Likitoci Sun Tsunduma Yajin Aiki, Sun Fusata da Gwamnati Ta Ƙi Biyan Buƙatunsu

Likitoci Sun Tsunduma Yajin Aiki, Sun Fusata da Gwamnati Ta Ƙi Biyan Buƙatunsu

  • Likitoci a jihar Ondo sun tsunduma yajin aikin gargadi na kwanaki uku saboda sakaci da gwamnati ta yi wa fannin kiwon lafiya
  • Karkashin kungiyar NAGGDDPP, likitocin sun koka kan ƙarancin ma'aikata, rashin biyan albashi, alawus, da kuɗin karin matsayi
  • Sai dai gwamnatin Ondo ta ce ta fara biyan kuɗaɗen da ake bin su, kuma a shirye take ta ɗauki ƙarin likitoci idan akwai masu son aikin

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Ondo – Likitoci sun fara yajin aikin gargadi na kwanaki uku don nuna rashin jin dadinsu da abin da suka kira rikon sakainar kashi da gwamnatin ta yi wa fannin kiwon lafiya.

Ma'aikatan lafiyar a ƙarƙashin inuwar kungiyar likitocin gwamnati da na haƙora (NAGGDDP) reshen jihar Ondo ne suka tsunduma wannan yajin aiki.

Kara karanta wannan

Tashin hankali: An harbe sojan Najeriya har lahira a Kogi, an samu karin bayanai

Likitoci sun tsunduma yajin aiki saboda rashin samun alawus alawus da kudin karin matsayi
Wasu likitoci suna zazzaune yayin da daya daga cikin ke rike da karin shaidar rigakafin Covid19. Hoto: Getty Images A kula: An yi amfani da hoton don misali ne kawai.
Source: Getty Images

Likitoci sun shiga yajin aiki a Ondo

Yajin aikin, wanda ya fara ranar Litinin, ya shafi ayyukan lafiya a asibitocin gwamnati a faɗin jihar, kamar yadda rahoton Punch ya nuna.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwar haɗin gwiwa wacce shugaban kungiyar reshen Ongo, Dakta Richard Obe, da sakatarensa, Dakta Adekunle Owolabi, suka sanya wa hannu.

Kungiyar NAGGDDP ta bayyana cewa likitocin sun gaji da korafi kan tsananin ƙarancin ma'aikata, inda ta ce akwai asibitocin kananan hukumomi da ke da likita ɗaya kawai.

Har ila yau, kungiyar ta nuna fushinta kan rashin biyan albashi da alawus-alawus ga likitoci takwas da aka ɗauka aiki a watan Oktobar 2024.

Sanarwar ta ƙara da cewa:

“Sauran korafe-korafen sun haɗa da rashin biyan alawus-alawus na haɗarin aiki na Oktoba zuwa Disamba 2023 da Janairu 2024.
"Haka kuma ba a biya kuɗin karin matsayi ba daga Yuni zuwa Disambar 2024, ga kuma uwa uba ƙarancin albashi da rashin biyan alawus-alawus ga mambobi.”

Kara karanta wannan

Abu ya girma: Jiga jigai 3 sun nemi ruguza haɗaƙar Atiku, Obi da yan haɗaka a ADC

Likitoci sun yi wa gwamnati barazana

Ƙungiyar ta yi gargaɗi cewa idan har aka gaza biyan buƙatunsu, hakan na iya tilasta mambobinta tsunduma yajin aikin sai baba-ta-gani, wanda zai iya lalata tsarin kiwon lafiya na jihar.

Buƙatunsu sun haɗa da ɗaukar ƙarin likitoci nan take a dukkanin ƙananan hukumomi 18, biyan duk wani albashi da alawus-alawus da aka biyo, dawo da tsarin haraji na baya, da kuma biyan kuɗin karin matsayi.

Likitocin sun tunatar da cewa an bai wa gwamnatin Gwamna Lucky Orimisan Aiyedatiwa gargadin kwanakin aiki 14 a baya, amma gwamnatin jihar ta gaza ɗaukar mataki kan gargadin.

Gwamnatin Lucky Aiyedatiwa ta ce tuni ta fara biyan hakkokin likitocin kuma ta dauki karin ma'aikata
Gwamnan jihar Ondo, Lucky Aiyedatiwa ya ce a shirye yake ya dauki karin likitoci. Hoto: @LuckyAiyedatiwa
Source: Twitter

Martanin gwamnatin jihar Ondo

Da yake mayar da martani game da yajin aikin, mai ba gwamnan Ondo shawara na musaman kan harkokin lafiya, Farfesa Simidele Odimayo, ya ce gwamnatin jihar ta fara magance matsalolin da ake magana a kansu.

Farfesa Simidele ya ce:

“Mun fara biyan kuɗaɗen da aka biyo saboda gwamna ya ba da umarni a biya kuɗaɗen, kuma za mu magance sauran matsalolin da suka gabatar.”

Kara karanta wannan

Tinubu ya rufe bakin ƴan adawa, ya faɗi abin da ake yi da kudin tallafin man fetur

Game da batun ƙarancin ma'aikata, Odimayo ya lura cewa gwamnati ta fitar da sanarwar daukar aiki kuma ta ɗauki ma'aikatan da suka nema.

“Idan suna da mutanen da suke so mu ɗauka aiki, su zo da su. Gwamnati ba za ta iya ƙirƙiro likitoci ba, amma a shirye muke mu ɗauke su aiki.”

- Farfesa Simidele Odimayo.

Yajin aikin likitoci ya jawo asara rai

A wani labarin, mun ruwaito cewa, wata mata mai juna biyu ta mutu a asibitin kwararru na jihar Nasarawa, wanda mallakin gwamnatin jihar ne da ke Lafia.

An gano cewa matar ta mutu ne sakamakon rashin likitocin da za su duba ta, biyo bayan yajin aikin gargaɗi na kwanaki biyar da suka shiga.

An kuma bayyana cewa an yi gaggawar kwashe marasa lafiya masu buƙatar kulawa ta musamman zuwa asibitocin kudi don ci gaba da samun kulawar likitoci.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com