"Ina Lalata da Maza 600 a Wata": An Ji Ta Bakin Budurwa da Ke Karuwanci a Katsina

"Ina Lalata da Maza 600 a Wata": An Ji Ta Bakin Budurwa da Ke Karuwanci a Katsina

  • 'Yan mata uku da hukumar NAPTIP ta ceto a wani otel din Katsina sun bayyana cewa suna yin lalata da akalla maza 20 a kowacce rana
  • Daya daga cikin wadanda aka ceto, ta ce wata mata ce ta yaudare su zuwa Katsina da suna za ta ba su aiki, sai ta tilasta su yin karuwanci
  • NAPTIP ta ce jami'anta sun kama mutane uku da ake zargin 'an kungiyar safarar mutane ce, kuma an kama manaja da ma'aikatan otel din

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Katsina – Jami’an hukumar yaki da fataucin mutane (NAPTIP) sun ceto wasu 'yan mata uku da ake tilasta masu yin karuwanci a jihar Katsina.

An ceto 'yan matan ne lokacin da NAPTIP ta bankaɗo wata ƙungiyar fataucin mutane tsakanin jihohi a ɗaya daga cikin manyan otel-otel na Katsina.

Kara karanta wannan

An gano wani otel da ake safarar 'yan mata da tilasta su yin karuwanci a Katsina

NAPTIP ta ceto wasu 'yan mata 3 da aka yi safararsu daga Kudu zuwa Katsina ana tilasta su karuwanci
Wasu 'yan mata uku zaune a cikin dakin otel, inda suke cikin damuwa da karuwanci da suke yi. Hoto: Sani Hamza/Staff
Source: Original

Jami'in yaɗa labaran NAPTIP, Vincent Adekoye, ya tabbatar da hakan a cikin sanarwar da ya fitar ranar Laraba, 9 ga Yuli, kamar yadda Channels TV ta ruwaito.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An bankado masu safarar mutane a Katsina

Vincent Adekoye ya kuma ce jami'an hukumar na reshen Katsina sun samu nasarar cafke mutum uku da ake zargin mambobin kungiyar safarar mutanen ne.

Hukumar ta bayyana cewa an kama waɗanda ake zargin a ɗaya daga cikin manyan otel-otal a cikin garin Katsina (amma ba a bayyana sunansa ba).

An kuma kama manajan otel ɗin da wasu ma'aikata biyu yayin farmakin, a cewar sanarwar mai magana da yawun NAPTIP.

Mun ruwaito cewa Vincent Adekoye ya bayyana cewa yayin farmakin, an gano waɗanda aka ceto a wani ɗan ƙaramin ɗaki cikin otel din da ke cike da kazanta.

Yadda aka yi safarar 'yan matan zuwa Katsina

Sanarwar ta ƙara da cewa an yi safarar 'yan matan, masu shekaru tsakanin 21 zuwa 26, daga Jihohin Benue da Rivers, kuma an tilasta musu yin karuwanci a Katsina.

Kara karanta wannan

Sojoji, 'yan sanda sun gwabza fada da 'yan bindiga a Katsina, an rasa rayuka 36

Da take magana da jami'an NAPTIP bayan an ceton su, ɗaya daga cikin 'yan matan ta ba da labarin bakar wahalar da ta sha a hannun mutanen.

Ta labarta cewa:

“Wata mata ce ta kawo ni nan. Ta yi alƙawarin ba ni aiki kuma ta ce za a rika biya na kudi masu yawa. Na tambaye ta irin aikin, amma ta ce zan gani idan na iso nan.
"Sai dai lokacin da muka iso nan, don ba ni kadai ba ce ta dauko, sai ta gabatar mana da harkar karuwanci, wadda ba ita ce sana'ar da ta yi mana tayi ba tun farko."
'Yan matan da aka ceto a otel din Katsina sun ce suna lalata da maza 20 a kullum
'Yan matan da NAPTIP ta ceto a Katsina sun bayyana bakar wahalar da suka sha. Hoto: @naptipnigeria/X, Sani Hamza/Staff
Source: UGC

"Muna lalata da maza 20 kullum" - Budurwa

Cikin hawaye, budurwar ta ci gaba da cewa:

“Ana tilasta mana yin lalata da akalla maza 20 kowace rana, kuma shugabar wurin, wacce ake kira da Amarachi ne ke karbe dukkanin kuɗin da muka samu.
"Suna tilasta mu kwanciya da maza ko da kuwa a lokacin al’adar mu na wata-wata ne ko kuma idan muna rashin lafiya, ko kuma mun gaji daga mazan da muka yi lalata da su.

Kara karanta wannan

JAMB ta saki bayanan dalibin da ya fi kowa samun maki a jarabawar UTME 2025

"Sun gaya mana cewa jin daɗinmu ko halin da muke ciki ba shi da muhimmanci – kuɗi ne kawai ke da mahimmanci a wajensu. Har ma suna ba mu abubuwan sha masu ƙarfi irin su Fearless kowane dare don mu ci gaba da aiki.”

Wadda aka aka ceton ta kuma bayyana cewa masu fataucin sun dauki hayar wasu maza da ke kula da su don a hana su guduwa da kuma tabbatar da ci gaba da cin zarafin su.

"Na yi lalata da maza 3,000" - Jarumar fim

A wani labarin, mun ruwaito cewa, fitacciyar jarumar fina-finan Nollywood, Esther Nwachukwu, ta bayyana wasu bayanai da ke ɗaukar hankalin jama'a dangane da irin rayuwarta ta sirri.

A yayin wata hira da aka yi da ita a shirin 'Honest Bunch', jarumar ta bayyana cewa tana da ƙarfin sha’awa fiye da yadda mutane ke zato, lamarin da ya ja hankalin masu sauraro.

Esther ta kuma bayyana cewa a cikin shekaru 30 da suka gabata, ta yi hulɗar soyayya da maza kusan 3,000 a wurare daban-daban ciki har da wasu ƙasashen waje da garuruwan Najeriya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com