2027: INEC za Ta Fito da Ka'idojin da Suka Shafi Duba Sakamakon Zabe a Najeriya

2027: INEC za Ta Fito da Ka'idojin da Suka Shafi Duba Sakamakon Zabe a Najeriya

  • Shugaban hukumar INEC, Farfesa Mahmood Yakubu ya ce za a ƙara fitar da ƙa’idoji don sake nazari da tantance sakamakon zaɓe
  • Ya bayyana hakan ne a wani taron kwamishinonin zaɓe na jihohi da aka gudanar a Abuja a wani ɓangare na shirin babban zaɓen 2027
  • Legit Hausa ta gano cewa hukumar INEC ta ce za ta wallafa ƙa’idojin a shafinta na yanar gizo tare da bayani ga jama'a idan ta samar da su

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Abuja, FCT - Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC) ta bayyana shirinta na fitar da sababbin ƙa’idoji da za su jagoranci yadda za a sake tantance sakamakon zaɓe.

Shugaban hukumar, Farfesa Mahmood Yakubu, ne ya bayyana hakan yayin taron kwana biyu da kwamishinonin zaɓe na jihohi (RECs) a birnin tarayya Abuja a ranar Litinin, 1 ga Yuli, 2025.

Kara karanta wannan

'Shirin ɗaukar Kwankwaso a matsayin abokin takarar Tinubu a 2027 ya fara ƙarfi'

Shugaban Hukumar INEC, Mahmood Yakubu.
Shugaban Hukumar INEC, Mahmood Yakubu. Hoto: INEC Nigeria
Source: Facebook

BBC Hausa ta wallafa cewa Mahmood Yakubu ya ce ƙa’idojin za su zama ƙarin bayani da jagora ga Sashe na 65 na dokar zaɓe ta 2022.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sauyin da INEC za ta yi kan sakamakon zabe

Shugaban INEC ya ce sababbin ƙa’idojin za su nuna yadda za a yi amfani da Sashe na 65 na dokar zaɓe, inda hukumar ke da hurumin nazari da sake tantance sakamako idan aka samu takaddama.

A cewar Farfesa Yakubu, wasu na fassara wannan sashe ta wata hanya da ba daidai ba, hakan yasa hukumar ke shirin fitar da ƙa’idoji don bayyana yadda aikin ke gudana a fili.

Punch ta wallafa cewa ya ce INEC ta ce:

“Da zarar hukumar ta yanke hukunci, watakila tun cikin wannan mako, za mu wallafa ƙarin ƙa’idoji a shafukanmu na yanar gizo da sauran hanyoyin sadarwa domin jama’a su sani.”

INEC na cigaba da haɗa kai da masana

Kara karanta wannan

INEC za ta gudanar da zaɓen cike gurbi a Kano da jihohi 11, an ba jam'iyyu umarni

Mahmood Yakubu ya ce hukumar ta riga ta gana da shugabannin jam’iyyu, kungiyoyin fararen hula, jami’an tsaro da ’yan jarida domin samun haɗin kai wajen gudanar da zaɓe mai inganci.

Ya kuma tabbatar da cewa dukkan jihohin ƙasar nan da Abuja yanzu suna da kwamishinonin zaɓe (RECs) da ke da cikakken iko na gudanar da ayyuka bisa tsarin doka.

Hukumar ta ce ƙa’idojin za su taimaka wajen gina amincewa da sahihancin tsarin zaɓe, tare da fayyace matakai da hanyoyin da ake bi idan aka samu korafi ko rashin fahimta kan sakamakon zaɓe.

INEC na shirin gudanar da zabe a jihohi
INEC na shirin gudanar da zabe a jihohi. Hoto: INEC Nigeria
Source: Twitter

Zaɓuka 5 da hukumar INEC za ta yi

Farfesa Mahmood Yakubu ya bayyana cewa INEC na shirin gudanar da zaɓuka guda biyar a cikin wata 13 masu zuwa, ciki har da zaɓen gwamna na Anambra da na Ekiti da Osun.

INEC ta jaddada cewa bin doka da oda ne za su tabbatar da sahihanci da amincewa da duk wani zaɓe da za a gudanar.

INEC: 'Yan adawa sun nemi kafa ADA

A wani rahoton, kun ji cewa 'yan adawa sun rubutawa hukumar INEC domin yi musu rajistar sabuwar jam'iyya.

Kara karanta wannan

Dalla dalla: Abubuwan da ake buƙata wajen kafa sabuwar jam'iyyar siyasa a Najeriya

Daya daga cikin jagororin 'yan adawa a Najeriya, Nasir El-Rufa'i na cikin mutanen da suke gaba gaba wajen samar da jam'iyyar ADA.

Ana hasashen cewa 'yan adawa za su yi amfani da ADA ne wajen yaki da APC da shugaba Bola Ahmed Tinubu a zaben 2027.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng