An Fatattaki Shugabannin PDP daga Sakatariyar Jam'iyyar, an Canja Wurin Taro
- Jami'an tsaro sun hana taron kwamitin amintattu na PDP a hedikwatar jam'iyyar da ke Abuja, inda suka kore su daga zauren taron
- An umurci jami'an tsaro da su tabbatar babu wani taro da ya gudana a hedikwatar, a daidai lokacin da rikicin PDP ke ƙara tsananta
- Sai dai, jam'iyyar PDP ta canja wurin taron BoT din daga hedikwatar ta zuwa Cibiyar Yar'Adua a Abuja saboda abin da ya faru
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - Jami'an tsaro da aka jibge a sakatariyar PDP da ke Abuja sun hana mambobin kwamitin amintattu (BoT) gudanar da taron su a hedikwatar jam'iyyar.
Yayin rubuta wannan rahoton, an ga wasu daga cikin mambobin suna tattauna halin da ake ciki a hankali, bayan jami'an tsaro sun kore su daga dakin taro.

Source: Twitter
Jami'an tsaro sun kori BoT daga sakatariyar PDP
Daily Trust ta tattaro cewa an umurci jami'an tsaro da su tabbatar babu wani taro da zai gudana a hedikwatar jam'iyyar.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Jami'an, waɗanda suke da yawa, sun mamaye zauren NEC inda ake sa ran za a gudanar da taron kuma suka umurci waɗanda ke wurin da su fice.
Wakilin jaridar ya ji wani babban jami'i yana gaya wa wasu daga cikin jami'an tsaron da ke ƙarƙashinsa cewa su tabbatar kowa ya bar dakin taron.
Ya ba da umarni cewa:
"Ku tabbatar babu kowa a zauren can. Wannan umarni ne. Na ji akwai wani zaure a sama. Ku tabbatar babu wanda ke taro a can."
Rikicin cikin gida ya yi kamari a PDP
PDP ta dade tana fama da rikici tun bayan zaɓen fitar da gwani na shugaban ƙasa na zaɓen 2023, inda kusan dukkanin sassan jam'iyyar suka kasu kashi biyu.
Rikicin na baya-bayan nan kan wanda shine sahihin sakataren jam'iyyar na kasa ya haifar da rudani tsakanin shugabannnin jam'iyyar a matakin kasa.
Muƙaddashin shugaban jam'iyyar na kasa, Ambasada Umar Damagum, da mataimakin shugaban jam'iyyar na kasa na Kudu, Taofeak Arapaja, na jagorantar tsagi daban-daban na NWC.
PDP ta canja wurin taron kwamitin amintattu
Bayan abubuwan da suka faru a sakatariyar PDP ta kasa, jam'iyyar ta fitar da sanarwa ta musamman ta sanar da sauya wurin da za a gudanar da taron.

Source: Twitter
Sanarwar ta ce an canza wurin taron kwamitin amintattu (BoT) na jam'iyyar wanda aka shirya gudanarwa da karfe 10:00 na safiyar Litinin a sakatariyar jam'iyyar ta ƙasa da ke Abuja.
Sanarwar ta da aka wallafa a shafin jam'iyyar na X ta ce an mayar da taron ne zuwa Cibiyar Yar'Adua, dake yankin Central Business District, Abuja, tana mai cewa:
"A saboda haka, jam'iyyar ta bukaci dukkain mambobin BoT da su garzaya sabon wurin taron."
Karanta sanarwar a kasa:
Jami'an tsaro sun mamaye hedikwatar PDP
Tun da fari, mun ruwaito cewa, ‘yan sanda sun mamaye hedikwatar jam’iyyar PDP da ke Abuja, yayin da takaddama game da taron NEC ke ƙara ƙamari.
An hana mambobi, ma’aikatan jam’iyyar da ‘yan jarida shiga harabar sakatariyar. Wasu rahotanni na cewa an tura ‘yan sandan ne don dakile taron.
Sai dai PDP ta jaddada cewa taron NEC na karo na 100 zai gudana kamar yadda aka tsara, tana kira ga ‘ya’yanta su yi watsi da jita-jita.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


