'Yan Sanda Sun Gwabza Kazamin Fada da Ƴan Bindiga a Nasarawa, An Samu Asarar Rai
- Ƴan sandan Nasarawa sun dakile harin ƴan bindiga a hanyar Kadarko–Makurdi, inda suka tilasta musu guduwa zuwa dajin Benue.
- An yi musayar wuta mai zafi; wani ɗan sanda ya ji rauni, kuma wani farar hula ya mutu sakamakon harsashin ƴan bindigar.
- Kwamishinan CP Jauro-Mohammed ya ba da umarnin bincike, yana mai tabbatar wa jama'a za a kama waɗanda suka kai harin.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Nasarawa – Rundunar 'yan sandan jihar Nasarawa ta ce jami’anta sun dakile wani hari da wasu ƴan bindiga suka kai musu a kan hanyar Kadarko–Makurdi a karamar hukumar Keana ta jihar.
A cikin wata sanarwa da aka fitar ranar Juma’a a Lafia, babban birnin jihar, Ramhan Nansel, kakakin ƴan sanda a jihar, ya ce harin ya faru ne da misalin karfe 10:55 na daren Talata.

Source: Twitter
'Yan bindiga sun farmaki 'yan sanda a Nasarawa
Nansel ya ce maharan sun bude wuta kan jami’an da ke bakin aiki bayan sun fito daga wani daji a jihar Benue da ke makwabtaka da Nasarawa, inji rahoton The Cable.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yadda aka dakile harin da rasa rayuka
Sanarwar Ramhan Nansel ta ce:
“Ƴan bindigar da suka yi wa jami’anmu kwanton bauna tare da farmakar su sun fito ne daga dajin Benue, inda suka fara harbi ba kakkautawa kan jami'anmu.
“Jami’anmu sun nuna ƙarfin hali da dabara, inda suka gwabza kazamin faɗa da maharan. Sun samu nasarar dakile harin kuma suka tilasta wa ƴan ta’addan rantawa a na-kare zuwa dajin Benue da alamar raunukan harbin bindiga.”
Mutum 1 ya mutu a harin 'yan bindigar
Sai dai sanarwar ta ce duk da kokarin da jami'an suka yi, wani ɗan sanda mai suna Sufeto Sunday Apochie, ya sami raunin harbin bindiga yayin musayar wutar.

Kara karanta wannan
Sojoji sun yi ruwan wuta kan 'yan ta'adda da ke hijira a tsakanin Kebbi da Zamfara
Ramhan Nansel ya ce sashen ƴan sanda na Kadarko ya amsa kiran gaggawa tare da ceto jami'in da ya ji rauni.
Amma kakakin rundunar 'yan sandan ya yi alhinin sanar da cewa wani farar hula da ke kusa da wurin da abin ya faru ya mutu sakamakon harsashin maharan da ya same shi.
Ya kuma ƙara da cewa jami’in da ya ji rauni yana samun kulawa a asibiti kuma yana murmurewa cikin sauri a halin yanzu.

Source: Twitter
'Yan sanda sun fara gudanar da bincike
Ramhan Nansel ya ce kwamishinan ƴan sandan Nasarawa, Shetima Jauro-Mohammed, ya bayar da umarnin gudanar da kwakkwaran bincike kan harin.
Shetima Jauro-Mohammed, ya kuma tabbatar wa al'ummar Nasarawa cewa 'yan sanda na ƙoƙar wajen ganin cafke waɗanda ake zargin sun kai harin da suka gudu.
Kwamishinan ƴan sanda ya kuma mika ta’aziyyarsa ga iyalan farar hular da ya rasu.
Jami'an tsaro su kashe 'yan bindiga 30
A wani labarin, mun ruwaito cewa, jami’an tsaro sun kashe ’yan bindiga 30 a Katsina yayin musayar wuta da suka yi da daruruwan ’yan ta’addan.

Kara karanta wannan
Plateau: Batun kisan ƴan Zaria ya dawo, an gurfanar da mutum 22 bayan gama bincike
An ce jami'an sun yi musayar wuta da 'yan ta'addar a kokarin dakilen harin da suka kai garuruwan Kadisau, Raudama, da Sabon Layi da ke Faskari.
Gwamnatin jihar Katsina ta bayyana cewa sojoji biyu, jami’an ’yan sanda uku da wani farar hula sun rasa rayukansu yayin wannan artabun da aka yi.
Asali: Legit.ng
