Ba Kamar Yadda AKe Zato Ba, Akpabio Ya Fadi Dalilin Zuwansu Majalisa
- Shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio ya fadi abin da suka sanya a gaba a majalisa domin kawo cigaba
- Akpabio ya ce ‘yan majalisa ba don neman kudi suke ba, sai don sadaukarwa da cigaban al’umma masu zuwa
- Hakan ya biyo bayan Majalisar Dattawa ta fara nazarin gyara dokar wutar lantarki don warware rikice-rikicen da ke hana cigaba
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
FCT, Abuja - Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, ya bayyana abin da ya kai su majalisa a Najeriya.
Akpabio ya bayyana cewa ba don tara kudi ‘yan majalisa ke zama a majalisa ba, sai don sadaukarwa.

Source: Facebook
Ana tattunawa kan dokar gyaran wutar lantarki
Ya bayyana hakan ne yayin tattaunawa kan sabuwar dokar gyaran wutar lantarki wadda ke neman warware matsaloli a bangaren samar da lantarki, cewar Vanguard.

Kara karanta wannan
Bauchi: Sarakuna sun aika sako ga magoya baya kan shirin kirkirar sababbin masarautu
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A cikin jawabinsa, Akpabio ya bayyana cewa babu yadda za a samu ci gaban masana'antu a kasar nan idan babu wutar lantarki. Ya ce kowa na fatan a yi garambawul gaba ɗaya ga bangaren wutar lantarki.
Akpabio ya fadi nufinsu ga yan Najeriya
Akpabio ya ce gyaran dokar zai taimaka wajen sauya tsarin wutar lantarki gaba daya domin samar da ci gaba ga masana’antu da kasa baki daya.
A cewarsa, jama’a na ganin ‘yan majalisa na neman kudi ne kawai, amma a gaskiya suna sadaukarwa ne domin cigaban ‘ya’yansu da al’umma gaba daya.
Akpabio ya ce:
“Mutane na tunanin muna nan a Majalisar Dattawa don neman kudi, ba tare da sanin cewa muna nan ne domin sadaukarwa ga al’ummomin gaba ba.”

Source: Facebook
Abin da kudirin gyaran wuta ke kunshe da shi
Sabon kudirin na majalisa zai taimaka wajen kaucewa rikice-rikice na doka tsakanin gwamnati da jihohi game da harkar wutar lantarki.
Za a kuma karfafa batun daukar nauyin bangaren wutar lantarki tare da samar da tsari mai inganci na hulda da al’umma da ma’aikata.
Sanata Enyinnaya Abaribe, wanda ya dauki nauyin kudirin, ya ce ana so a cire ruɗani daga dokar da aka yi a baya domin ta fi sauƙi da fahimta, cewar The Nation.
Matakin da za a dauka kan wutar lantarki
Za a kara karfi wajen hukunta masu lalata kayan aikin wutar lantarki da samar da kariya ga al’ummomin da masu wutar ke aiki a cikinsu.
Majalisar ta tura kudirin zuwa kwamitin wutar lantarki domin ci gaba da nazari, inda ake sa ran rahoto zai dawo a cikin makonni shida.
Akpabio ya shawarci Obi kan takara a 2027
Kun ji cewa shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio ya soki Peter Obi kan maganar da ya yi cewa "aikin 'yan mazan jiya ya zama na banza".
Godswill Akpabio ya bukaci Peter Obi da ya fara magance rikice-rikicen da ke addabar jam'iyyar LP kafin ya ce zai shugabanci Najeriya.
Shugaban majalisar ya kuma zayyano nasarorin da ya samu a matsayinsa na gwamna, ya ce ya biya wa Musulmi 5,800 kudin aikin Hajji.
Asali: Legit.ng
