Yan Sanda Sun Fara Kame bayan Jina Jina Tsakanin Masoyan Sanusi II da Aminu Ado

Yan Sanda Sun Fara Kame bayan Jina Jina Tsakanin Masoyan Sanusi II da Aminu Ado

  • Rundunar yan sandan Kano ta tabbatar da cewa an fara kama wasu daga cikin wadanda suka tayar da rikici a Kofar Kudu a ranar Lahadi
  • Rahotanni sun ce an yi arangama a tsakanin magoya bayan Muhammadu Sanusi II da Sarkin Kano na 15, Aminu Ado Bayero
  • Lamarin ya jawo raunuka tare da lalata kofar shiga fadar kafin jami'an tsaro su kawo dauki tare da shawo kan rikicin cikin gaggawa

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kano – Rundunar ƴan sandan jihar Kano ta tabbatar da kama mutane huɗu da ake zargi da hannu a rikicin da ya faru a fadar Sarkin Kano da ke unguwar Kofar Kudu.

Mai magana da yawun rundunar, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya tabbatar da kama waɗanda ake zargin a wata sanarwa da ya fitar a ranar Talata.

Kara karanta wannan

Rikicin sarauta: Gwamnatin Kano ta fito ta fayyace abin da ya faru a Fadar Sanusi II

Rikicin masarautar Kano
Yan sanda sun fara kame kan rikicin Fadar Kudu Hoto: Masarautar Kano/Abdullahi Haruna Kiyawa/Sanusi II Dynasty
Source: Facebook

Punch ta ruwaito cewa hatsaniyar da ta faru tsakanin magoya bayan Sarkin Kano na 16, Muhammadu Sanusi II, da na Sarkin Kano na 15, Aminu Ado Bayero, ta tayar da hankali.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ƴan sanda sun fara bincikin rikicin Kano

Rundunar ƴan sandan ta tabbatar da cewa ana gudanar da bincike domin gano hakikanin musabbabin rikicin da ya faru tsakanin magoya bayan manya a masarautar Kano.

SP Abdullahi Haruna Kiyawa ya ce:

“Eh, rundunar ta kama mutane huɗu da ake zargi da hannu a lamarin, kuma suna tsare a hannun ƴan sanda yayin da ake cigaba da bincike.”

Ya bayyana cewa kwamishinan ƴan sanda na jihar Kano, Ibrahim Bakori, ya kafa wani kwamitin bincike don nazarin rikicin da ya auku tare da ɗaukar mataki

SP Abdullahi Haruna Kiyawa bai bayyana sunayen waɗanda aka kama ba, amma ya tabbatar da cewa suna hannun ƴan sanda.

Yan sanda sun kai dauki Kano

Kara karanta wannan

Sanusi II ya yi magana kan rigimar da ta faru a fadarsa da Aminu Ado ya zo wucewa

Rikicin ya samo asali ne bayan da wasu matasa da ake zargin magoya bayan Muhammadu Sanusi ne suka tare hanyar da Aminu Ado Bayero ke wucewa.

Sarkin Kano na 15, Aminu Ado Bayero na shirin wucewa a lokacin da yake dawowa daga fadar Mandawari ta'aziyyar marigayi Aminu Dantata zuwa fadar Nassarawa.

Rundunar yan sandan Kano
Yan sanda sun kama mutum 4 a Kano Hoto: Abdullahi Haruna Kiyawa
Source: Facebook

Shaidun gani da ido sun bayyana cewa wasu masu gadin fada sun ji rauni, an lalata motoci mallakar ƴan sanda da kuma rusa ƙofar shiga fadar.

Sai dai hanzarin da ƴan sanda suka yi wajen kawo ɗauki da tarwatsa matasan da hayaki mai sa hawaye ya hana rikicin rikidewa zuwa kashe-kashe.

Gwamnatin Kano ta magantu kan rikicin masarauta

A baya, kun ji cewa rikicin siyasa da ke ci gaba da ƙamari a masarautar Kano ya sake bayyana a fili, yayin da aka kai hari fadar mai martaba Sarkin Kano na 16, Muhammadu Sanusi II.

Wani rukuni na mutane da ba a tantance ba sun farmaki fadar, lamarin da ya jawo lalata ɗaya daga cikin ƙofofin shiga fadar da fasa motocin ‘yan sanda.

Gwamnatin Kano ta nuna damuwa game da lamarin da ya faru a fadar Sarkin Kano, tare da bayyana cewa tana bin diddigin al’amuran da ke ƙara tayar da hankali.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng