NiMet: Za a Sheka Ruwan Sama a Bauchi, Kano, Zamfara da Jihohi 18 a Ranar Juma'a

NiMet: Za a Sheka Ruwan Sama a Bauchi, Kano, Zamfara da Jihohi 18 a Ranar Juma'a

  • Hukumar NiMet ta bayyana cewa za a samu ruwan sama da tsawa a yawancin jihohin Najeriya, tare da yiwuwar iska mai ƙarfi
  • Jihohin Arewa kamar Taraba, Borno, Yobe, Jigawa, Bauchi da sauran su za su fuskanci tsawa da ruwan sama da rana har zuwa dare
  • A Kudu da Arewa ta Tsakiya ma ana hasashen ruwan zai sauka, inda NiMet ta shawarci jama'a su kauce wa wuraren da ke da haɗarin ambaliya

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja – Hukumar kula da hasashen yanayi ta Najeriya (NiMet) ta fitar da hasashen yanayi na yau Juma'a, 11 ga watan Yulin 2025, kamar yadda ta saba kullum.

Hasashen NiMet ya nuna cewa za a sheka ruwan sama a yau Juma'a a yawancin sassan ƙasar, kuma akwai yiwuwar ruwan ya zo da tsawa ko iska mai karfi.

Kara karanta wannan

Tashin hankali: Fulani makiyaya sun bankawa gidaje 100 wuta, mutum 1 ya mutu a Taraba

Hukumar NiMet ta yi hasashen saukar ruwan sama a Kaduna, Kano da wasu jihohin Arewa da Kudu a ranar Juma'a
Za a zabga ruwan sama da iska mai karfi a wasu jihohin Najeriya. Hoto: Sani Hamza/Staff
Source: Original

A sanarwar da ta fitar a shafinta na X, hukumar ta yi gargadi ga jama'a da su kasance cikin shiri don akwai yiwuwar ambaliyar ruwa, iska mai ƙarfi, da kuma rushewar gidaje.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tsawa da ruwan sama a Arewacin Najeriya

Sanarwar hasashen yanayin, wacce NiMet ta fitar a ranar 10 ga Yulin 2025, ta bayyana cikakken yanayin da ake sa ran a jihohin Arewa, Tsakiya, da Kudu.

A safiyar ranar Juma'a, ana sa ran za a samu tsawa tare da ruwan sama mai matsakaicin ƙarfi a sassan jihohin Taraba, Borno, Yobe, Jigawa, da Bauchi. Sauran yankuna za su kasance cikin yanayi mai rana tare da ɗan gajimare.

Da yamma zuwa dare kuwa, ana sa ran tsawa tare da ruwan sama mai matsakaicin ƙarfi a sassan Adamawa, Taraba, Kaduna, Zamfara, Bauchi, Kebbi, Borno, Jigawa, Yobe, Katsina, da Kano.

Hasashen yanayi a jihohin Arewa ta Tsakiya

Kara karanta wannan

NiMet: Za a sha ruwa da iska mai karfi a Kano, Yobe da jihohi 24 a ranar Alhamis

A safiyar ranar Juma'a, 11 ga Yuli, NiMet ta ce a jihohin Arewa ta Tsakiya, ana sa ran za a samu sararin samaniya mai rana tare da ɗan gajimare.

Da yamma zuwa dare ne ake sa ran tsawa tare da ruwan sama mai matsakaicin ƙarfi a Abuja, Nasarawa, Kogi, Kwara, Benue, Niger, da Plateau.

Jihohin Kudu: Ruwan sama mai matsakaicin karfi

A safiyar ranar Juma'a a jihohin Kudu, ana sa ran za a samu haduwar hadari tare da yiwuwar saukar ruwan sama a sassan jihohin Rivers, Cross River, da Akwa Ibom.

Da yamma zuwa dare kuwa, ana sa ran za a samu ruwan sama mai matsakaicin ƙarfi a yawancin sassan yankin kudancin ƙasar.

Hukumar NiMet ta ce ruwa da iska mai karfi na iya lalata gidaje da haddasa cunkoson ababen hawa
Za a zabga ruwan sama da iska mai karfi a wasu jihohin Najeriya. Hoto: Sani Hamza/Staff
Source: Original

Gargadi ga jama'a kan hatsarin ruwa

NiMet ta shawarci jama'a da su kasance cikin shiri don yiwuwar ambaliyar ruwa ta farat ɗaya, iska mai ƙarfi, da kuma katsewar lantarki da rushewar gidaje sakamakon ruwa da iska.

Hukumar hasashen yanayin ta buƙaci jama'a da su ɗauki matakan kariya da kuma guje wa wuraren da ke da haɗarin ambaliya, da daina yin tuki ana ruwa mai karfi.

Kara karanta wannan

An gano wani otel da ake safarar 'yan mata da tilasta su yin karuwanci a Katsina

Za a sheka ruwa na kwanaki 250 a Najeriya

A wani labarin, mun ruwaito cewa, NiMet ta yi hasashen jihohi shida a Kudu za su fi samun ruwan sama a 2025, inda take hasashen z a su samu ruwa na kwanaki 250.

Cikin jerin jihohin da za su fi samun ruwa akwai Legas da Osun, sai kuma wasu hudu da ba a bayyana ba, yayin da jihohin Ogun da Oyo ke biye da su a yawan kwanakin ruwan.

A ɓangaren Arewa kuwa, NiMet na hasashen cewa jihohin yankin za su samu ruwan sama daga kwanaki 150 zuwa 200, sai wasu sassan da za su fuskanci kasa da hakan.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com