Bidiyo: Ganin Karshe da 'Yan Najeriya Suka Yi wa Buhari, Yana Tare da Atiku, El-Rufai
- A ranar 11 ga Afrilun 2025, Atiku Abubakar da wasu jiga-jigan siyasa sun kai ziyara gaisuwar Sallah ga Muhammadu Buhari a Kaduna
- Bidiyon ganawarsu ya karade intanet, inda aka ga tsohon shugaban cikin nishadi, wanda hakan shi ne ganinsa na karshe kafin rasuwarsa
- Daga lokacin aka ce ba a sake ganin wani bidiyon Buhari ba, sai a yau Lahadi kwatsam, Garba Shehu ya sanar da rasuwar Buhari a London
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Kaduna - A ranar Juma'a, 11 ga watan Afilun 2025, Atiku Abubakar ya jagoranci wasu 'yan siyasa, ciki har da Nasir El-Rufai suka yi wa Muhammadu Buhari barka da Sallah.
Wannan ganawar tasu, wacce bidiyonta ya yadu a intanet, ita ce ganin karshe da 'yan Najeriya suka yiwa tsohon shugaban kasar, wanda ya rasu a yau Lahadi a London.

Source: Twitter
Bindiyon karshe na Buhari a Kaduna
Bidiyon Buhari tare da su Atiku wanda Legit Hausa ta gani a shafin X na tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai, ya nuna Buhari cike da fara'a, da dariya, kamar ajali ba ya kusa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Nasir El-Rufai, ya wallafa cewa:
"Tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar, tsofaffin gwamnonin jihohi Aminu Tambuwal (Sokoto), Achike Udenwa (Imo), Gabriel Suswam (Benue) da ni, tare da wasu da dama, mun ziyarci tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari a Kaduna domin gaisuwar bayan Sallah.
"Mun halarci sallar Juma’a tare da daruruwan mabiya a masallacin titin Yahaya, sannan muka ci abincin rana mai dadi a gidan Buhari."
Da yawa daga cikin wadanda suka ziyarci Buhari a wannan ranar, ita ce ranar karshe da suka sanya shi a idanunsu, domin tun bayan sallar aka daina jin duriyarsa.
Kalli bidiyon a nan kasa:
Rashin lafiyar Buhari da jinya a London
A 'yan kwanakin nan ne jita-jitar rashin lafiyar tsohon shugaban kasar ta karade shafukan sada zumunta, inda har wasu na rade-radin ya rasu a makon jiya.

Kara karanta wannan
'An yi babban rashi': Tsohon shugaban kasa Buhari ya rasu, ƴan Najeriya sun magantu
Sai dai a makon jiyan, mai magana da yawunsa, Garba Shehu, ya fito ya shaidawa 'yan kasar cewa lallai Buhari ba shi da lafiya, amma ya samu sauki sosai.
Garba Shehu ya ce a lokacin Buhari ya na samun kulawar likitoci a wai asibiti da ke London, kuma zai dawo gida Najeriya da zarar ya murmushe, kamar yadda muka ruwaito.

Source: Twitter
Rasuwar Muhammadu Buhari a ranar Lahadi
Sai dai kwatsam, a ranar Lahadi, 13 ga watan Yulin 2025, Garba Shehu ya sanar da cewa Muhammadu Buhari, tsohon shugaban Najeriya ya rasu.
Mun ruwaito cewa, Garba Shehu ya ce Buhari ya rasu ne a wani asibitin London a yammacin ranar, inda yake samun kulawa daga likitoci.
Jim kadan bayan wannan sanarwar, Shugaba Bola Tinubu ya fitar da sanarwa, inda ya bukaci mataimakinsa, Kashim Shettima da ya hanzarta zuwa London inda Buhari ya rasu.
A cikin sanarwar da Bayo Onanuga, mai magana da yawun shugaban kasar ya fitar, Tinubu ya bukaci Shettima ya rako gawar Buhari zuwa gida Najeriya, kamar yadda muka ruwaito.
'Yan Najeriya sun magantu kan rasuwar Buhari
Tun da fari, mun ruwaito cewa, 'yan Najeriya sun kadu matuka da suka samu labarin rasuwar tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari, wanda ya rasu a London.
'Yan Najeriya sun aika sakonnin ta'aziyyarsu ga iyalan Buhari bisa wannan babban rashi da aka yi tare da yi masa addu'ar samun rahamar Ubangiji.
Shi ma Shugaba Bola Tinubu ya tattauna da Aisha Buhari don jajanta mata sannan ya umarci Kashim Shettima da ya rako gawar marigayin shugaban ƙasar.
Asali: Legit.ng

