Shugaban NNPCL Ya Samu Matsala da Majalisa kan Ɓacewar N210trn
- Sanatoci sun bukaci shugaban kamfanin NNPCL, Bayo Ojulari da ya bayyana a gabanta domin amsa tambayoyi kan wasu kuɗi
- Majalisa ta bayyana takaici a kan bambancin kuɗi na Naira tiriliyan 210 da aka samu daga rahoton asusun kamfanin mai na kasa
- Bayan rashin bayyanar Ojulari a gabanta, majalisa ta yi barazanar cewa za ta iya sawa a kamo shi, sannan a mika shi kotu
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT, Abuja – Takaddama na kunno kai tsakanin Kwamitin Binciken Asusu na Majalisar Dattawa da Shugaban Kamfanin Man Fetur na Ƙasa (NNPCL), Bayo Ojulari.
A ranar Alhamis, 'yan majalisar sun bai wa shugaban kamfanin mai na ƙasa umarnin gaggawa da ya bayar da bayani kan bambancin kuɗi na N210trn da ke cikin bayanan kuɗin kamfanin.

Source: Facebook
Arise News ta ruwaito cewa 'yan majalisar sun yi barazanar cewa idan ya gaza bin umarnin, zai fuskanci cikakken hukunci, ciki har da kama shi, gurfanarwa da yi masa tonon silili.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
NNPCL: An yi zazzafar muhawara a majalisa
Jaridar The Guardian ta ruwaito cewa a zaman majalisar na ranar Alhamis, Sanatoci sun bayyana ɓacin ransu kan yadda NNPCL ke ƙin amsa gayyata da dama da aka aike masa.
Sun bayyana kin halartar shugabannin NNPCL a matsayin raini da yunƙurin kauce wa bayar da bayanan da aka buƙata daga gare su.
Shugaban kwamitin majalisa, Sanata Aliyu Wadada, ya ce:
“A fahimta, wannan gayyata ba zaɓi ba ce. Wannan kwamitin yana da ƙarfin doka daga kundin tsarin mulkin Najeriya da wasu dokokin da suka dace. Duk wanda ya fi ƙarfin bin doka, to ya fara tunanin sauya ƙasa.”
Kwamitin majalisa ya gargaɗi NNPCL
Sanata Wadada ya ce majalisa ba za ta yi kasa a guiwa ba wajen amfani da ƙarfin dokarta domin kiran, cafke da gurfanar da duk wani jami’in gwamnati da ke ƙoƙarin raina huruminta.

Kara karanta wannan
Bauchi: Sarakuna sun aika sako ga magoya baya kan shirin kirkirar sababbin masarautu
Rikicin da ke faruwa yanzu ya samo asali ne daga gagarumin sabani da ke cikin bayanan da NNPCL ta fitar na asusun kamfanin da aka tantance, wanda kwamitin ya ce dole ne a fayyace su.

Source: Facebook
Daga cikin matsalar akwai batun rahoton da kamfanin ya bayar na mallakar kadarorin Naira tiriliyan 210 da ba a samar da takardun da ke tabbatar da hakan ba.
Wadada ya ce:
“Abin da muka ce, kuma da muke nanatawa shi ne, dole NNPCL ta bayar da cikakken bayani kan Naira tiriliyan 210 da aka nuna a cikin bayanan kuɗinta.”
Sanatan ya bayyana cewa kwamitin bai zargin NNPC da sata, sai dai ya nace cewa dole ne a zo da takardun da suka dace don tabbatar da kuɗin.
Natasha ta rasa babbar kujera a majalisa
A baya, mun ruwaito cewa majalisar dattawan ta cire Natasha Akpoti-Uduaghan daga muƙaminta na shugabar kwamitin harkokin ‘yan gudun hijira da kungiyoyin sa-kai.
Shugaban majalisar, Godswill Akpabio, ya sanar da nadin Aniekan Bassey a matsayin sabon shugaban kwamitin, inda ya tabbatar da cewa zai maye gurbin Natasha.
Sanata Natasha wacce ke wakiltar Kogi ta Tsakiya a majalisar dattawa, ta karɓi shugabancin kwamitin harkokin ‘yan gudun hijira a watan Fabrairun shekarar 2027.
Asali: Legit.ng
