Dantata Ya Yi wa Aminu Ado Bayero Wasiyya kan Jana'izarsa, Sarki Ya Tafi Madina

Dantata Ya Yi wa Aminu Ado Bayero Wasiyya kan Jana'izarsa, Sarki Ya Tafi Madina

  • Sarkin Kano na 15, Aminu Ado Bayero, ya isa Saudiyya domin halartar jana’izar Alhaji Aminu Dantata da ya rasu a Dubai
  • Dantata ya roƙi Aminu Ado Bayero tun kafin rasuwarsa da ya kasance cikin masu masa sutura idan ya riga mu gidan gaskiya
  • A daya bangaren, gwamna Abba Kabir Yusuf ya jagoranci tawagar gwamnati da ta hada da Muhammadu Sanusi II zuwa Madina

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Kano - Sarkin Kano na 15, Alhaji Aminu Ado Bayero, ya tashi daga Najeriya zuwa ƙasar Saudiyya domin halartar jana’izar Alhaji Aminu Alhassan Dantata.

Legit ta rahoto cewa Alhaji Aminu Alhassan Dantata ya rasu a Dubai ranar Asabar yana da shekara 94.

Aminu Ado Bayero tare da marigayi Dantata
Aminu Ado Bayero tare da marigayi Dantata. Hoto: Masarautar Kano
Source: Facebook

Masarautar Kano ta wallafa a X cewa Aminu Ado Bayero na cikin mutanen da Aminu Dantata ya yi wa wasiyya wajen masa jana'iza da sutura.

Kara karanta wannan

A karo na 2, an ƙara ɗaga jana'izar fitaccen ɗan kasuwa, Alhaji Aminu Ɗantata a Madina

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A wata hira da jaridar Punch ta yi da mai magana da yawun Aminu Ado, Abubakar Balarabe Kofar Naisa, ya tabbatar da tafiyar da cewa Dantata da kansa ya yi wasiyyar.

Aminu Ado ya tafi Madina jana'izar Dantata

Duk da yake gwamnatin Kano ƙarƙashin Abba Kabir Yusuf ta tura tawaga tare da Muhammadu Sanusi II zuwa jana’izar, Aminu Ado Bayero ya tafi da manyan masu mukaman gargajiya.

Tawagar Bayero ta hada da manyan jami’an fada kamar Sarkin Dawaki, Aminu Babba Dan’agundi da kuma ɗan majalisar tarayya mai wakiltar Doguwa/Tudun Wada, Hon. Alhassan Ado Doguwa.

Rahotanni sun ce wannan tafiya da Aminu Ado Bayero ya yi na nuna girmamawa ne ga Alhaji Aminu Dantata, wanda ya yi tarayya da mahaifinsa Ado Bayero a cikin huldar mutunci da alaka ta kusa.

An yi sallar jana’izar Dantata a Kano

Rahotanni sun nuna cewa an gudanar da sallar jana’iza ba tare da gawa ba ga mamacin a Kano ranar Asabar a Masallacin Umar Bin Khattab.

Kara karanta wannan

Dantata: Dangote ya karbi tawagar gwamnatin Kano da Jigawa a Madina

Shugaban majalisar malamai ta jihar Kano, Sheikh Ibrahim Khalil ne ya jagoranci sallar, inda daruruwan jama’a suka halarta domin yin addu’a ga marigayin.

Dantata ya rasu ne a Abu Dhabi, kuma ana ganin rasuwarsa babban gibi ne ga harkar kasuwanci, addini da taimako a Arewacin Najeriya.

Sheikh Ibrahim Khalil da ya jagoranci jana'izar Danatata a Kano
Sheikh Ibrahim Khalil da ya jagoranci jana'izar Danatata a Kano. Hoto: Khalili Network
Source: UGC

Aminu Ado Bayero zai hadu da Sanusi II

Majiyoyi daga bangarorin sarautar Kano sun tabbatar da cewa Aminu Ado Bayero da Sanusi II za su gana da iyalan Dantata domin girmama marigayin.

Wani mai sharhi a kan lamuran sarauta, Mustapha Isa Kwaru, ya bayyana haduwar sarakunan biyu a Saudiyya a matsayin abin tarihi da alamar hadin kai duk da sabanin da ke kasa.

An daga jana'izar Dantata zuwa Talata

A wani rahoton, kun ji cewa gwamnatin Najeriya ta sanar da canza rana da lokacin jana'izar marigayi Aminu Alhassan Dantata a Madina.

Rahoton da Legit Hausa ta samu ya nuna cewa a karon farko an sanar da cewa za a yi jana'izar ne a ranar Litinin amma aka daga zuwa Talata.

Ministan yada labarai da wayar da kan al'umma, Mohammed Idris ne ya bayyana haka ga manena labarai daga kasar Saudiyya.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng