Gwamna Radda Ya Sanar da Wurin da Za a Yi Jana'izar Shugaba Muhammadu Buhari
- Gwamnan jihar Katsina, Malam.Dikko Umaru Raɗɗa ya tabbatar da rasuwar tsohon shigaban ƙasa, Muhammasu Buhari a Landan
- Dikko Raɗɗa ya bayyana cewa za a yi jana'izar Buhari yau Litinin, 14 ga watan Yuli, 2025 a gidansa da ke Daura a jihar Katsina
- Gwamna Radda ya kuma miƙa sakon ta'aziyya ga al'ummar Katsina da Najeriya bisa wannan rashi na uba da aka yi
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Katsina - Da yammacin jiya Lahadi, 13 ga watan Yuli, 2025 aka samu labarin rasuwar tsohon shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari.
Iyalan marigayin sun sanar da cewa Buhari ya rasu ne a wani asibiti a birnin Landan na ƙasar Ingila bayan fama da rashin lafiya.

Source: Facebook
Sai dai a wata hira da DW Hausa ta yi da shi, gwamnan Katsina, Malam Dikko Raɗɗa ya ce za a yi jana'izar Buhari a gidansa da ke Daura.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gwamna Raɗɗa ya ce yana ƙasar Ingila lokacin da Allah ya karɓi rayuwar Buhari, domin ya je duba shi tun ranar Juma'a da ta gabata.
Gwamnan Katsina ya tabbatar da rasuwar Buhari
Da yake tabbatar da rasuwar Buhari, Malam Dikko Raɗɗa ya ce:
"InnalilLahi wa inna ilaiHi ra'i'un, Allah Shi yake da rayuwa kuma Ya karɓi ran babanmu, ubanmu, uban ƙasar nan, Muhammadu Buhari.
"Kuma muna yi wa mutanen Katsina da ɗaukacin ƴan Najeriya ta'aziyyar wannan rashi saboda wannan rashi ba namu ba ne kaɗai, na ƙasarmu ne.
"Mun rasa jagora wanda rayuwarsa gaba ɗaya ya kafa ta a kan yadda zai taimaki talaka da yadda talaka zai samu sauƙi na rayuwa. Ba a taɓa yin ɗan siyasar da ya samu martaba da ƙauna kamar yadda ya samu ba a rayuwarsa."
Dikko Raɗɗa ya bayyana cewa yana shirin dawowa gida bayan ya je duba lafiyar Buhari, kwatsam kuma Allah ya ƙarɓi rayuwarsa.

Kara karanta wannan
Shin ya kamata ƴan Najeriya su yafewa Buhari? Sheikh Aminu Daurawa ya roƙi abubuwa 2

Source: Twitter
A ina za a yi jana'azar Buhari?
Da aka tambaye shi kan ina za a yi jana'iza, gwamnan ya ce ya yi magana da iyalan mamacin kuma sun cimma matsayar cewa za a yi masa sutura a mahaifarsa watau Daura.
"Yanzu muka rabu da iyalansa a asibitin da ya rasu, kuma an yi ittifaƙin za a kai shi gida Najeriya a Katsina, a Daura domin a yi ma shi sutura.
"Kuma in Sha Allahu da safe za su baro Ingila domin mataimakin shugaban ƙasa ya taso daga Najeriya zai zo ya tafi da gawar bisa umarnin shugaban ƙasa."
"Za mu koma Katsina mu tare su daga nan mu wuce Daura inda za a masa sutura da izinin Allah.
- Gwamna Dikko Raɗɗa.
Gwamnan ya ƙara da cewa idan komai ya tafi yadda aka tsara, za a yi jana'izar Buhari a Daura da La'asar yau Litinin, 14 ga watan Yuli, 2025.
Abubuwan da za a tuna Buhari da su
A wani labarin, mun kawo maku wasu abubuwan da suka faru a mulkin marigayi Muhammadu Buhari da ba za a manta da su ba.
Muhammadu Buhari ya shafe wani lokaci yana jinya a birnin London bayan ya sauka a mulki shekaru biyu da suka wuce, kafin Allah ya karɓi ransa.
Rasuwar Shugaba Buhari ta girgiza Najeriya baki daya wanda al'umma suke yi masa fatan samun gafara da rahamar Allah.
Asali: Legit.ng

