'Yan Bindiga Sun Kai Hari a Katsina, an Kashe Mutane ciki Har da Malamin Addini
- Wasu ƴan bindiga ɗauke da makamai sun kai hari a ƙaramae hukumar Kafur ta jihar Katsina da ke yankin Arewa maso Yamma
- Ƴan bindigan sun hallaka wani fasto tare da mamba na cocinsa a harin da suka kai a cikin daren ranar Litinin
- Miyagun sun dai kutsa cikin ƙauyen ne sannan suka fara buɗe wuta kan mutanen da ba su san hawa ba, ba su san sauka ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Katsina - Ƴan bindigan sun kashe malamin addinin Kirista da wani mutum guda a wani hari da suka kai a jihar Katsina.
Ƴan bindigan sun kai harin ne a ƙauyen Gidan Taro da ke ƙaramar hukumar Kafur.

Source: Facebook
Masani kan harkokin tsaro a yankin Tafkin Chadi da Arewacin Najeriya, Zagazola Makama, ya bayyana hakan a shafinsa na X.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ƴan bindiga sun kai hari a Katsina
Ƴan bindigan ɗauke da makamai sun kai harin ne a Bege Baptist Church inda suka kashe limamin cocin, Fasto Emmanuel Na’allah, yayin da ake gudanar da ibada.
Ƴan bindigan, waɗanda suka kai harin a daren ranar Litinin, 7 ga watan Yuli, 2025, sun harbe wani mamban cocin mai suna Malam Samaila Goma Gidan Taro har lahira.
Hakazalika sun kuma yi garkuwa da wata mace da ke cikin masu ibada a cocin.
Lamarin dai ya faru ne da cikin dare lokacin da maharan suka shigo ƙauyen suka fara harbi ba tare da kakkautawa ba.
Majiyoyi sun bayyana cewa mutanen guda biyu da aka kashe, Fasto Emmanuel Na’allah Auta mai shekara 46, da Sama’ila Goma Gidan Taro, sun samu munanan raunuka sakamakon harbin bindiga.
An garzaya da su zuwa babban asibitin gwamnati na Malumfashi, amma daga bisani aka tabbatar da rasuwarsu.
Maharan sun kuma yi garkuwa da wata mata mai shekara 25 da haihuwa mai suna Maryam Ezikiel, inda suka tafi da ita zuwa wani wurin da ba a sani ba.
Jami’an tsaro sun je wurin da abin ya faru domin tantance halin da ake ciki, tare da fara aikin farautar waɗanda suka aikata wannan ta’asa.
A halin yanzu, ana ci gaba da kokarin gano inda aka kai Maryam Ezekiel da kuma ceto ta cikin ƙoshin lafiya.

Source: Original
Me ƴan sanda suka ce kan lamarin?
A gefe guda kuma, Legit Hausa ta tuntuɓi jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ƴan sandan jihar, Sadiq Abubakar, domin samun ƙarin bayani kan lamarin.
Kakakin ƴan sandan ya tabbatar da aukuwar lamarin, amma ya ce a jira shi domin yana kan tattara bayanai ne a kan harin.
"Eh ka ɗan jira ni ina tattara bayanai ne a kan harin kafin na fitar da sanarwa."
- Sadiq Abubakar
Gwamna Radda ya yi magana kan ƴan bindiga
A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnan jihar Katsina, Dikko Umaru Radda, ya koka kan matsalar ƴan bindiga.
Gwamna Radda yaa bayyana cewa mafi yawan ƴan bindigan da suka addabi Katsina, ƴan cikin gida ne ba baƙi ba.
Radda ya nuna cewa ƴan bindigan suna rayuwa ne a cikin jama'a, kuma an sansu an san iyayensu har ma da kakanni.
Asali: Legit.ng


