An Gano Yadda Buhari Ya Sha Fama da Matsananciyar Jinya a Landan

An Gano Yadda Buhari Ya Sha Fama da Matsananciyar Jinya a Landan

  • An kwantar da tsohon Shugaba Muhammadu Buhari a ICU a Birtaniya, amma an sallame shi a makon da ya gabata bayan samun sauƙi
  • Rahotanni sun bayyana cewa Buhari da Mamman Daura duka suna jinya a Landon, kuma ana sa ran tsohon shugaban zai dawo Najeriya
  • Duk da dai ba a sanar da rana ba, majiyoyi daga cikin makusantansa sun ce da zarar ya karasa murmurewa zai dawo gida

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Kasar England – Tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari yana fama da rashin lafiya ne a wani asibiti da ke ƙasar Birtaniya.

Rashi lafiyar ta yi kamarin da har an kwantar da shi a dakin kula da marasa lafiya mai tsanani wato ICU, kamar yadda rahotanni suka tabbatar.

Kara karanta wannan

David Mark: Takaitaccen tarihin jagoran hadakar ADC da ya yi gwamna tun a 1984

Tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari
Tsohon shugaban kasa yana jinya a Landan Hoto: Muhammadu Buhari
Source: Twitter

Jaridar The Cable ta wallafa cewa wani kusa da Buhari ya ce shugaban gamu da rashin lafiyar ne a lokacin da yake duba lafiya a Landon.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Muhammadu Buhari zai dawo gida

Majiyoyi daga kusa da iyalan tsohon shugaban sun tabbatar wa Empowered Newswire da cewa ana sa ran Buhari zai dawo Najeriya da zarar ya murmure gaba ɗaya.

Zuwa yanzu, rahotanni sun ce an sallame shi daga ICU a makon da ya gabata, kuma yana murmurewa a Landan, ana samun sauki.

An kuma gano cewa Mamman Daura, ɗan uwan Buhari kuma amintaccensa, shi ma yana samun sauƙi daga jinyar da ya sha fama da ita a Birtaniya.

Sai dai har yanzu, an ki a bayyana wa jama'a abin da ke damun tsohon shugaban kasar.

Buhari ya jima bai Najeriya ba

A lokacin da aka gudanar da shagulgulan bikin cika shekaru 50 na ƙungiyar ECOWAS da aka gudanar a Legas ranar 28 ga Mayu, tsohon shugaba Buhari bai halarci zaman ba.

Kara karanta wannan

ADC: Atiku ya fara kokarin jawo jagorori zuwa tafiyar fatattakar APC a 2027

A cikin wata wasiƙa da ya aika wa Shugaba Bola Tinubu, Buhari ya bayyana cewa rashin halartar sa taron ya samo asali ne saboda duba lafiyarsa da ake yi a ƙasar Birtaniya.

Tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari
Buhari ya sha fama da jinya a Landan Hoto: Muhammadu Buhari
Source: Facebook

Amma ya aika wasika ga jagororin taron ta hannun Bola Tinubu, inda ya bayyana cewa:

“Kamar yadda ka sani, ina Birtaniya a halin yanzu ana duba lafiyar ta kamar yadda nake yi akai-akai, don haka ba zan iya halartar wannan taro na tarihi ba.”

Ko a ranar 1 ga Mayu, wani hoto da ya nuna tsohon shugaban hukumar EFCC, Abdulrasheed Bawa, tare da Buhari ya bayyana a yanar gizo.

Rahoton ya ce Bawa ya kai masa ziyara a London, sai dai ba a bayyana manufar ziyarar ba.

Garba Shehu: 'Buhari ba ya karbar cin hanci'

A wani labarin, mun wallafa cewa Mai magana da yawun tsohon shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, Garba Shehu, ya ce Muhammadu Buhari ya kammala mulki a cikin mutunci.

Ya bayyana cewa tsohon shugaban kasar ya shahara wajen gaskiya da amana, kuma har ya bar mulkin Najeriya bai karbi cin hanci daga hannun kowa ba.

A bayanin da ya yi, wanda ya ce na kunshe a cikin littafinsa, ya ya yi bayanin yadda ya gudanar da aikinsa a matsayin mai magana da yawun shugaban kasa.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng