Turawa Sun Zakulo Abba Kabir cikin Gwamnoni, an Karrama Shi a London
- Gwamna Abba Kabir Yusuf na jihar Kano ya samu lambar yabo a matsayin gwamnan da ya yi fice wajen bunkasa abubuwan more rayuwa
- An mika masa kyautar ne a taron zakarun nahiyar Afrika karo na 15 da aka gudanar a fadar majalisar wani yanki na London
- Gwamnatin Kano ta bayyana wannan nasara a matsayin wata alama ta yadda ayyukan raya kasa ke kawo canji mai ma’ana a jihar baki daya
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Birtaniya – Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya samu lambar yabo ta musamman a matsayin gwamnan da ya yi fice kan samar da abubuwan more rayuwa.
Rahotanni sun nuna cewa an karrama Abba Kabir ne a taron bada kyaututtukan zakarun Afrika karo na 15 da aka gudanar a London.

Source: Facebook
Sanarwar da mai magana da yawun gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar a Facebook ta bayyana cewa an gudanar da taron ne a fadar tarihi ta Westminster da ke Birtaniya.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An mika kyautar ne daga hannun mataimakin magajin garin London, Mete Coban, domin girmama kokarin Gwamna Yusuf wajen aiwatar da manyan ayyuka na sabunta jihar Kano.
Ayyuka da suka jawo karrama Abba Kabir
Abba ya samu lambar yabon ne saboda jajircewarsa wajen gina sababbin tituna, shirye-shiryen gyaran birane da maido da ingancin muhimman cibiyoyin gwamnati.
A madadin gwamnan, mai ba da shawara kan harkokin jiha, Usman Bala, mni tare da shugaban yada labarai, Bature Dawakin Tofa sun karɓi kyautar a wurin bikin.
A jawabinsa, Usman Bala ya ce:
“Wannan lambar yabo shaida ce ta yadda Gwamna Yusuf ke ba da fifiko ga ci gaban da ya shafi rayuwar al’umma kai tsaye.”
Girman taron da martabar kyautar Abba Kabir
Taron na da nufin girmama shugabanni da cibiyoyi masu tasiri a nahiyar Afrika, kuma ya zama dandalin nuna kwarewa da jajircewa a fannoni daban-daban.
A wannan karon, gwamnan jihar Benue da Sarkin kasar Zolu na Afirka ta Kudu suma sun samu lambobin yabo, abin da ke nuna yadda ake girmama shugabanni daga sassa daban-daban.

Source: Facebook
Kano ta zama abin koyi a Najeriya
Samar da wannan lambar yabo ga Abba Kabir ya kara tabbatar da matsayin jihar Kano a matsayin wadda ke tafiyar da mulki mai dogaro da bunkasa abubuwan more rayuwa.
Gwamnatin Kano ta ce za ta ci gaba da mayar da hankali kan manyan ayyuka da za su kawo sauyi ga rayuwar al’umma.
Abba Kabir ya ba Ahmad Musa mukami
A wani rahoton, kun ji cewa gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya karrama fitaccen dan kwallon da ya takawa Najeriya leda, Ahmad Musa da mukami.
Mai girma Abba Kabir Yusuf ya ba Ahmad Musa mukami a kungiyar kwallon kafar jihar Kano da aka fi sani da Kano Pillars a makon da ya wuce.
Ana fatan Ahmad Musa zai yi amfani da basirar shi wajen kawo cigaba a kungiyar kwallon kafan tare da sake fito da darajar ta a Najeriya.
Asali: Legit.ng

