Garba Shehu Ya Fadi Halin da Buhari Ke Ciki Yayin da Yake Jinya a Birtaniya

Garba Shehu Ya Fadi Halin da Buhari Ke Ciki Yayin da Yake Jinya a Birtaniya

  • Mallam Garba Shehu ya tabbatar da cewa tsohon Shugaba Muhammadu Buhari na samun sauƙi bayan rashin lafiya da ya tafi duba lafiyarsa
  • Garba Shehu ya ce Buhari ya kamu da rashin lafiya yayin duba lafiya na shekara-shekara da ya saba yi a ƙasar Birtaniya tun ba yau ba
  • A baya, Buhari ya shafe sama da kwana 100 a London yana jinya, musamman a 2017, hakan ya sa mutane suka dage da yi masa addu'o'i

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

London, UK - Mai magana da yawun tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari, Malam Garba Shehu, ya bayyana cewa tsohon shugaban na samun sauƙi a jinyar da yake yi a Birtaniya.

Garba Shehu ya ce Buhari ya tafi Birtaniya domin duba lafiya na shekara-shekara, sai ya kamu da rashin lafiya a lokacin.

Kara karanta wannan

David Mark: Takaitaccen tarihin jagoran hadakar ADC da ya yi gwamna tun a 1984

Buhari na cigaba da samun sauki a London
Garba Shehu ya yi magana kan rashin lafiyar Buhari. Hoto: Muhammadu Buhari.
Source: Twitter

Garba Shehu ya bayyana haka ne a ranar Laraba, yayin da yake amsa tambaya kan halin da Buhari ke ciki dangane da rahotannin rashin lafiya, cewar Daily Trust.

Faman da Buhari ya yi da lafiyarsa a mulki

A lokacin da yake mulki daga 2015 zuwa 2023, Buhari ya yi fama da jinya da dama inda ya fi yawan zuwa London domin duba lafiya.

A shekarar 2017, ya shafe fiye da kwana 100 a London yana jinya kan wata cuta da ba a bayyana ba wanda hakan ya jawo maganganu daga dukan fadin kasa.

Daga baya sai aka rage tafiye-tafiyensa sakamakon bullar cutar Korona da ta hana zirga-zirga a duniya baki ɗaya.

An fadi yadda Buhari ke samun sauki

Garba Shehu ya ce kowace shekara Buhari na zuwa London domin duba lafiyarsa amma jikin da sauki inda ya gode da addu'o'in da ake yi masa.

Kara karanta wannan

An gano yadda Buhari ya sha fama da matsananciyar jinya a Landan

Ya ce:

"Gaskiya ne cewa tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari ba shi da lafiya. Amma yana samun sauƙi a jinyar da yake yi yanzu.
"Kamar yadda ya saba, ya sanar da tafiyarsa domin duba lafiya kafin a samu wannan sauyin yanayi."
Garba Shehu ya roki addu'a ga Buhari
An bayyana halin da Buhari ke ciki yayin jinya a London. Hoto: Muhammadu Buhari.
Source: Facebook

Buhari: Rokon Garba Shehu ga 'yan Najeriya

Garba Shehu ya roki jama’a da su yi masa addu’ar samun cikakken sauƙi da lafiya mai ɗorewa a yayin da yake jinya.

Gwamnatin Buhari a wancan lokaci ta sha suka daga ‘yan Najeriya kan rashin bayyanawa gaskiya game da lafiyarsa, cewar Premium Times.

Sai dai Garba Shehu ya jaddada cewa a yanzu lafiyar Buhari na kara ingantuwa, kuma gwamnati da dangi na kula da shi.

Tsohon shugaban ya bar ofis a 2023 bayan kammala wa’adinsa na biyu da ya yi a matsayin shugaban Najeriya.

Garba Shehu ya kare Buhari kan cire tallafi

Kun ji cewa hadimin tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya bayyana gaskiya kan zargin da ake yi wa gwamnatin da ta shude.

Kara karanta wannan

Cin hanci: Garba Shehu ya bayyana sirrin mulkin Muhammadu Buhari

Malam Garba Shehu ya ce Buhari bai yi wani shiri na kawo cikas ga gwamnatin Bola Tinubu ba musamman kan cire tallafin mai.

Ya ce dukkansu 'yan jam'iyyar APC ne, don haka babu yadda Buhari zai hana Tinubu nasara ko ya jefa shi cikin matsala.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.