Ana tsaka da Korar 'Yan Ta'adda, Sun Jikkata Jami'in Dan Sanda a Katsina
- Wasu da ake zargin 'yan bindiga ne sun kai hari kan sansanin tsaron C a karamar hukumar Kankia a jihar Katsina da cikin dare
- Jami'an tsaro sun yi tsayin daka, aka yi musayar wuta mai zafi ta tilasta wa ‘yan bindigar janyewa daga harin da suka kai babu shiri
- A yayin gumurzu da maharan, jami’in da ke kula da ofishin ‘yan sanda na Rimaye, ASP Shola Odenkule, ya samu rauni a sassan jikinsa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kano – Dakarun tsaro sun dakile wani yunkurin harin 'yan bindiga da suka kai a jihar Katsina bayan an shafe tsawon lokaci ana fafatawa.
Rahotanni sun bayyana cewa 'yan bindiga sun kai hari ne a sansanin jami'an tsaron sa ido da ke kauyen Rimaye, karamar hukumar Kankia ta jihar Katsina.

Source: Facebook
Zagazola Makama ya wallafa a shafinsa na X cewa harin ya faru ne da misalin karfe 12:30 na dare a ranar 30 ga watan Yuni 2025.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
'Yan ta'adda sun kai hari aKatsina
Bayanan sun nuna cewa wasu da ake zargin 'yan bindiga ne suka kutsa sansanin da nufin kwace shi daga hannun jami’an tsaro.
Majiyoyin tsaro sun ce da zaran suka samu labarin harin, sai suka aika da tawaga ta musamman zuwa wurin, inda suka yi artabu da maharan.
Dakarun tsaron sun tilasta wa 'yan bindigar janyewa bayan musayar wuta mai tsanani, inda jam'an suka nuna harumta.
Rahotanni sun ce akwai wadanda suka ji rauni daga bangaren 'yan bindigar, amma ba a bayyana adadinsu ba.
'Yan sanda na samun nasara a Katsina
Rahotanni daga baya-bayan nan na nuna cewa rundunar ƴan sandan jihar Katsina sun yi nasarar daƙile wani hari da ƴan bindiga ke kai wa.
A harin da suka kai a dajin Kwari Manaja da ke cikin ƙaramar hukumar Sabuwa, an ceto wasu manoma guda shida da aka sace a lokacin.

Source: Facebook
Rahoton ya nuna cewa rundunar ƴan sanda ta dakile harin ne a ranar Asabar, 21 ga Yuni, da misalin ƙarfe 5:41 na yamma, lokacin da suka farmaki manoma.
'Yan sanda sun ji rauni a Katsina
A yayin musayar wutar, jami’in da ke kula da ofishin ‘yan sanda na Rimaye, ASP Shola Odenkule, ya samu raunin harbin bindiga a ƙafarsa ta dama.
Rahotanni sun ce Odenkule ya kuma samu raunuka a kansa da hannunsa na dama yayin artabun da aka gwabza.
An garzaya da shi zuwa cibiyar kula da lafiya ta farko da ke Rimaye (PHC), inda aka ba shi kulawar likita tare da kwantar da shi domin karin bincike da kulawa.
Yan bindiga sun farmaki kauyen Katsina
A wani labarin, kun ji cewa al'ummar jihar Katsina na cikin firgici da tsoro bayan wani hari da 'yan bindiga suka kai a wasu sassan jihar, lamarin da ya haifar cece-kuce.
Rahotanni daga majiyoyi masu tushe sun tabbatar da cewa 'yan bindigar sun kwace iko da wasu yankuna na karamar hukumar Kankara a cikin ruwan sanyi.
Wasu bayanai da ke yawo sun nuna cewa miyagun sun karbe ikon karamar hukumar gaba ɗaya, kodayake hukumomi sun ce ba haka lamarin ya ke ba.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


