Jerin gwamnoni huɗu da suka ɗauki tsauraran matakan kawo karshen 'yan bindiga a jihohin su

Jerin gwamnoni huɗu da suka ɗauki tsauraran matakan kawo karshen 'yan bindiga a jihohin su

Gwamnoni a Najeriya na cigaba da ɗaukar tsauraran matakan yaki da nufin dakile matsalar tsaro da ke ƙara taɓarɓarewa a jihohin su.

Yan ta'adda, yan fashin daji, yan fashi da makami, masu garkuwa da mutane da sauran kashe-kashen masu aikata muggan laifuka na cigaba da hana zaman lafiya a wasu sassan Najeriya.

Sai dai wasu gwamnoni da lamarin ya shafi jihohin su, sun ɗauka matakai masu tsauri na ƙara wa jami'an tsaro ƙarfi, da ba jama'a damar kare kai da nufin dawo da zaman lafiya.

Gwamnoni sun ɗauki tsauraran matakai.
Jerin gwamnoni huɗu da suka ɗauki tsauraran matakan kawo karshen 'yan bindiga a jihohin su Hoto: thenationonlineng.net
Asali: UGC

Legit.ng Hausa ta tattaro muku wasu gwamnoni huɗu, waɗan sa a ƴan kwanakin nan suka bayyana sabbin matakan da zasu ɗauka don shawo kan kalubalen.

Gwamna Matawalle na jihar Zamfara

Gwamna Bello Matawalle na jihar Zamfara ya umarcin al'umma mazauna jihar su mallaki bindigu don kare kansu daga yan bindiga waɗan da suka hana su zaman lafiya.

Kara karanta wannan

Gwamnan APC ya ba 'yan bindigan jiharsa wa'adin kwana 10 su miƙa wuya ko a tura su Lahira

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

The Nation ta rahoto cewa Ya umarci hukumomin tsaro su harbe duk wanda suka gani kan Mashin don tunatar musu cewa dokar hana hawa Mashin na nan daram a jihar Zamfara.

Kwamishinan yaɗa labarai na jihar Zamfara, wanda ya sanar da sabbin matakan da gwamnatin Matawalle ta ɗauka, ya ce:

"Daga yau gwamnati ta umarci ɗai-ɗaikun mutane su mallaki bindigu don kare kansu daga 'yan bindiga, ta umarci kwamishinan yan sanda ya ba da lasisi ga mutanen da suka shirya kuma suka cancanci mallakar bindiga da nufin kare kan su."
"Gwamnati ta kammala shirye-shiryen raba Fom 500 ga masarautu 19 da ke faɗin jihar domin mutanen da suke da niyyar mallakar bindiga don kare kan su. Kara taɓarɓarewar tsaro abin damuwa ne matuƙa."
"Gwamna ya kuma hana hawa Babur da siyar da Man Fetur a yankunan Moda, Wonaka, Ruwan Bore da 'Yan Doto. An kulle duk gidajen Man yankin, duk wanda aka gani a Babur a yankunan za'a dauka ɗan bindiga ne."

Kara karanta wannan

2023: Guguwar sauya sheƙa ta mamaye PDP, mambobi sama da 5,000 sun koma APC a jiha ɗaya

Gwamna Hope Uzodinma na Imo

Gwamnan jihar Imo, Hope Uzodinma, ya bai wa yan bindigan da ke faɗin jihar wa'adin kwanaki 10 su miƙa wuya tare da aje makamansu ko kuma su fuskanci ruwan wuta.

Daily Trust ta rahoto cewa gwamnan, wanda ya yi jawabin a gidan gwamnati dake Owerri, ya ce gwamnatinsa ta yanke kawar da dazukan jihar Imo, waɗan da yan bindiga ke samun mafaka.

Gwamna Hope Uzodinma.
Jerin gwamnoni huɗu da suka ɗauki tsauraran matakan kawo karshen 'yan bindiga a jihohin su Hoto: Hope Uzodinma/facebook
Asali: Facebook

Uzodinma yace daga ranar 27 ga watan Yuni, "Jihar Imo zata fara karɓan kayan aikin sojoji da zata yi amfani da su wajen kawar da baki ɗaya yan bindigan dake ɓuya a dazuka."

Saboda haka gwamnan ya ba yan ta'addan kwanaki 10 su fito daga sansanonin su, "Su kai kansu ga Sarakunan gargajiyan yankunan su domin gwamnati ta duba yuwuwar yafe musu."

Gwamna Seyi Makinde na jihar Oyo

Gwamna Makinde na jihar Oyo ya yi magana kan ɗaukar karin mutum 500 a hukumar tsaro ta jihar WNSN a wurin taron tsaron da ya gudanar tare da Ciyamomi, mataimakansu, shugabannin hukumomin tsaro, Sarakuna da sauran su.

Kara karanta wannan

Da Ɗumi-Ɗumi: 'Yan bindiga sun yi garkuwa a babban ɗan sanda a Nasarawa, sun bukaci Miliyoyi

Gwamnan ya ce:

"Tsaro ya rataya a kan kowa, idan har kowa zai ba da gudummuwarsa yadda ya dace, zamu samu cikakken zaman lafiya kuma mahallanmu zasu kasance a tsare."
"A yanayin ayyukan dakarun Amotekun, mun fara shirin ɗaukar sabbin mutum 500 domin ƙara musu karfi da kuma ƙara inganta tsarin tsaron jihar mu."

Jihar Ondo

Majalisar dokokin jihar Ondo ta ce ta fara shirye-shiryen sake duba dokar da ta kirkiri Amotekun domin daƙile yaɗuwa matsalar tsaro a jihar.

Kakakin majalisar, Gbenga Omole, yace hakan na ɗaya ɗa cikin zantukan da aka tattauna a taron tsaro na Oka, wanda garin Oka ya shirya a ƙaramar hukumar Akoko, a karshen makon nan da ya shude.

Omole, mamba a kwamitin tsaro na majalisar Ondo, ya ce sake nazari kan dokar zai ba dakarun Amotekun damar amfani da Fasaha da kuma manyan makamai don kawo karshen ƙalubalen tsaro.

A wani labarin na daban kuma Bayan ganawa da Buhari, Bola Tinubu ya tafi ƙasar Faransa, An faɗi abinda zai yi

Kara karanta wannan

Gwamnan arewa ya faɗi manyan dalilai uku da suka sa baya iya biyan ma'aikata Albashi a jiharsa

Tsohon gwamnan jihar Legas, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, ya tafi ƙasar Faransa don cigaba da neman shawari bayan gana wa da Buhari.

Mai magana da yawun jigon APC na ƙasa, Tunde Rahman, ya ce Tinubu zai halarci wasu taruka masu muhimmanci a birnin Farisa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel