Fadar Shugaban Kasa Ta Zargi wasu Ƴan Siyasa da Ƙoƙarin Gwara Buhari da Tinubu

Fadar Shugaban Kasa Ta Zargi wasu Ƴan Siyasa da Ƙoƙarin Gwara Buhari da Tinubu

  • Fadar shugaban kasa ta zargi wasu yan siyasa da ƙoƙarin gwara kawunan magoya bayan Bola Tinubu da Muhammadu Buhari
  • Daniel Bwala ya zargi wasu ‘yan siyasa da suka rasa madafun iko da ƙoƙarin haddasa rikici tsakanin magoya bayan shugabannin biyu
  • Bwala, ya ce duk ƙoƙarin sauya kalaman mai magana da yawun Buhari, Garba Shehu domin hada su rigima, hakan ba zai yi tasiri ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT Abuja – Mai bai wa Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu shawara na musamman kan harkokin sadarwa, Daniel Bwala ya dura kan wasu yan siyasa.

Ya zargi wasu 'yan siyasa da suka rasa madafun iko da ƙoƙarin tayar da rikici tsakanin magoya bayan Shugaba Bola Tinubu da na magabacinsa, Muhammadu Buhari.

Kara karanta wannan

ADC: An fara ƙoƙarin canza wa Atiku tunani, haɗaka na fuskantar gagarumar matsala

Bola Tinubu da Muhammadu Buhari
Fadar shugaban kasa ta caccaki yan siyasa Hoto: Muhammadu Buhari
Source: Facebook

A sakon da ya wallafa a shafinsa na X, Bwala ya ce suna sane da yadda wadansu ƴan siyasa ke fadi tashi domin tayar da husuma a tsakanin yan APC.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Bwala ya caccaki yan adawa

A cewar Bwala, waɗannan 'yan siyasa da ke cikin wata haɗakar hamayya, na amfani da kafafen yaɗa labaransu wajen haifar da sabani da yaɗa ƙarya don tayar da rikici.

Ya fadi haka ne a matsayin martani kan zargin wasu daga cikin magoya bayan Buhari, da suka fassara kalaman tsohon sakataren gwamnatin tarayya, Boss Mustapha, a baibai.

Daniel Bwala, Tinubu da Atiku
Daniel Bwala ya zargi yan hadakar adawa da son tayar da rikici a APC Hot: Daniel Bwala/Atiku Abubakar
Source: Twitter

A baya an ruwaito cewa Boss Mustapha ya ce ba Tinubu ne ya ba Buhari nasara a zaɓen 2015 ba, inda ya ce kuri’un Buhari miliyan 12 ne suka ba shi damar lashe zaɓen.

Lamarin ya jawo ana juya magana, inda wasu daga cikin wadanda suka rike madafun iko a gwamnatin Buhari ke cewa Tinubu bai goyi bayan takarar Buhari ba a wancan lokaci.

Kara karanta wannan

'Mun gane wayon': ADC ta yi martani kan zargin shiryawa Tinubu 'juyin mulki'

Bwala ya dura kan yan adawa

Amma a martaninsa, Bwala ya siffanta haɗakar adawa da taron yan siyasa da suka rasa tudun dafawa, saboda haka suna kokarin tayar da tarzoma a tsakanin ƴaƴan APC.

Ya kara da cewa:

“Waɗannan ‘yan siyasa da suka rasa madafun iko suna amfani da kafafen yaɗa labaransu domin haifar da rikici tsakanin yaran Buhari da na Tinubu.
“Haka suka fassara maganganun Boss Mustapha, tsohon Sakataren gwamnati yadda zai yi masu dadi."
“Har ma suka jingina wani rubutu da Garba Shehu ya yi gare ni da fatan zan shiga cece-kuce da shi. Amma sun gaza cimma manufarsu, domin ni da Garba Shehu mun tattauna mun fahimci juna.

Bwala ya yiwa Atiku shagube

A wani labarin, kun ji cewa hadimin shugaban kasa, Daniel Bwala ya ce yan adawa ba su da hadin kan da za su zama barazana ga mulkin Bola Ahmed Tinubu a 2027.

Ya jaddada cewa har yanzu APC ce ke ci gaba da karɓar sababbin ‘yan siyasa saboda yawan sauya sheƙar da ake yi zuwa jam’iyyar, wanda ke nuna karɓuwarta.

Bwala, wanda ya kasance tsohon makusancin Atiku Abubakar ne kafin ya sauya sheka zuwa APC, ya ce babu cikakkiyar jituwa ko kaɗan a tsakanin jagororin adawa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng