari, Lagos ta samu amincewar shugaban kasa wajen sabunta hanyar filin jirgin saman MMIA zuwa babbar hanya.

Source: UGC
'Yana da tsoron Allah' - An yabawa marigayi Buhari
Haka kuma, Ambode ya ce jihar ta mallaki wasu kadarorin gwamnatin tarayya ciki har da masaukin shugaban kasa da ke Marina a Lagos, cewar The Nation.

Kara karanta wannan
Bidiyo: Cikin hawaye, Fatima Buhari ta isa Daura inda za a binne gawar mahaifinta
Tsohon gwamnan jihar ya mika ta'azziyarsa ga iyalansa bayan rasuwar Buhari inda ya yi masa addu'ar samun rahama a lahira.
“Ya yi shugabanci da tsoron Allah, da imani da alƙawarin ci gaban ƙasa, da kuma cikakken nauyin hidima ga al’umma.
“Ni da iyalina muna mika ta’aziyyar mu ga iyalan marigayin. Najeriya na cikin alhini tare da ku a wannan babban rashi.
“Allah SWT ya karɓi ayyukan alheri, ya saka masa da Aljanna Firdaus, ya kuma ba iyalansa da ƙasa ƙarfin jure wannan babban rashi.”
- Akinwumi Ambode
Buhari ya rasu ne a ranar Lahadi 13 ga Yuli 2025 a wani asibiti da ke birnin London, ya yi mulki daga shekarar 2015 zuwa 2023.
Tinubu ya kadu bayan rasuwar Buhari a London
Mun ba ku labarin cewa shugaba Bola Ahmed Tinubu ya sanar da rasuwar Muhammadu Buhari a London da misalin ƙarfe 4:30 na yammacin ranar Lahadi bayan rashin lafiya.
Tinubu ya tattauna da Aisha Buhari don jajanta mata sannan ya umarci Kashim Shettima da ya rako gawar marigayi shugaban ƙasar zuwa garin Daura a jihar Katsina.
Buhari ya taɓa mulki a matsayin shugaban soja da na farar hula, yayin da Tinubu ya umarci da a sauke tutoci domin girmama marigayin.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
