Rigima tsakanin Malamai: An Tsare Malamar Musulunci a Gidan Kaso kan Bata Suna

Rigima tsakanin Malamai: An Tsare Malamar Musulunci a Gidan Kaso kan Bata Suna

  • An tura wata shahararriyar malamar addinin Musulunci daga Ibadan, Alhaja Kafilat Kaola gidan gyaran hali na Oke Kura a Ilorin, Jihar Kwara
  • Kaola na fuskantar tuhuma kan batanci da take yi wa wani malami, Alhaji Taofeek Akeugbagold, inda ta ce shi boka ne kuma mutane su guje shi
  • Lauyan Akeugbagold ya gabatar da bidiyo inda Kaola ke zagin alkalai, don haka kotu ta ki bayar da beli, ta tura ta kurkuku har 17 ga Yuli

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Ilorin, Kwara - An tsare wata malamar addinin Musulunci da ke Ibadan, Alhaja Kafilat Kaola kan bata sunan wani malami a jihar Kwara.

Majiyoyi sun tabbatar da cewa an tura ta gidan gyaran hali na Oke Kura da ke Ilorin a Jihar da ke Arewacin Najeriya.

Kara karanta wannan

Ana tsaka da korar 'yan ta'adda, sun jikkata jami'in dan sanda a Katsina

An tura malamar Musulunci gidan kaso
Malamar Musulunci ta kwana a gidan kaso kan zargin batanci. Hoto: Igbiyanju The - Effort.
Source: Facebook

Zargin da ya jefa malama a gidan kaso

An umurci Kaola da ta zauna a gidan gyaran hali daga kotun 'Upper Area' da ke Garin Ganmo, cewar rahoton Punch.

Ana zargin malamar kan batanci ga wani malami, Alhaji Taofeek Akeugbagold, wanda shi kuma ya shigar da kara.

A baya-bayan nan, Kaola ta fito karara tana zargin Akeugbagold da cewa shi boka ne kuma mutanen da ke neman ilimin addini su guje shi.

Akeugbagold ya musanta zargin, yana mai cewa:

“Ba zan shiga gardama da ita ba, sai ta kawo hujja saboda wannan zargi ya bata min suna.”

Ya ce batanci da aka yi masa ya shafi kasuwancinsa da kuma mutuncinsa, kuma manyan malamai sun shiga tsakani amma ba zai yafewa Kaola ba sai ta wanke shi.

Malamar Musulunci ta jefa kanta a matsala
An tsare malamar Musulunci a gidan kaso kan ɓata suna. Hoto: Legit.
Source: Original

Yadda zaman kotu ta kaya a Kwara

A lokacin zaman kotu ranar Litinin, lauyan Kaola ya roki kotu ta bayar da belinta saboda matsayinta a idon jama’a da kuma cewa ba za ta tsere ba, Tribune ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Kaduna: Ƴan bindiga sun shammaci mutane da tsakar dare, sun ɗauke basarake

Amma lauyan wanda ake kara, Ajasa Ademola, ya ki amincewa da bukatar, yana mai cewa Kaola bata cancanci irin wannan beli ba saboda wani laifi makamancin haka.

Ajasa ya gabatar da bidiyon da ake yadawa inda Kaola ke zagin wani alkalin kotu da lauyan wani shari’ar baya da ta taba tsoma baki a cikin lamarin.

Ya ce:

“Wanda ke zagin alkalan kotu a bainar jama’a bai cancanci beli ba.”

Bayan sauraron hujjojin daga bangarorin biyu, alkalin kotu ya yanke hukuncin tura Kaola gidan gyaran hali na Oke Kura har zuwa ranar da za a ci gaba da shari’a, 17 ga Yuli, 2025.

Malami yana zargin ana yawan bautar gumaka

Kun ji cewa wani limamin Musulunci, Dr Sharafdeen Gbadebo Raji, ya fusata mutane da maganganunsa kan zargin bautar gumaka a Arewa.

Raji ya tambayi dalibansa su lissafa al’adu marasa ɗa'a da ba su bin addini a jihar Kwara, inda suka lissafo su da dama wanda hakan ya jawo maganganu a jihar.

Mutane da dama daga Ilorin sun fusata, suna cewa ya bata sunan garinsu, suna neman a kai shi kotu saboda zagin jama'a gaba ɗaya.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.