Rigima a Kano: FIRS Ta Garkame Ofishin KEDCO kan Basussukan Biliyoyin Naira
- Hukumar tattara haraji ta ƙasa (FIRS), reshen Kano, ta rufe hedikwata da ofisoshin kamfanin rarraba lantarki na KEDCO a jihar
- Lamarin ya biyo bayan basussukan da aka ce kamfanin KEDCO ya ƙi biyan FIRSC na tsawon kusan shekaru shida da suka gabata
- A matsayin martani, KEDCO ya datse wutar lantarki daga dukkan ofisoshin FIRS a jihar Kano, lamarin da ya kara dagula al’amura
Jihar Kano – An shiga wani halin saɓata juyata Kano bayan saɓani ya shiga tsakanin hukumar gwamnati da kamfani mai zaman kansa.
Hukumar tattara haraji ta kasa, reshen jihar Kano (FIRS) ta rufe hedkwata da ofisoshin kamfanin rarraba hasken wutar lantarki a jihar (KEDCO).

Source: UGC
A sakon da hadimin tsohon shugaban APC na kasa, Salihu Tanko Yakasai ya sanya a shafinsa na X, lamarin bai yiwa kamfanin KEDCO dadi ba.
Dalilin rufe ofisoshin KEDCO a Kano
Solacebase ta wallafa cewa hukumar ta dauki wannan matakin ne kan zargin cewa KEDCO na bin FIRS harajin miliyoyin Naira.
Wani ma’aikaci a KEDCO ya bayyana wa jaridar cewa:
“An kulle ofisoshinmu n tsawon kwanaki tara ba wani ma’aikaci da ya iya shiga. Har ma ma’aikatan tsaronmu sun tsaya a waje."
Motocin sintiri sun makale a cikin ofishin — ba za mu iya fitar da su ba. Na kasance a wurin da FIRS suka iso da takardar kotu kafin su kulle ofishin.”
Duk da tsawon kwanakin da aka shafe, ba a samu wani bayani bangaren KEDCO ba a kan matakan da suka shirya dauka bayan zarginsu da taurin bashi na tsawon shekaru.
Martanin KEDCO ga hukumar FIRS
A wani martani, KEDCO ya yanke wutar lantarki daga dukkanin ofisoshin FIRS a jihar Kano, abin da ya kara tsananta hargitsi tsakanin hukumar da kamfanin rarraba wuta.

Source: Original
Haka kuma, an tuntubi wani jami’i a FIRS fannin bashin haraji a ofishinsu da ke titin Gwarzo, amma bai bada bayanin dalilin rufe ofishin ba.
Sai dai wani ma’aikaci daga cikin FIRS ya bayyana cewa KEDCO ta yi taurin bashi har na shekaru shida, wanda ya samo asali ne daga wasu gwamnatoci da suka gabata.
Ko da yake, Legit ta yi ƙoƙarin samun ƙarin bayani daga daga bakin jami'in yada labaran na kamfanin KEDCO a Kano, Malam Sani Bala, bai amsa wayarsa ba.
Zuwa yanzu dai, ana ci gaba da sa ido domin ganin yadda za ta kaya a tsakanin hukumomin biyu, ko za a kawo karshensa a kwana kusa, ko kuma kowa ya ja layi.
KEDCO: Rashin wuta ya fusata mutanen Kano
A wani labarin, mun wallafa cewa al’ummar da ke zaune a unguwar Dakata, a karamar hukumar Nassarawa a jihar Kano, sun shafe kwanaki 70 ba tare da samun wutar lantarki ba.
Mazauna yankin ma zargin kamfanin KEDCO, wanda ke da alhakin rarraba wutar lantarki a Kano da kewaye, bai kai wuta yankin ba tsawon kusan watanni biyu kuma babu wani bayani.
Sakamakon wannan matsala, ’yan kasuwar Dakata sun gudanar da gangamin sallar Nafila tare da yin addu’o’in Alkunuti, inda suka roƙi Allah ya hukunta duk wanda ke da hannu a lamarin.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

