Gwamnan Kwara Ya Fusata, Ya Gurfanar da Tsohon Ɗan Majalisa da Ɗan Uwansa a Kotu
- Gwamnan jihar Kwara ya maka Moshood Mustapha da ɗan'uwansa a kotu bisa zargin tayar da zaune tsaye da yaɗa bidiyon ɓatanci
- An gurfanar da su be a ranar Litinin a Ilorin, ammma sun musanta tuhume-tuhumen, inda alkali ya bayar da su beli a kan N5m
- Tuhume-tuhumen sun haɗa da haɗin baki don ƙirƙira da yaɗa bidiyon ɓatanci, wanda zai iya tunzura jama'a kan gwamnan jihar
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Kwara - Gwamna Abdulrahman Abdulrazaq na jihar Kwara ya maka tsohon ɗan tarayya kuma ɗan kasuwa, Moshood Mustapha, tare da ɗan'uwansa, Bolakale Mustapha, a kotu.
Gwamnan ya maka ƴan uwan ne bisa zargin tayar da zaune tsaye, yin bayanan ƙarya, da kuma wallafawa da yaɗa bidiyo a yanar gizo wanda zai iya tunzura jama'a a kan gwamnan.

Source: Twitter
Gwamna ya gurfanar da 'yan uwa a kotu
An gurfanar da mutanen biyu a gaban Mai Shari'a Muhammed Abdulgafar na babbar kotun jiha a ranar Litinin, 30 ga Yuni, kamar yadda Channels TV ta ruwaito.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sai dai, sun musanta tuhume-tuhume biyar da ake yi musu game da bidiyon da gwamnan ya ce zai iya jawo mutane su yi masa ko gwamnatinsa bore.
Mai Shari'a Muhammed Abdulgafar ya ba da belin wadanda ake tuhumar a kan kuɗi Naira miliyan biyar, yayin da aka dage zaman zuwa 18 ga Yuli, 2025, don fara shari'a.
Wannan shari'ar ta bambanta domin daya daga cikin wadanda ake tuhuma dan jam'iyyar APC ne kafin ya samu saɓani da gwamnan, kuma jama'a na jiran ganin yadda shari'ar za ta kaya.
Bayanan tuhume-tuhumen da ake yi musu
A cikin takardar tuhuma mai lamba KWS/85c/25, tsakanin gwamnatin jihar Kwara da waɗanda ake tuhuma, an zargi mutanen biyu da laifuka biyar.
Jaridar Tribune ta rahoto wasu sassa na tuhume-tuhumen suna cewa:
"Cewa ku Bolakale Mustapha da Moshood Mustapha wani lokaci a watan Oktoba, 2024 a Ilorin, jihar Kwara kun haɗa baki a tsakaninku don aikata haramtaccen aiki, watau; kun haɗa baki don fito da wani bidiyo, dora shi a yanar gizo da kuma yada shi.

Source: Twitter
"Wanda yin hakan zai iya haifar da rashin zaman lafiya ko tayar da hankalin jama'a kuma ta haka kuka aikata laifin da za a iya hukuntawa a ƙarƙashin Sashe na 97 na Dokar Laifuffuka, CAP. P4, Dokokin jihar Kwara."
"Cewa kai Moshood Mustapha a ranar 6 ga Oktoba, 2024 ko kusan haka a Ilorin, jihar Kwara ka aikata haramtaccen aiki, watau; ka samar, ka wallafa kuma ka yada bidiyo na tsawon minti biyar da daƙiƙa arba'in da ɗaya (5:41).
"Bidiyon yana ɗauke da kalamai na cin mutunci, zagi da baƙar magana ga gwamnan jihar Kwara, Malam AbdulRahman AbdulRazaq ta hanyar da za ta iya tunzura jama'a a kan gwamnatin Kwara, kuma mai yiwuwa, za ta iya haifar da rashin zaman lafiyar jama'a a jihar.

Kara karanta wannan
An taso Firaministan Isra'ila a gaba bayan gama yaƙi da Iran, ya fara roƙon arziƙi
"Da wannan ka aikata laifi da za a iya hukuntawa a ƙarƙashin Sashe na 399 na Dokar Laifuka, CAP. P4, Dokokin jihar Kwara."
'Abin da sojoji ke bukata' - Gwamna Abdulrazaq
A wani labarin, mun ruwaito cewa, gwamnan Kwara ya tabo batun rashin tsaro da ke damun ƙasar tsawon shekaru ba tare da samun mafita ta gaskiya ba.
Abdulrahman Abdulrazaq ya jaddada cewa ba wai siyan makamai kaɗai ba ne mafita, sai an ɗauki matakai na cikakken sauyi a harkar sojin Najeriya.
Ya ce dole ne a samar da kayayyakin more rayuwa domin sauƙaƙa wa sojoji aiki, su samu kwarin gwiwa wajen yaƙi da ‘yan ta’adda.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

