Ganduje Ya Yi Magana a Karon Farko bayan Shugaba Tinubu Ya ba Shi Muƙami a FAAN

Ganduje Ya Yi Magana a Karon Farko bayan Shugaba Tinubu Ya ba Shi Muƙami a FAAN

  • Tsohon shugaban APC na ƙasa, Dr. Abdullahi Ganduje ya kama aiki a matsayin shugabam Majalisar gudanarwa ta hukumar FAAN
  • Bayan kama aiki a jiya Laraba, Ganduje ya bayyana cewa shi da sauran abokan aikinsa za su yi aiki tuƙuru domin bunƙasa hukumar FAAN
  • Ya ce za su duba kundin dokokin hukumar kula da filayen jiragen sama domin tabbatar da cewa ba su ketare iyakar doka ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja - Gwamnatin tarayya ƙarƙashin Shugaba Bola Tinubu ta kawo ƙarshen shakaru 13 da hukumar kula da filayen jiragen sama ta ƙasa (FAAN) ta yi babu Majalisar gudanarwa.

Ministan harkokin sufurim jiragen sama, Festus Keeyamo ya kaddamar da Majalisar gudanarwa ta FAAN, wadda tsohon shugaban APC, Abdullahi Ganduje ke jagoranta.

An nada Ganduje a FAAN.
Gwamnatin Tarayya ta rantsar da Ganduje a matsayin sabon shugaban Majalisar gudanarwa ta FAAN Hoto: @FAAN_Official
Source: Twitter

Binciken Daily Trust ya nuna cewa a shekaru 8 da Muhammadu Buhari ya yi a kan mulki, ba a kafa majalisar gudanarwa a FAAN da sauran hukumomin jiragen sama ba.

Kara karanta wannan

APC: 'Yan siyasar Arewa sun fara neman kujerar Ganduje gadan gadan

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ganduje ya kama aiki a hukumar FAAN

An kaddamar da Ganduje, tsohon gwamnan jihar Kano, tare da sauran mambobin majalisar, ciki har da Manajan Darakta na FAAN, Olubunmi Kuku.

Sauran sune Dorothy Duruaka; Ahmed Ibrahim Suleiman; Injiniya Nasiru Muazu; Omozojie Okoboh; Injiniya TP Vembe, da Bridget Gold, wadda za ta rike mukamin Sakatariyar Majalisar.

Ganduje ya sha alwashin cewa Majalisar za ta yi nazari kan dokar kafa FAAN domin tabbatar da cewa ba ƙetare iyaƙar ikon da doka ta ba su ba, Vanguard ta rahoto.

Ministan Tinubu ya ja hankalin su Ganduje

A yayin bikin kaddamarwar da aka gudanar a Abuja, Ministan Sufurin Jiragen Sama, Festus Keyamo, ya bayyana cewa:

“Yayin da muke kaddamar da ku, muna fatan zamu haɗu mu ci gaba da samar da yanayi da zai ba fannin sufurin jiragen sama damar bunƙasa, ya haɗa sassa daban-daban na ƙasa, kuma ya inganta zamantakewa da tattalin arziki a faɗin Najeriya.”

Kara karanta wannan

Gwamnatin Bola Tinubu ta ba Ganduje mukami a FAAN, ya fara aiki

Keyamo ya bukaci mambobin Majalisar gudanarwar da su tallafa wa hukumar FAAN tare da aiwatar da ayyukansu bisa yadda doka ta tanada.

Shugaban Majalisar gudanarwar FAAN, Abdullahi Ganduje.
Ganduje ya yi jawabin farko bayan karɓar muƙami a gwamnatin Tinubu Hoto: @sisinaabdallah5
Source: Twitter

Ganduje ya yi magana bayan kama aiki a FAAN

Da yake martani, sabon shugaban Majalisar gudanarwar FAAN, Dr. Ganduje, ya tabbatar da kudurinsu na haɗa kai da ma’aikatar sufurin jirage domin ci gaban hukumar.

Ganduje ya ce:

“A matsayina na shugaban wannan majalisa, tare da sauran mambobi, za mu taimaka wajen ɗaukaka wannan ma’aikata zuwa mataki na gaba.
"Babu shakka, za mu nazarci dokar kafa FAAN domin sanin iyakokin mu, don kada mu ƙetare doka. Na san wannan matsala ce da ke yawan faruwa tsakanin masu gudanarwa da shugabannin hukumomi da ma’aikatu.
Mun fahimci hakan sosai. Saboda haka, ni da mambobin majalisar nan za mu tabbata mun yi aiki bisa doka ba tare da zarce iyaka ba, kuma ba za mu zama marasa tasiri ba ta hanyar kasa cika ayyukan da ake tsammani daga gare mu.”

Matsalar da Ganduje ya fara shiga a APC

Ganduje ya fara bayyana cewa akwai gibba da matsaloli masu ƙarfi a cikin jam’iyyar APC, musamman bayan saukarsa daga kujera cikin takaddama da rashin goyon bayan wasu jiga-jigan jam’iyyar.

Kara karanta wannan

Yadda jagororin APC suka ki tarbar Kashim Shettima a Kano bayan Ganduje ya yi murabus

Wannan sauyi ya zo ne a daidai lokacin da aka ba shi sabon mukami a matsayin shugaban Majalisar gudanarwa ta hukumar kula da filayen jiragen sama ta ƙasa (FAAN).

A yayin da ya kama aiki a sabon matsayinsa, Ganduje ya bayyana cewa zai mai da hankali wajen inganta FAAN bisa doka da tsarin aiki.

Wannan na iya nuna cewa tsohon gwamnan na Kano ya koma gefe a harkar siyasar jam’iyyar APC, bayan ya fuskanci karancin goyon baya da yuwuwar fitina daga cikin gida.

Ganduje, wanda ke da shekaru masu yawa a siyasa, ya ce yana son kaucewa matsalolin rashin fahimta da suka addabi shugabannin da aka ɗora musu nauyin jagoranci.

A halin yanzu, yana mai da hankali kan sabon aikinsa a FAAN, yayin da wasu ke ganin hakan wata hanya ce ta kaucewa rikicin siyasar jam’iyyar da ya fara hango rauni da tabarbarewa a cikinta.

Kamfanin sufurin jiragen Enugu Air ya fara aiki

A wani labarin, kun ji cewa ministan sufurin jiragen sama, Festus Keyamo ya jagoranci kaddamar da kamfanin sufuri na Enugu Air.

Kara karanta wannan

Kisan Danbokolo: Abin da al'umma suka shirya saboda tsoron abin da ka iya biyo baya

Keyamo ya ce Gwamna Mbah na jihar Enugu yana daya daga cikin gwamnonin da suka fi kowa kyakkyawan aiki a Najeriya.

Ministan ya kuma buƙaci Gwamna Mbah ya kula da kamfanin sufurin jiragen sama na Enugu Air, kada ya bari siyasa ta shiga cikin harkokin gudanarwa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262