Takara: Jigon ADC Ya Fara Tone Tone kan Yadda Wike Ya Raba 'Cin Hanci' a 2022
- Tsohon mai neman takarar shugaban kasa a PDP, Dele Momodu ya gargadi Bola Ahmed Tinubu a kan Nyesom Wike
- Momodu ya zargi Wike da amfani da kudi wajen neman tikitin takarar shugaban kasa a 2022 inda ya rika raba Daloli
- Ya shawarci shugaban kasa da kar ya aminta da Nyesom Wike, ko ya dogara da shi a babban zaben 2027 da ke zuwa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT Abuja – Fitaccen ɗan jarida kuma tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa, Dele Momodu, ya caccaki Ministan Abuja, Nyesom Wike kan yadda ya ke siyasarsa.
Guda daga cikin abin da ya ja hankalin Momodu shi ne yadda Wike ya gudanar da harkokin siyasa a zaɓen fitar da gwani na shugaban ƙasa da jam’iyyar PDP a 2022.

Kara karanta wannan
Jam'iyyar haɗaka ADC ta zaɓi ɗan takara tsakanin Atiku, Obi da Amaechi? An samu bayanai

Source: Facebook
A wata hira da aka yi da shi a Channels TV, Momodu ya zargi Wike da bayar da dala $30,000 ga kowanne wakilin jam'iyya lokacin.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya ce ya kashe makudan kudin ne da niyyar ya samu nasarar zama dan takarar shugaban ƙasa karkashin jam’iyyar PDP.
Wike: Yadda aka ja kunnen Dele kan takara
Jaridar The Guardian ta ruwaito cewa wani tsohon shugaban ƙasa ya aika sako ga Dele Momodu yana shawartarsa da kada ya tsaya takarar shugaban ƙasa saboda kudin da ake rabawa wakilai.
Momodu ya ce:
“Wani tsohon shugaban ƙasa ya turo da sako cewa kada in ɓata lokacina da kuɗina wajen takarar PDP, domin Wike ya ɗaga sikeli zuwa $30,000 ga kowanne wakili. Idan ka ninka hakan da wakilai 774, ka ga girman kuɗin."
Ya kara da zargin Wike da gudanar da siyasar kuɗi domin cimma mauradunsa ba tare da la'akari da tsarin dimokuraɗiyyar ba.
Ya jaddada cewa bai kamata Shugaba Bola Tinubu ya dogara da Wike a 2027 ba, yana mai bayyana Wike a matsayin mutum da bai dace da riƙe ikon gwamnati ba.

Kara karanta wannan
"Zai iya kifar da Tinubu," Momodu ya faɗi wanda ya dace ADC ta tsayar takara a 2027
A kalaman Dele Momodu:
“Kiran da nake yi ga Shugaba Tinubu shi ne, wannan mutumin ba irin wanda ya kamata ka ciyar gaba ba ne. Ba irin matashin da ya kamata ya karɓe dukiyar kasa ba ne.”

Source: Twitter
Dele ya bayyana damuwa kan Suke
Dele Momodu ya bayyana damuwa kan yadda Wike ke canjawa tun bayan hawansa kujerar Ministan Abuja a karkashin gwamnatin Bola Ahmed Tinubu.
Ya ce:
“Idan mutumin da ba a san shi ba sosai ba ya samu iko, yana fara canzawa sannu a hankali, har sai da ya zama yana bayar da mamaki."
A shekarar 2022, Momodu da Wike sun kasance daga cikin ‘yan takarar shugaban ƙasa a PDP, amma a ƙarshe tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, ne ya lashe zaɓen fidda gwanin jam’iyyar.
Dele Momodu ya yiwa Wike tonon silili
A baya, mun wallafa cewa fitaccen ɗan jarida kuma ɗan siyasa, Dele Momodu, ya soki Ministan Babban Birnin Tarayya, Nyesom Wike, kan zargin cin amana.
Dele Momodu ya yi zargin cewa Wike ya ci amanar abokan tafiyarsa na baya da suka taimaka masa kafin ya samu nasarar siyasa, har ya samu shiga gwamantin APC.
Momodu ya ce dangantakarsa da Wike ta taɓarɓare ne saboda yadda Wike ke amfani da mutane a lokacin da yake buƙatarsu, amma daga baya sai ya juya musu baya.
Asali: Legit.ng
