Majalisa Ta Kira Gwamna, Tsofaffin Gwamnoni, Jami'an Tsaro kan Kashe Kashe
- Kwamitin wucin gadi kan rashin tsaro a Filato ya fara laluben yadda za a magance asarar rayuka a sassa daban-daban na jihar
- Kwamitin ya gayyaci Gwamna Caleb Mutfwang, tsofaffin gwamnoni da shugabanni domin neman mafita kan rikice-rikicen
- Taron zai hada da shugabannin addini, hukumomin tsaro, kungiyoyin matasa da na farar hula, da kungiyoyin wanzar da zaman lafiya
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT Abuja – Kwamitin wucin gadi na Majalisar Wakilai kan matsalolin tsaro a jihar Filato ya bayyana damuwa matuka kan tabarbarewar tsaro a jihar.
Wannan ta sa ya gayyaci Gwamna Caleb Mutfwang, tsofaffin gwamnonin jihar da sauran shugabannin al’umma domin halartar babban taron tsaro na musamman.

Source: Facebook
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa taron zai mayar da hankali ne kan shawo kan tashe-tashen hankula da kashe-kashen da ke faruwa a jihar Filato.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Majalisa na nemawa Filato mafita
BBC Hausa ta wallafa cewa shugaban kwamitin, Dr. Wale Hammed, ya ce taron wani bangare ne na kokarin tattara shawarwari da hanyoyin magance matsalar rikici a Filato..
Ya kara da cewa ana yawan kashe mutane a yankunan Bokkos, Bassa da Mangu—inda kisan gilla da hare-hare suka zama ruwan dare ga yan gari da matafiya.
Dr. Hammed ya kuma bayyana cewa an buɗe kafa domin karɓar ra’ayoyi da shawarwarin jama’a daga masu ruwa da tsaki, domin tabbatar da warware matsalolin.
Ya ce:
“Majalisa ita ce za ta iya fuskantar kalubalen kare rayuka da dukiyoyin ‘yan kasa. Wannan taro na neman mafita ne, ba don kara rarrabuwar kawuna ba.”
Ana fama da kashe-kashe a Filato
Majalisa ta ce an shirya taron bayan muhawara a majalisa a watan Mayu da Yuni kan kashe mutane 13 a Rimi, Basawa Sabon, a Mangu da kuma sauran hare-hare.
Dr. Hammed ya ce kwamitin yana aiki ne bisa tanadin sashe na 88 da 89 na Kundin Tsarin Mulki na 1999, domin tabbatar da adalci da samun sahihiyar fahimta daga masu ruwa da tsaki.
Daga cikin wadanda ake sa ran za su halarci taron akwai: Gwamna Caleb Mutfwang, da tsofaffin gwamnonin Filato: Simon Lalong, Jonah Jang da Joshua Dariye

Source: Facebook
Sai kuma Sanatoci da ‘yan majalisar wakilai daga jihar, da shugabannin kananan hukumomi da sarakunan gargajiya da shugabannin addinai, kungiyoyin matasa da farar hula.
Sauran su ne shugabannin hukumomin tsaro: Sojoji, ‘Yan sanda, DSS, NSCDC da jami’an 'Operation Safe Haven' na yanzu da na baya da kungiyoyin CAN, JNI da Miyetti Allah.
Yan bindiga sun tare jama'a a Filato
A baya, kun samu labarin cewa wasu ‘yan bindiga sun kai mummunan hari kan wasu mutane a kauyen Rim da ke karamar hukumar Riyom, jihar Filato.
Maharan sun farmaki wasu matasa da ke dawowa daga jana’iza, suka harbi mutum daya sannan suka yanke hannunsa, yayin da suka jefa jama'a a firgici.
Masu makokin dai sun fito ne daga jana’izar wani mamaci a kauyen Bachit, kafin ‘yan bindigar su tare su a hanya suna dawowa gida tare da yi masu ɓarna.
Asali: Legit.ng

