Sanata Ta Tsokano Wike, Ta Fadi Ministan da Ya Fi Shi Aiki a Abuja

Sanata Ta Tsokano Wike, Ta Fadi Ministan da Ya Fi Shi Aiki a Abuja

  • Sanata Ireti Kingibe wacce ke wakiltar babban birnin tarayya Abuja a majalisar dattawa, ta yi kalamai kan Nyesom Ezenwo Wike
  • Ireti Kingibe ta bayyana talakawan Abuja ba su amfana da ayyukan da ministan ya ke cewa yana gudanarwa a babban birnin na tarayyar Najeriya
  • Ta nuna cewa tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai ya fi Wike aiki a lokacin da ya riƙe kujerar ministan birnin tarayya Abuja

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Sanatar da ke wakiltar Abuja a majalisar dattawa, Ireti Kingibe, ta caccaki Nyesom Wike.

Ireti Kingibe ta bayyana cewa Nasir El-Rufai ya fi Wike aiki a matsayin ministan babban birnnin tarayya Abuja

Sanata Ireti Kingibe ta caccaki Wike
Sanata Ireti Kingibe ta ce mutane ba sa ganin aikin Wike a Abuja Hoto: Nyesom Ezenwo Wike - CON, GSSS, Sen. Ireti Kingibe
Source: Twitter

Sanatar ta bayyana haka ne a shirin 'Political Paradigm' na tashar Channels Tv wanda aka watsa a ranar Talata.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cewarta, samun nasara a matsayin ministan Abuja ba ya tsaya ne kawai akan aikin gine-gine da samar da ababen more rayuwa ba.

Kara karanta wannan

'Zuwansa alheri ne': Ribadu ya faɗi yadda Tinubu ya ceto Najeriya daga tarwatsewa

Ireti Kingibe ta ce talakawan Abuja ba sa cin moriyar ayyukan da Wike ke gudanarwa a cikin birnin, inda ta ƙara da cewa ministan bai san matsalolin da jama’a ke fuskanta ba.

Sanata Kingibe ta yabi El-Rufai kan Wike

Sanatar ta ce bata goyon bayan waɗanda ke yaba wa Wike ba dangane da ayyukansa a Abuja, domin kuwa ayyukansa ba su sauƙaƙa rayuwar mazauna birnin ba.

"Idan ka tambayi kowane mazaunin Abuja wanda ya fi kowa aiki a matsayin minista, za su ce maka El-Rufai. Me ya sa? Saboda El-Rufai ya gina tituna, kuma ya riƙa mayar da hankali kan bukatun jama’a."

- Sanata Ireti Kingibe

Ta ƙara da cewa El-Rufai minista ne da idan mutane na fuskantar matsala mai tsanani, baya barin lamarin ya tsaya ga sanata ko wani mutum matsayi, yana tunkarar matsalar kai tsaye.

“Ba za su iya zuwa wurin ba, babu tsaro, babu ruwa, babu komai. Don haka nasarar minista ba ta ta’allaka ne kawai da ababen more rayuwa ba."

- Sanata Ireti Kingibe

Ta jaddada cewa dole ne minista ya kasance mai sauraron jama’a domin fahimtar ainihin inda matsaloli ke akwai.

Kara karanta wannan

'Barci ba naka ba ne,' Malamin addini ya zaburar da Tinubu kan haɗakar ADC

Sanata Ireti ta soki Nyesom Wike
Sanata Kingibe ta soki aikin da Wike yake yi a Abuja Hoto: Sen. Ireti Kingibe
Source: Twitter

Karanta wasu labaran kan Wike

Dele Momodu ya fallasa Wike

A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar PDP, Dele Momodu ya caccaki salon siyasar ministan birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike.

Dele Momodu ya bayyana cewa Wike ya ba da cin hanci ga deliget a lokacin zaɓen fidda gwanin ɗan takarar shugaban ƙasa na PDP da aka gudanar a shekarar 2022.

Ya bayyana cewa Wike wanda ya ba da $30,000 ga kowane deliget, ya yi hakan ne domin ganin ya samu zama ɗan takarar shugaban ƙasa a ƙarƙashin inuwar jam'iyyar PDP.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng