Gwamnatin Tinubu Ta Karbo Bashin Dala Miliyan 747 domin Aikin Titi a Legas

Gwamnatin Tinubu Ta Karbo Bashin Dala Miliyan 747 domin Aikin Titi a Legas

  • Gwamnatin tarayya ta samu lamunin Dala miliyan 747 domin kammala ginin sashen farko na titin Legas-Calabar
  • Lamunin ya zama mafi girma a tarihin Najeriya da aka samu don aikin gina hanya daga masu zuba jari na duniya
  • An ce aikin ya kai fiye da kashi 70 cikin 100, kuma ana amfani da fasaha domin ganin aikin ya kai shekara 50 da karfinsa

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Ma’aikatar kudi ta bayyana cewa gwamnatin tarayya ta samu bashin Dala miliyan 747 domin kammala wani sashe na aikin babbar hanyar Legas-Calabar.

Rahotanni sun bayyana cewa aikin da za a yi da kudin ya fara daga yankin Victoria Island zuwa kauyen Eleko a jihar Legas.

Najeriya ta karbo bashi domin karasa aikin titin Legas Calabar
Najeriya ta karbo bashi domin karasa aikin titin Legas-Calabar. Hoto: Bayo Onanuga
Source: Facebook

Vanguard ta ce sanarwar ta fito daga daraktan yada labarai na ma’aikatar, Mohammed Manga, wanda ya ce lamunin ne mafi girma da aka taba samu a tarihin Najeriya don aikin titin mota.

Kara karanta wannan

Ana maganar hadaka, Dangote ya rubutawa Bola Tinubu budaddiyar wasika

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cewarsa, hakan na nuni da yadda masu zuba jari na duniya ke kara samun kwarin gwiwa kan shirin gyaran tattalin arzikin gwamnatin Shugaba Bola Tinubu.

Kamfanoni da suka ba da bashi kan aikin

Bankin Deutsche ne ya jagoranci samar da wannan lamunin tare da wasu manyan cibiyoyin kudi na cikin gida da na kasashen waje.

Wasu daga cikin sauran manyan masu tallafawa sun hada da bankin First Abu Dhabi, bankin Afrexim, ADEX, bankin EBID, bankin Nexent N.V., da kuma bankin Zenith

Haka zalika, cibiyar musulunci ta ICIEC ta bayar da inshora don tabbatar da amincin kudin da aka zuba.

Ana aiki da fasaha wajen aikin titin

Aikin gina wannan hanya na karkashin tsarin EPC+F, wanda ke nufin Engineering, Procurement, Construction da Financing.

The Guardian ta wallafa cewa wannan tsari ne da ke bai wa kamfanonin kudi da masu gine-gine damar yin aiki tare.

Kara karanta wannan

Bayan zargin badakala, Peter Obi ya fadi alakar da ta hada shi da Abacha

Kamfanin gini na Hitech da ke daya daga cikin manyan kamfanonin gine-gine na Najeriya, shi ne ke jagorantar aikin.

Ma’aikatar kudi ta bayyana cewa tuni aikin ya kai sama da kashi 70 cikin 100, alamar da ta nuna ya kusa kammaluwa.

Ana amfani da fasahar CRCP wato Continuously Reinforced Concrete Pavement, fasahar da ke ba hanya damar daukar shekaru 50 ba tare da gyara ba.

Maganar ministan kudi kan bashin

Ministan kudi kuma mai hada-hadar tattalin arziki, Wale Edun, ya ce wannan lamuni na nuni da yadda duniya ke kara amincewa da Najeriya karkashin gwamnatin Tinubu.

Edun ya ce:

“Wannan yarjejeniya na nuna yadda muke dagewa wajen samar da kudi cikin gaskiya da bin doka, don gina manyan ayyuka da za su amfani ‘yan kasa."
Ministan kudin Najeriya, Wale Edun
Ministan kudin Najeriya, Wale Edun. Hoto: Federal Ministry of Finance
Source: Getty Images

Ginin titi: Dangote ya yabawa Tinubu

Edun a ce: on, kun ji cewa Alhaji Aliko Dangote ya yaba wa shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu kan ayyukan raya kasa.

Aliko Dangote ya yaba da yadda Bola Tinubu ya ke aikin manyan tituna a yankuna daban daban na kasar nan.

Haka zalika, Dangote ya yaba da matakan da gwamnatin shugaba Tinubu ke dauka wajen magance matsalar ambaliyar ruwa a Najeriya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng