Mutane na kwashe yan uwansu daga asibiti yayinda Likitoci suka tafi yajin aiki

Mutane na kwashe yan uwansu daga asibiti yayinda Likitoci suka tafi yajin aiki

  • Yau Kwana na biyu da Likitoci a Najeriya suka sake shiga yajin aiki
  • Likitocin sun zargi gwamnatin tarayya da rashin cika alkawuranta
  • Marasa lafiya na jin jiki a asibitoci sakamakon wannan yaji

Lagos - Yan uwa na kwashe marasa lafiyansu daga asibitocin gwamnati yayinda yajin aikin kungiyar Likitoci masu neman kwarewa (NARD) ya shiga kwana ta biyu.

Jaridar Sun ta bayyana cewa a asibitocin da ta ziyarta, Likitoci sun dauke kafa gaba daya kuma an bar marasa lafiya babu mai duba su.

Hakazalika an fadawa wadanda suka kawo sabbin marasa lafiyansu su tafi asibitoci masu zaman kansu.

Manyan Likitocin dake asibitocin sun yi karanci da yawa kuma ba zasu iya maye gurbin kananan likitocin da ke yaji ba.

Wasu marasa lafiya sun bayyanawa TheSun cewa suna kira ga gwamnati ta gaggauta kawo karshen wannan yajin aiki da Likitocin ke yi.

Mutane na kwashe yan uwansu daga asibiti
Mutane na kwashe yan uwansu daga asibiti yayinda Likitoci suka tafi yajin aiki Hoto: www.sunnewsonline.com
Asali: UGC

Kara karanta wannan

Yajin aiki: Ku zo mu zauna muyi magana: Ministan Lafiya ya bukaci Likitoci

A asibitin FMC Abeokuta, jihar Ogun, malaman jinya sun fara sallaman marasa lafiyan dake jinya.

Wata Malamar jinya ta bayyana marasa lafiyan su biya kudin da asibiti ke binsu kuma su tafi gida ko su nemi wani asibitin.

Shugaban kungiyar Likitocin NARD na asibitin, Dr Busuyi Adebiyi, yace ya zama wajibi suyi biyayya ga uwar kungiya.

Yace:

"Har sai mun samu wani umurni na daban, zamu cigaba da yajin aiki. Wannan yajin aikin na kowa da kowa ne."

Hakazalika, Likitoci a asibitin koyarwan jami'ar Ilori (UITH) sun bazama yajin aiki yayinda suke kira ga uwar kungiya ta wajabtawa gwamnati biyan bukatunsu.

Likitoci a Najeriya sun tsunduma yajin aiki ranar Litinin

Kungiyar likitoci a kasar nan (NARD) ta umurci mambobinta dasu tsunduma yajin aikin sai baba ta gani ranar Litinin, 2 ga watan Agusta.

Da yake yiwa yan jarida bayani a karshen taron, Shugaban kungiyar, Dr Okhuaihesuyi Uyilawa ya bayyana cewa an umurci mambobin dasu fara yajin aikin sai baba ta gani.

Ya bayyana yadda gwamnatin tarayya ta gaza cimma bukatun likitoci, wannan yana daga cikin abinda yasa suka yanke hukuncin shiga yajin aikin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng