Sanusi II Ya Yi Magana kan Rigimar da Ta Faru a Fadarsa da Aminu Ado Ya Zo Wucewa

Sanusi II Ya Yi Magana kan Rigimar da Ta Faru a Fadarsa da Aminu Ado Ya Zo Wucewa

  • Sarkin Kano na 16, Muhammadu Sanusi II ya zargi magoya bayan Aminu Ado Bayero da kai hari fadarsa tare da karya ƙofa
  • A wata sanarwa da masarautar Kano ta fitar, ta ce Sanusi II ba ya cikin fadar a lokacin da lamarin ya faru ranar Lahadi da ta gabata
  • Rahotanni sun nuna cewa Aminu Ado Bayero da tawagarsa sun bi ta titin gaban fadar Kofar Kudu, lamarin da ya jawo tashin rikici tsakanin magoya baya

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Kano - Rikicin sarautar Kano tsakanin Sarki na 16, Muhammadu Sanusi II da na 15, Aminu Ado Bayero ya dauki sabon salo a karshen makon da ya gabata.

Sarkin Kano na 16, Mai Martaba Muhammadu Sanusi II, ya zargi magoya bayan Alhaji Aminu Ado Bayero, da kai hari a fadarsa tare da ɓalle daya daga cikin ƙofofi.

Kara karanta wannan

Rikicin sarauta: Gwamnatin Kano ta fito ta fayyace abin da ya faru a Fadar Sanusi II

Sarkin Kano na 16, Muhammadu Sanusi II.
Sanusi II ya zargi magoya bayan Aminu Ado da kai hari fadarsa Hoto: Masarautar Kano
Source: Twitter

Leadership ta rawaito cewa harin ya faru ne a fadar da ke Kofar Kudu, inda Muhammadu Sanusi II ke zaune tun bayan dawo da shi kan sarauta.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An ce rikicin ya auku ne a ranar Lahadi lokacin da Aminu Bayero da dumbin masu rakiyarsa suka dawo daga gidan Mandawari, suka wuce ta kusa da fadar.

Abin da ya faru a fadar Sarkin Kano

A cikin wata sanarwa da sashen yaɗa labarai ta masarautar Kano ya fitar, wacce Sadam Yakasai ya sa wa hannu, an ce Sarkin Sanusi ba ya nan lokacin da lamarin ya faru.

Mai magana da yawun masarautar Kano, Sadam Yakasai ya ce:

“Sun karya ƙofar fadar, sannan suka farmaki masu gadinta, har wasu sun jikkata. Sun lalata motoci na ‘yan sanda da ke cikin fadar.
"Aminu Ado ya biyo titin gaban fadar Sarki da gangan, maimakon ya bi hanyar Koki zuwa Nassarawa. ‘Yan barandansa suka yanke shawarar kai hari Gidan Rumfa,” in ji Yakasai.

Kara karanta wannan

Kano: Ƴan sanda sun fara binciken rikicin magoya bayan Sanusi II da Aminu Ado Bayero

Masarautar Kano ta zargi Aminu Ado Bayero

Yakasai ya ce wannan ba shi ne karon farko da Aminu ke wucewa da gangan ta kofar fadar ba, yana mai cewa yana yi ne domin tsoratar da jama’ar unguwar.

Ya kara da cewa tun bayan tsige Aminu Ado Bayero daga kan kujerar sarauta da gwamnatin jihar Kano ta yi, ya koma zaman fadar Nassarawa ba tare da bin ka’ida ba.

"Bai ƙalubalanci tsigewar da aka masa a kotu ba, amma ya jingina da waɗanda suka kai ƙara. Gwamna ya yi haƙuri duk da matsalolin da Sarkin da aka tsige da magoya bayansa ke haifarwa a kusa da gidan gwamnati."
Aminu Ado Bayero da Muhammadu Sanusi II.
Masarautar Kano ta zargi Aminu Ado da tayar da rikici da gangan Hoto: @masarautarkano
Source: Twitter

Aminu ya rasa goyon bayan hakiman Kano

Yakasai ya jaddada cewa babu wani babban jigo daga cikin manyan masu ruwa da tsaki a masarautar da ke goyon bayan Aminu Ado Bayero, inda 37 daga cikin Hakimai 38 suka riga suka yi mubaya’a ga Sanusi II.

“Sai ɗaya kawai daga cikin ‘yan uwan Aminu Ado Bayero shida da bai yi mubaya’a ba. Har ma ɗan uwan tsohon gwamnan Kano, Abdullahi Ganduje, aka naɗa Magajin Garin Ganduje ta Sanusi II, ba Aminu ba.”

Kara karanta wannan

Rashin biyayya: An umarci masoyan Aminu Ado su fice daga gidan Sarki Sanusi II

“Wannan shi ne karon farko da Aminu Ado Bayero ya tayar da rikici kai tsaye a Gidan Rumfa, duk da yana ci gaba da zama fadar Nassarawa da ke makwabtaka da gidan gwamnati,” in ji Yakasai.

An kori magoya bayan Aminu daga fada

A wani rahoton, kun ji cewa rikicin sarautar Kano na ƙara ƙamari a ƴan kwanakin nan da aka umarci masoyan Aminu su bar fadar Sanusi II.

Rahotanni sin bayyana cewa wasu daga cikin jami'an fadar Sarki da ke Kofar Kudi da ake zargin suna goyon bayan Aminu Ado da aka tsige sun sha ihu.

Rikicin masarautar Kano na cigaba da jefa masu rike da mukaman gargajiya cikin rudani kan wanda za su mara wa baya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262