'Yan Bindiga Sun kai Hari Gidan Tsohon Minista a Filato, Sun Yi Kisa

'Yan Bindiga Sun kai Hari Gidan Tsohon Minista a Filato, Sun Yi Kisa

  • Wasu ’yan bindiga sun kai hari gidan tsohon Ministan Wasanni, Damishi Sango, a ƙaramar hukumar Riyom a jihar Filato
  • Rahotannin sun nuna cewa maharan sun harbe wata ’yar uwarsa mace har lahira tare da jikkata ɗan sanda a gidan
  • Bayan fara bincike, an gano cewa maharan sun kuma tafi da bindigar ɗan sandan da ke bakin aiki a gidan tsohon ministan

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Filato – An samu tashin hankali a daren Talata a lokacin da wasu ’yan bindiga suka kai hari gidan tsohon ministan wasanni, Damishi Sango a Filato.

Rahotanni sun nuna cewa 'yan bindigar sun kai harin ne a gidan ministan da ke kauyen Dalwal, a ƙaramar hukumar Riyom ta jihar Filato.

Tsohon ministan wasanni da aka kai hari gidan shi.
Tsohon ministan wasanni da aka kai hari gidan shi. Hoto: Zagazola Makama|Legit
Source: Facebook

Legit ta tattaro bayanai kan lamarin ne a cikin wani sakon da Mai sharhi kan tsaro, Zagazola Makama ya wallafa a X.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun nuna rashin imani, su buɗe wuta ana tsakiyar Sallah a jihar Sakkwato

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Harin ya yi sanadiyyar mutuwar wata ’yar uwarsa mace da kuma raunata wani jami’in ‘yan sanda mai suna Walba Go Tom da ke gadin gidan.

Rahotanni sun tabbatar da cewa ’yan bindigar sun yi awon gaba da bindigar jami’in bayan sun harbe shi.

An kai hari gidan tsohon minista a Filato

Rahoton ya nuna cewa harin ya auku ne da misalin ƙarfe 10:46 na dare lokacin da maharan suka farmaki gidan tsohon ministan tare da bude wuta.

A yayin harin, jami’in ‘yan sanda daga sashen SPU da ke Makurdi, wanda aka tura domin tsaron lafiyar Damishi Sango, ya samu harbin bindiga a jikinsa.

Bayan haka, wata mace daga cikin dangin tsohon ministan ta samu rauni sakamakon harbin bindiga, inda daga bisani ta rasu a asibitin kwararru na jihar Filato da ke Jos.

Jami’in ‘yan sandan na kwance a asibiti

Bayan samun raunin, jami’in ‘yan sandan da lamarin ya shafa ya garzaya asibiti domin samun kulawar gaggawa, kuma rahotanni sun tabbatar da cewa yana samun sauƙi a halin yanzu.

Kara karanta wannan

Ana tsaka da korar 'yan ta'adda, sun jikkata jami'in dan sanda a Katsina

Majiya daga yankin ta ce ’yan bindigar sun tsere kafin jami’an tsaro ko mazauna yankin su iya kawo ɗauki.

An kuma bayyana cewa maharan sun gudu da bindigar jami’in ‘yan sandan da suka raunata yayin harin.

Gwamnan jihar Filato bai yi magana kan hari da ka kai ba.
Gwamnan jihar Filato bai yi magana kan hari da aka kai ba. Hoto: Plateau State Government
Source: Twitter

Halin da ake ciki bayan kai harin

Yanzu haka, jami’an tsaro da mazauna yankin na cigaba da bincike tare da neman bayanai domin gano wadanda suka aikata wannan danyen aiki.

Hukumomi ba su fitar da cikakken bayani kan harin ba tukuna, sai dai ana sa ran za a ƙara tsaurara matakan tsaro a yankin domin hana faruwar irin hakan a gaba.

An kama 'yan ta'adda 14 a jihar Benue

A wani rahoton, kun ji cewa jami'an tsaro sun kama mutum 14 da ake zargi sun shirya kai hari jihar Benue.

Rahotanni sun nuna cewa an kama mutanen ne bayan samun bayanan sirri kan makircin da suka kulla.

Bincike farko da aka gudanar ya nuna cewa mutanen da aka kama na da alaka da wani rikakken dan bindiga da ya addabi jihar.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng