Gwamnatin Sokoto Ta Kafa Sharadin Sulhu da Bello Turji

Gwamnatin Sokoto Ta Kafa Sharadin Sulhu da Bello Turji

  • Gwamnatin jihar Sokoto ta yi martani kan kiran da hatsabibin ɗan bindiga, Bello Turji, ya yi na yin sulhu
  • Mai ba Gwamna Ahmed Aliyu shawara kan harkokin tsaro, ya buƙaci ɗan bindigan da ya sako mutanen da ke tsare a hannunsa
  • Kanal Ahmed Usman (mai ritaya) ya nuna cewa suna son Bello Turji ya nuna cewa da gaske yana da burin ganin an samu zaman lafiya

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Sokoto - Mai ba gwamnan jihar Sokoto shawara kan harkokin tsaro, Kanal Ahmed Usman (mai ritaya), ya yi kira ga jagoran ƴan bindiga, Bello Turji.

Kanal Ahmed Usman ya buƙaci Bello Turji da ya saki dukkan mutanen da ya sace ba tare da wani sharaɗi ba, da kuma dakatar da hare-hare kan al’ummomin karkara.

Gwamnatin Sokoto ta yi magana kan Bello Turji
Gwamnatin Sokoto ta bukaci Bello Turji ya sako mutanen da ya sace Hoto: @Ahmedaliyuskt
Source: Twitter

Jaridar The Punch ta ce kiran da Kanal Ahmed Usman ya yi ya biyo bayan wani saƙon sautin muryar Bello Turji da ya yadu a kafafen sada zumunta.

Kara karanta wannan

Kisan Danbokolo: Abin da al'umma suka shirya saboda tsoron abin da ka iya biyo baya

A cikin saƙon, Bello Turji ya nuna niyyarsa ta rungumar zaman lafiya tare da kiran sauran shugabannin ƴan bindiga su shiga tattaunawa.

Me gwamnatin Sokoto ta cewa Bello Turji?

Kanal Ahmed Usman ya yaba da wannan furuci a matsayin wata dama mai muhimmanci wajen dawo da zaman lafiya a yankin.

Ya jaddada cewa gwamnatin jihar Sokoto za ta auna irin waɗannan kalamai ne ta fuskar ayyuka masu gamsarwa, ba da magana kawai ba.

"Idan har Bello Turji yana da gaskiyar burin zaman lafiya, dole ne ya tabbatar da hakan ta hanyar dakatar da duk wani nau’i na tashin hankali da sakin fararen hula da yake riƙe da su."

- Kanal Ahmed Usman

Tsohon jami’in sojan ya ƙara da cewa, kare rayuka da jin daɗin mazauna karkara na daga cikin manyan abubuwan da Gwamna Ahmed Aliyu ke baiwa muhimmanci.

Ya bayyana cewa ba za a iya gudanar da tattaunawa mai ma’ana ba yayin da hare-hare da sace-sace ke ci gaba da faruwa a cikin al’umma ba, rahoton jaridar Daily Trust ya tabbatar.

Kara karanta wannan

Tashin hankali: Fada ya barke tsakanin wasu 'yan gida 1 a Filato, an yi kisan kai

“Ba za a samu tattaunawa ta gaskiya ba yayin da mutane ke rayuwa cikin tsoro da ƙunci. Zaman lafiya na buƙatar matakai na ainihi da ke gina amana."

- Kanal Ahmed Usman

Gwamnatin Sokoto na goyon bayan zaman lafiya

Kanal Ahmed Usman ya tabbatar da cewa gwamnati a shirye take ta tallafa wa kowanne tsari na zaman lafiya da ke da niyyar kawo ƙarshen rashin tsaro, amma ya gargaɗi cewa ba za a lamunci aikata laifi da sunan sulhu ba.

Gwamnatin Sokoto ta yi kira ga Bello Turji
Gwamnatin Sokoto ta aika da sako ga Bello Turji kan sulhu Hoto: Legit.ng
Source: Original

Ya kuma buƙaci shugabannin al’umma, malamai, ƙungiyoyin fararen hula da sauran masu ruwa da tsaki da su haɗa kai wajen tabbatar da zaman lafiya mai ɗorewa.

A ƙarshe, ya buƙaci Turji da mabiyansa da su amfana da wannan dama ta hanyar bin tafarkin sulhu na gaskiya da ƙaurace wa tashin hankali.

“Wannan dama ce ta kawo ƙarshen wahala. A fara da dawo da duk mutanen da aka sace cikin ƙoshin lafiya."

- Kanal Ahmed Usman

Yaran Bello Turji sun yi ɓarna a Sokoto

A wani labarin kuma, kun ji cewa yaran hatsabibin ɗan bindiga, Bello Turji, sun kai hare-hare a wasu ƙauyukan Sokoto.

Kara karanta wannan

An bayyana sunan mutum 1 tilo da ya kashe hatsabibin 'dan bindiga, Yellow Danbokolo

Ƴan bindigan sun kai hare-haren na ta'addanci ne a ƙauyukan Satiru, Makwaruwa da Gidan Gyara.

Kai hare-haren dai na zuwa ne a daidai lokacin da jami'an tsaro suka ƙara ƙaimi wajen farautar Bello Turji wand ake nema ruwa a jallo.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng