Sokoto: Gwamnati Ta Kafa Sharuɗa Masu Tsauri ga Turji yayin da Ake Maganar Sulhu

Sokoto: Gwamnati Ta Kafa Sharuɗa Masu Tsauri ga Turji yayin da Ake Maganar Sulhu

  • Gwamnatin jihar Sokoto ta yi magana kan sulhu da ake shirin yi da yan bindiga bayan munanan hare-haren da ake kai wa
  • Gwamnatin ta bukaci rikakken dan bindiga, Bello Turji da ya saki dukkan fursunonin da ke hannunsa
  • Mai bai wa Gwamna Aliyu shawara, Kanal Ahmed Usman mai ritaya, ya ce furucin Turji na neman zaman lafiya ba zai yi tasiri ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Sokoto - Gwamnatin Jihar Sokoto ta tura bukata ta musamman ga rikakken dan bindiga, Bello Turji yayin da ake maganar sulhu.

Gwamnatin ta bukaci dan bindiga, Bello Turji, da ya nuna gaskiyarsa ga shirin zaman lafiya ta hanyar sakin fursunoni.

Gwamnatin Sokoto ta kafa sharuda ga Bello Turji
Gwamnatin Sokoto ta gindaya sharuɗa ga Turji yayin da ake shirin sulhu. Hoto: Ahmed Aliyu.
Source: Twitter

Mai ba Gwamna Ahmed shawara, Kanal Ahmed Usman mai ritaya shi ya tabbatar da haka a wata sanarwa da ya fitar, cewar rahoton Leadership.

Kara karanta wannan

Gwamna ya hana Fulani makiyaya kiwo a jiharsa, ya ba su wa'adin kwana 12 kacal

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda ake kokarin sulhu da Bello Turji

Hakan ya biyo bayan fara shirin sulhu da ake yi domin tabbatar da cewa an dakile hare-haren da ake yi.

Tun farko ana zargin Bello Turji ne ya fara neman sulhu da ake tunanin ya fara shan matsin lamba daga sojoji.

An ce hakan bai rasa nasaba da kisan babban kwamandansa kuma ɗan uwansa, Kachallah Yellow Danbokolo.

Gwamnatin Sokoto ta tura bukata ga Turji

Kanal Ahmed ya yi kira ga Turji ya daina kai hare-hare kan kauyuka yayin da yake iƙrarin zaman lafiya a yankin.

Wannan kiran na Usman ya biyo bayan yaduwar wani sauti da Turji ya fitar yana nuna niyyarsa na zaman lafiya da tattaunawa da sauran shugabanni.

Usman ya bayyana cewa, kalaman Turji na iya zama matakin farko, amma wajibi ne ya bi su da ayyuka da za su kawo kwanciyar hankali.

Ya ce:

“In har Turji na son zaman lafiya da gaske, to sai ya daina tashin hankali gaba ɗaya kuma ya saki dukkan fararen hula da ya kama."

Kara karanta wannan

Adamawa: Gwamna Fintiri ya ƙaƙaba dokar hana fita bayan ɓarkewar rikici

An shinfida sharuda ga Bello Turji kan sulhu
Gwamnatin Sokoto ta bukaci Turji ya sako wadanda ya kama. Hoto: Legit.
Source: Original

Sulhu: Sharadin gwamnatin Sokoto ga Bello Turji

Mai bai wa gwamnan shawara ya ce gwamnatin Aliyu na mayar da hankali sosai wajen kare rayuka da dukiyoyin jama’ar karkara da ke fama da hare-hare.

“Ba za a iya yin tattaunawa da gaskiya ba alhali mutane na rayuwa cikin tsoro da ƙuncin zama a daji,”

- Cewar Kanal Usman

Ya sake bayyana cewa gwamnati za ta goyi bayan duk wani sahihin yunkuri na wanzar da zaman lafiya amma ba za ta yarda da laifi ko kaɗan ba, cewar Punch.

Usman ya kuma yi kira ga shugabannin al’umma, kungiyoyin farar hula da na addini su hada kai domin dawo da zaman lafiya da kwanciyar hankali.

Turji ya sake bidiyo ana maganar sulhu

Mun ba ku labarin cewa dan bindiga Bello Turji ya saki sabon bidiyo ana cikin maganar sulhu inda ya ce yana tattaunawa da gwamnati.

Dan ta'adda, Turji ya ce rigingimun baya rashin fahimta ne, amma mutane da dama sun nuna shakku, suna ganin yana kokarin tsira da kansa.

Masana sun gargadi gwamnati da ka da ta amince da shirin sulhu ba tare da adalci da hukunta laifuka ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.