Ba Rufa Rufa: Za a Fito da 'Yan Filato da Suka Kashe Hausawan Zariya Fili a Kotu
- Rundunar ‘yan sanda ta jihar Plateau za ta gurfanar da mutum 22 da ake zargi da hannu a kisan matafiyan Zaria a yau, 10 ga Yuli
- Mutane 13 daga cikin baki 31 da suka nufi Qua’an Pan daga Zaria sun mutu bayan da suka fada hannun matasa a garin Mangun
- Rahoto ya nuna cewa ‘yan sanda sun gayyaci ‘yan jarida su halarci shari’ar da za a yi a Kotun Kolin Jihar Plateau a yau Alhamis
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Plateau – Rundunar ‘yan sandan jihar Plateau ta bayyana cewa za ta gurfanar da mutum 22 a gaban kotu bisa zargin da ake musu na hannu a kisan matafiyan Kaduna a garin Mangun.
An shirya gurfanar da wadanda ake zargi ne a ranar Alhamis, 10 ga Yuli, 2025 a Kotun Kolin jihar Plateau, kotu ta 10, kamar yadda sanarwar rundunar ta tabbatar wa da manema labarai.

Source: Facebook
Rahoton jaridar Leadership ya nuna cewa rundunar 'yan sandan jihar ta gayyaci 'yan jarida su shaida shari'ar.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Lamarin ya faru ne a ranar 21 ga watan Yuni, inda wasu matafiya su 31 daga Basawa a Zaria, Kaduna, suka nufi Qua’an Pana a Plateau domin wani bikin aure, sai suka fada cikin iftila’in.
Yadda aka kashe matafiyan Zariya
Rahotanni sun nuna cewa baƙin sun gaza gane hanya sai suka tsaya a Mangun domin tambayar hanyar da za su bi, amma sai wani taron matasa ya far musu da duka da kuma kisa.
Legit Hausa ta rahoto cewa a cikin mummunan harin, mutane 13 ne suka mutu, ciki har da mata da yara.
Al’amarin ya tayar da kura a tsakanin jihohin Kaduna da Plateau, musamman ganin cewa wadanda abin ya rutsa da su ba su da alaka da wani rikici.
Za a gurfanar da wadanda aka kama
Kakakin rundunar ‘yan sanda ta jihar Plateau, DSP Alfred Alabo, ya ce an riga an gayyaci ‘yan jarida da su halarci zaman kotun da za a yi a safiyar ranar Alhamis da karfe 9:00 na safe.
A cewar DSP Alabo:
“Za mu kwashe ‘yan jarida daga kotu zuwa hedikwatar rundunar ‘yan sanda bayan shari’a, inda Kwamishinan ‘yan sanda zai gana da su domin karin bayani.”
Ya kara da cewa za a tanadar da motar daukar ‘yan jarida daga kotu zuwa hedikwatar rundunar domin saukaka musu zirga-zirga.

Source: Twitter
Rundunar ‘yan sanda ta ce tana gudanar da bincike mai zurfi kan lamarin kuma za ta tabbatar da cewa kowa ya fuskanci hukunci bisa laifin da ya aikata.
Yadda ta'addancin Filato ya kashe mutane da yawa
Rikicin jihar Filato ya samo asali tun a shekarun 2001, lokacin da rikicin kabilanci da na addini ya barke a babban birnin Jos, ya kuma bazu zuwa wasu sassan jihar.
Wannan rikici ya samo asali ne daga takaddama kan mallakar ƙasa, siyasa, bambancin kabila da addini, inda kabilu irin su Berom, Afizere da Anaguta suka dade suna rikici da Fulani makiyaya da sauran kabilun Arewa da ke zaune a Jos da kewaye.
A mafi yawan lokuta, rikicin yana samo asali ne daga yawan kai farmaki da kashe-kashe tsakanin manoma da makiyaya, inda kowane ɓangare ke zargin ɗaya da laifi.
Wannan ya jawo dubban rayuka sun salwanta, gidaje da filaye sun lalace, sannan al’ummomi da dama suka rasa matsuguni.
Rikicin ya taɓa sauya salo zuwa na addini a wasu lokuta, musamman a Jos ta Arewa da Kudu, inda musulmi da kiristoci ke fama da rashin jituwa.
Duk da kokarin gwamnatin tarayya da ta jiha wajen kawo zaman lafiya, har yanzu ana ci gaba da samun hare-hare lokaci zuwa lokaci.
Harin da ya faru a Mangun, inda matafiya daga Zaria aka kashe, wani sabon alamar cewa rikicin Filato bai kawo ƙarshe ba duk da tsawon shekarun da ya shafe.
An kashe 'yan banga 70 a jihar Filato
A wani rahoton, kun ji cewa wasu 'yan banga sun hadu da jarrabawa yayin da suka yi kokarin kai farmaki kan wasu 'yan bindiga a jihar.
Yayin da 'yan bangar suka nufi maboyar 'yan ta'addan, 'yan bindigan sun yi kwanton bauna sun kashe da dama daga cikinsu.
Wani daga cikin 'yan bangar ya bayyana cewa an kashe kimamin mutanensu 70 tare da kona gidaje da dama yayin harin.
Asali: Legit.ng


