Rashin Biyayya: An Umarci Masoyan Aminu Ado Su Fice daga Gidan Sarki Sanusi II
- Masu biyayya ga Aminu Ado Bayero sun fuskanci korafi daga fada, saboda rashin goyon bayan Sarki Muhammadu Sanusi II
- Wasu jami’an fada da iyalansu sun sha ruwan ihu yayin da aka zargi ’yan daba da balle rufin gidajensu domin tilasta musu ficewa
- Rikicin masarautar Kano na cigaba da jefa masu rike da mukaman gargajiya cikin rudani kan wanda za su mara wa baya
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Kano - Wani sabon salon rigima ya kunno kai a rikicin masarautar Kano bayan samun rikici a tsakanin masoyan manyan sarakuna biyu a jihar.
Matsalar ta fara ne yayin da aka kori masu biyayya ga Sarkin Kano na 15, Aminu Ado Bayero daga babban fadar masarauta.

Source: Twitter
Wasu daga cikin iyalai da suka zauna a fadar shekaru da dama sun shaida cewa an kore su ne saboda iyayensu ba sa goyon bayan Sarki Sanusi, cewar Premium Times.

Kara karanta wannan
Aminu Ado Bayero ya yi magana, ya faɗi abin da magoya bayansa suka yi a Fadar Sanusi II
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Farkon fara rigimar masarauta a jihar Kano
Rikicin ya fara ne tun watan Mayun 2024, lokacin da Gwamna Abba Yusuf ya tube Ado Bayero da wasu sarakuna hudu, ya kuma dawo da Sarki Sanusi II.
Tun daga lokacin, Ado Bayero da Sarki Sanusi II ke gudanar da al’amuran sarauta daga fadoji biyu daban-daban a cikin jihar Kano.
Ado Bayero na ci gaba da kalubalantar tube shi daga karamin fada, yayin da Sanusi ke zaune a babban fadar da aka bayar da umarnin korar wasu.
Amma yanzu dai kowa ya zuba ido domin warware matsalar gaba daya yayin da ake jiran hukuncin Kotun Koli a kowane lokaci daga yanzu.

Source: Facebook
Manyan masoyan Aminu Ado da abin ya shafa
Wadanda abin ya shafa sun hada da Galadiman Sallama, Sani Kwano, Dan-Habu Maji-Dadi da wasu masu mukamai a masarautar.
Wasu majiyoyi sun ce ’yan daba sun balle rufin wasu gidaje da daddare domin fitar da mutanen da aka umurta barin fadar.
Wannan lamari ya haifar da tarzoma da dare yayin da iyalan da abin ya shafa suka bijire wa umarnin ficewar dole daga gidajensu.
Rudani da ke damun wasu masu mukamin sarauta
Rikicin masarautar na cigaba da jefa hakimai, masu mukamai da sauran dattawan gargajiya cikin rudani kan wanda ya kamata su mara wa baya.
Yanzu dai ana ci gaba da jiran yadda za a warware rikicin da ya dabaibaye masarautar Kano tun sama da shekara guda, cewar Punch.
Rundunar yan sanda ta tabbatar da fara binciken abin da ya faru domin gano bakin zaren da hukunta masu hannu a ciki.
Rikici ya barke tsakanin masoyan Sanusi, Bayero
Mun ba ku labarin cewa wasu da ake zargin ƴan daba ne sun farmaki fadar Sarkin Kano ta Ƙofar Kudu, inda Muhammadu Sanusi II ke zama.
An ce lamarin ya faru ne a ranar Lahadi da misalin karfe 1:00 na rana lokacin da Sarki na 15, Aminu Ado Bayero ya wuce ta unguwar Ƙofar Kudu.
Rundunar ƴan sanda ta tabbatar da aukuwar lamarin, wanda aka ce ƴan daban sun jefa duwatsu, sun lalata babura da wasu kayayyaki.
Asali: Legit.ng
