'Yan Boko Haram/ISWAP Sun Sha Wuta, Sojoji Sun Hallaka 'Yan Ta'adda Masu Yawa

'Yan Boko Haram/ISWAP Sun Sha Wuta, Sojoji Sun Hallaka 'Yan Ta'adda Masu Yawa

  • Dakarun sojojin Najeriya sun kai hare-hare kai maɓoyar ƴan ta'addan Boko Haram da ISWAP a jihohin Adamawa da Borno
  • Jami'an tsaron sun samu nasarar hallaka ƴan ta'adda da dama a hare-haren da suka kai musu
  • Hakazalika sun ƙwato makamai, babura, kekuna da sauran kayayyaki daga hannun ƴan ta'addan

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Borno - Dakarun sojojin rundunar Operation Hadin Kai tare da haɗin gwiwar sashen sojojin sama, CJTF da mafarauta, sun kashe ƴan ta’addan Boko Haram/ISWAP guda 24.

Dakarun sojojin sun hallaka ƴan ta'addan ne a jerin hare-haren da aka gudanar a jihohin Borno da Adamawa daga ranar 4 zuwa 9 ga watan Yuli.

Sojoji sun hallaka 'yan ta'addan Boko Haram
Sojoji sun kashe 'yan ta'addan Boko Haram Hoto: @HQNigerianArmy
Source: Facebook

Masani kan harkokin tsaro a yankin Tafkin Chadi da Arewacin Najeriya, Zagazola Makama ya bayyana hakan a shafinsa na X.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sojoji sun kashe ƴan ta'addan Boko Haram/ISWAP

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun kai hari a Katsina, an kashe mutane ciki har da malamin addini

Majiyoyi sun bayyana cewa hare-haren da aka ƙaddamar a yankin Arewa maso Gabas, sun lalata maɓoyar ƴan ta’adda da dama, ƙwace makamai, kayan aiki da motocin da suke amfani da su.

A cewar majiyoyin, ɗaya daga cikin farmakin farko ya faru a ranar 4 ga watan Yuli, inda dakarun suka yi kwanton ɓauna a Platari. Sojojin sun buɗe wuta, inda suka kashe uku nan take.

A wannan ranar ma, bayan samun bayanan leƙen asiri game da motsin ƴan ta’adda a kusa da Komala, an ƙaddamar da wani kwantan ɓauna wanda ya yi sanadiyyar kashe wani ɗan ta’adda.

Binciken da aka yi a wurin ya haifar da samun babura, kayan gyara, magungunan feshi da abinci da aka yi nufin kai su ga ƴan ta’adda.

Har ila yau, a ranar 4 ga Yuli, wani kwantan ɓauna da dakarun suka yi da dare a yankin Kawuri na ƙaramar hukumar Konduga ya haifar da kashe wasu ƴan ta’adda biyu da ke ƙoƙarin jigilar kayan abinci.

Kayayyakin da aka samu sun haɗa da gishiri, kayan ɗanɗano, sabulai da sauran kayayyakin masarufi, abin da ke nuna cewa suna ci gaba da shigo da kayan amfanin yau da kullum.

Kara karanta wannan

Wata sabuwa: Gwamna Radda ya yi fallasa kan hadakar 'yan adawa

A wani al’amari daban a ranar 4 ga Yuli, sojojin sun tare wasu ƴan ta’adda da ke ƙoƙarin kutsa wa sansanin ƴan gudun hijira na Madarari da ke Konduga.

An harbe ɗan ta'adda ɗaya, sauran kuma sun tsere da raunuka. An ƙwato alburusai a binciken da aka ci gaba da yi.

A ranar 6 ga Yuli, dakarun sun kai farmaki a maboyar ƴan ta’adda da ke Leno Kura. A wannan harin, an kashe ƴan ta’adda uku.

Wani gagarumin farmaki ya gudana a ranar 8 ga Yuli a Bula Marwa, wani katafaren sansanin ISWAP/JAS. Da taimakon jiragen yaƙi, sojojin sun kashe ɗan ta’adda ɗaya, suka rushe sansanin tare da ƙwato kayan ƴan ta'adda.

Sojoji sun yi gumurzu da ƴan ta'adda

A lokaci guda, sojoji tare da CJTF da mafarauta sun kai farmaki a garin Pambula na ƙaramar hukumar Madagali a jihar Adamawa.

Sojoji sun hallaka 'yan ta'adda a Borno, Adamawa
Sojoji sun kashe 'yan ta'addan Boko Haram a Adamawa da Borno Hoto: @HQNigerianArmy
Source: Facebook

An yi gumurzu da ƴan ta’adda, inda aka kashe ɗaya, kuma an ƙwato babura huɗu da bindigar gida guda ɗaya.

A daren ranar 8 ga Yuli, an ƙara tsananta farmaki a Bula Marwa inda aka sake kashe ɗan ta’adda ɗaya tare da rushe wani sansanin daban.

Kara karanta wannan

ADC ta shiga Borno da karfinta, tana wawashe yan PDP da APC gabanin 2027

A ranar 9 ga Yuli, an kai babban farmaki a Tangalanga da Bula Marwa, inda aka kashe ƴan ta’adda uku bayan musayar wuta mai tsanani.

Sojojin sun ƙwato bindigun AK-47 guda shida, manyan alburusai 47, da harsasai 90 masu kaurin 7.62mm. An kuma lalata dukkan kayan more rayuwar sansanin.

A ci gaba da aikin, sojojin sun yi kwantan ɓauna a ƙauyukan Ngailda, Manjim, da Wulle. Bayan yin gumurzu, sun kashe ƴan ta’adda shida, kuma sun ƙwato babura da kekuna.

Wannan jerin nasarori sun hana ƴan ta’adda damar samun kayan abinci da makamai ta hanyoyin da suka saba bi.

Sojoji sun daƙile shirin ƴan ta'adda

A wani labarin kuma, kun ji cewa dakarun sojojin Najeriya sun samu nasarar daƙile wani shirin ƴan ta'adda na dasa bama-bamai a jihar Borno.

Sojojin tare da haɗin gwiwar ƴan sa-kai sun gano wasu bama-bamai da ƴan ta'addan suka binne a kan hanyar Marte zuwa Dikwa.

Majiyoyi sun bayyana cewa ana zargin ƴan ta'addan Boko Haram ne suka binne bama-baman domin cutar da mutanen da ke bin hanyar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng