Gwamna Ya Fitar da N7.7bn, Zai Siyo Jiragen Sama Masu Gano Maɓoyar Ƴan Bindiga
- Gwamnatin Oyo ta amince da kashe N7.7bn domin siyan jirage biyu da za su rika aikin ganowa da tarwatsa ‘yan bindiga a maboyarsu
- Kwamishinan watsa labarai, Dotun Oyelade ya ce jiragen kirar DA42 MNG za su taimaka wa Amotekun da sauran jami’an tsaro a fadin jihar
- Oyelade ya bayyana cewa Amotekun a Oyo na da jami’ai 2,500, motocin aiki 181 da babura 450 tare da mafi ƙarancin albashi na N116,000 a wata
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Oyo - Gwamnan Oyo, Seyi Makinde ya fitar da ₦7,763,360,000 domin siyan jiragen leken asiri biyu da nufin dakile ayyukan 'yan bindiga da masu hakar ma’adinai ba bisa ka’ida ba.
Kwamishinan yada labaran jihar, Prince Dotun Oyelade, ya kare kudirin sayen jiragen da cewa mataki ne na yaki da matsalolin tsaro da ke addabar Oyo.

Source: UGC
Gwamnatin Oyo za ta sayo jiragen DA42 MNG
A cewar Oyelade, sayen jiragen zai ba da damar kara ƙaimi wajen yaki da masu hakar ma’adinai ba bisa ka’ida ba, da masu garkuwa da mutane da sauran 'yan ta'adda, inji rahoton Leadership.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kwamishinan yada labaran ya bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da ya fitar bayan zaman majalisar zartarwa na jihar da aka gudanar a ranar Laraba.
Oyelade ya ce an amince da sayen jiragen ne a wani yunƙuri na kara tsaurara matakan tsaro a jihar don dakile shigowar ‘yan bindiga da ayyukansu.
Ya bayyana cewa duk da jihar Oyo na cikin zaman lafiya idan aka kwatanta da wasu jihohi, gwamnati ba za ta ki daukar matakai ba ganin yadda ake samun hare-hare a wasu sassan jihar.
Dalilin Oyo na son sayen jiragen DA42 MNG
Prince Dotun Oyelade ya kara da cewa:
“Za a sayi jiragen biyu kirar DA42 MNG ne, wanda aka kera musamman domin leƙen asiri da sa ido, kuma suna ɗauke da na’urorin gano ababen harinsu daga nesa ko kusa."
Ya ce an zaɓi wannan nau’in jirgin ne maimakon jirage masu saukar ungulu saboda sauƙin kula da su da kuma samun kayan gyaransu cikin sauƙi.
Haka kuma, ya ce rundunar sojin saman Najeriya na da irin wannan jirgi, don haka hakan zai ba da damar haɗin gwiwa a tsare-tsaren tsaro.

Source: Getty Images
Mafi karancin albashin Amotekun ya kai N116,000
Prince Dotun Oyelade ya ce:
“Za a kashe N7,763,360,000 don sayo jiragen kuma za su tallafa wa rundunar Amotekun da sauran jami’an tsaro wajen ganowa da tarwatsa ‘yan bindiga a maboyarsu."
Oyelade ya bayyana cewa rundunar Amotekun ta jihar Oyo ce ke da mafi yawan jami’ai a shiyyar Kudu maso Yamma, da jami'ai 2,500, motoci 181 da babura 450.
Ya kuma ce jami'an Amotekun a Oyo na karɓar mafi girman albashi a shiyyar, inda mafi ƙarancin albashin jami'ai ya kai ₦116,000 duk wata.
Najeriya ta siyo jiragen yaki 12 daga Faransa
A wani labarin, mun ruwaito cewa, rundunar sojin saman Najeriya ta bayyana cewa gwamnati ta kammala sayen jiragen yaƙi kirar Alpha Jet guda 12 daga Faransa.

Kara karanta wannan
'Na raina albashin': Hadimin Sanata ya yi murabus daga muƙaminsa bayan shekaru tare
Hafsan sojin sama, Air Marshal Hassan Abubakar, ya ce rundunar na shirin karɓar karin jiragen yaƙi kirar M-346FA, T-129 da kuma wasu jiragen saukar ungulu.
Rahotanni sun bayyana cewa jiragen Alpha Jet suna da matuƙar amfani wajen ɗaukar makamai da gudanar da hare-hare kusa da inda sojoji ke aiki.
Asali: Legit.ng

