'Abin Duniya na Banza ne,' Wasu daga cikin Shawarwarin Buhari ga Ƴan Najeriya
- 'Yan Najeriya suna ci gaba da jajen tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari da ya kwanta dama a ranar Lahadi
- Tuni aka fara tuna wa da tsohon shugaban, inda ake waiwaye a kan wasu daga cikin abubuwan da ya fada a baya
- A baya, an shawarci 'yan Najeriya da su karfafa imaninsu, su rike amana, su kula da iyalansu da kuma mutanen da ke karkashinsu
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT Abuja – Tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari, na daya daga cikin shugabannin Najeriya da ba za a manta da su ba.
Daya daga cikin muhimman abubuwan da ake tuna shi da su, shi ne yadda ya rika horar da al’umma da su rike amana da gaskiya a duk inda aka dora su.

Kara karanta wannan
'Ba zan bar maku gadon dukiya ba,' Abin da Buhari ya fadawa ƴaƴansa kafin ya rasu

Source: Facebook
A daya daga cikin kalamansa da Premier Radio ta wallafa a shafinta na Facebook, an jiyo marigayi Buhari yana ba da shawara mai ma’ana ga ‘yan Najeriya.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Shawarar Buhari ga ‘yan Najeriya
Marigayi shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya taba shawartar ‘yan Najeriya da kada su ci amana a ko’ina aka sa su.
A cikin wasu daga cikin kalamansa da ya taba fada, Buhari ya ce:
“Ina son ku karfafa imaninku, ku yi iya kokarinku, amanar da aka ba ku ku rike. Ku rike amana, ku kula da iyalinku, ku rike jama’ar da aka dora muku shugabanci a kansu.”
Tsohon shugaban ya kara da cewa:
“Abin duniya abin banza ne.”
Buhari ya bayyana yadda ya rayu
A wasu kalaman da ya yi a shekarar 2023, tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana yadda ikon Allah Ya dora shi a kan shugabancin Najeriya.

Source: Getty Images
Ya yi wannan bayani ne yayin da yake zaburar da al’umma kan muhimmancin rike gaskiya da amana a cikin siyasa da shugabanci.
A cikin kalamansa, ya ce:
“Muna so jam’iyyarmu ta APC, a ci gaba da bata amana.Daga lokacin da muka dauka zuwa yanzu, ku kun fi kowa sanin iya kokarin da muka yi.”
“Za mu ci gaba da iya kokarinmu domin ganin halalinku an tabbatar maku da shi.”
Tsohon shugaban kasar, a wancan lokaci, ya yi addu'ar Allah ya ba 'yan isa ikon ci gaba da siyasa mai kyau.
“Allah Ya rufa mana asiri, ya kiyaye mu daga dukkannin sharri.”
“Mu mun gama namu In Sha Allahu. Nan da watan biyar duk zamu koma gida, muna fata a ci gaba da siyasa mai kyau. Nagode sosai, a sauka lafiya.”
Ndume ya yi takaicin rasuwar Buhari
A baya, kun ji cewa Sanatan Borno ta Kudu, Ali Ndume, ya bayyana alhini da kaduwa bisa rasuwar tsohon shugaban kasa na Najeriya, Muhammadu Buhari.
Ya bayyana cewa kasar nan ta yi babban rashi da rasuwar Buhari, wanda ya jagoranci Najeriya a lokuta biyu—na soja da kuma na farar hula.
A karshe, Sanata Ali Ndume ya roki Allah Madaukakin Sarki da Ya gafarta wa marigayi Muhammadu Buhari, tare da sanya shi cikin Aljannatul Firdaus.
Asali: Legit.ng
