'Ina Tausayawa Tinubu': Abin da Buhari Ya ce kan Mulkin Najeriya kafin Rasuwarsa

'Ina Tausayawa Tinubu': Abin da Buhari Ya ce kan Mulkin Najeriya kafin Rasuwarsa

  • Gwamna Dikko Umaru Radda ya bayyana halayen marigayi Muhammadu Buhari na raha da kishin kasa
  • Radda ya ce Buhari na shawartarsa da cewa su yi iya kokarinsu, amma kasar Najeriya sai Allah ne kawai zai iya mata
  • Gwamnan ya ce Buhari na jin tausayin Bola Tinubu, yana yabawa kokarinsa na cire tallafin mai da cewa shi namijin duniya ne

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Daura, Katsina - Gwamna Dikko Umaru Radda na jihar Katsina ya tuno irin hirar da suke yi da marigayi tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari.

Gwamna Radda wanda ya ke yawan zama tare da Buhari bayan ya dawo Daura tun bayan kammala mulki ya fadi kyawawan halayensa.

An fadi kalaman Buhari kan Tinubu kafin rasuwarsa
Dikko Umaru Radda ya yabawa halayen kirki na Buhari. Hoto: Muhammadu Buhari, Dikko Umaru Radda.
Source: Facebook

Gwamna Radda ya yabi halayen Buhari

Radda ya bayyana haka ne a cikin wani faifan bidiyo yayin hira da DCL Hausa da aka wallafa a Facebook.

Kara karanta wannan

'Ya yiwa yan Najeriya iya kokarinsa,' Abin da AbdulSalami ya ce kan Buhari

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cikin bidiyon, Radda ya fadi irin halayen Buhari na raha da kuma kishin kasa da al'umma duk lokacin da suke magana.

Ya ce:

"Ni abin da zan fi tunawa da shi tsakani da Allah tun da ya dawo bayan ya gama mulkinsa ya dawo Katsina kusan shekara biyu suna da yawa.
"Kusan ba a yin sati biyu, sati uku sati hudu ban je na gaishe shi ba muka yi labari, wadannan lokaci da muka yi hira da shi na karu kwarai da gaske.
"Mutum ne mai raha wanda idan dai ka je wurinsa sai ka yi dariya kuma sai ya nuna maka maganganu da yake nuna maka kishin al'umma da kasa."

Shawarar Buhari ga shugabanni kan mulkin Najeriya

Radda ya ce Buhari ya sha yi masa hannunka mai sanda cewa kasar Najeriya fa sai Allah ne kadai zai iya mata.

Gwamnan ya ce a lokacin yana yawan shawartarsa cewa su yi dai iya kokarinsu su kamanta adalci amma Najeriya sai Allah.

Kara karanta wannan

Mamman Daura: Bayanai sun fara fito wa kan rasuwar Muhammadu Buhari

Ya kara da cewa:

"Akwai wata kalma da kullum ya ke fada mani cewa mai girma gwamna ku je dai ku yi abin da za ku iya yi amma Najeriya sai Allah.
"Ya ce mani ya sha walaha sosai amma yanzu jinsa yake yi sakau, ya ce har tausayin Bola yake yi kan wannan abin da ya gani yana yi."

Gwamnan ya ce Buhari yana yawan yin magana kan yadda Tinubu ya yi namijin kokari musamman wurin cire tallafin mai a Najeriya.

"Kuma akwai maganar da ya fada mani cewa Bola namijin duniya ne da ya cire tallafin man nan, ni da na yunkuro sai a ce kaza a ce kaza, ka ga shi rana daya ya cire da ya shawarci wani da bai yi ba."

- Dikko Umaru Radda

Mutuwar Buhari: Jihar Katsina ta ba da hutu

Kun ji cewa al'umma na ci gaba da jimamin rasuwar tsohon shugaban ƙasan Najeriya, Muhammadu Buhari wanda ya rasu a birnin London.

Kara karanta wannan

Mutuwar Buhari ta girgiza Buba Galadima, ya ce ya yafe masa abin da ya faru a baya

Gwamnan jihar Katsina Dikko Umaru Radda ya ayyana ranar hutu saboda rasuwar Buhari wanda yake ɗan asalin garin Daura ne.

Za a gudanar da jana'izar tsohon shugaban ƙasan ne a garin Daura a ranar Talata, 15 ga watan Yulin 2025.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.