Sanata Natasha Ta Sake Shiga Matsala, an Gurfanar da Ita gaban Kotu kan Tuhuma 6
- An gurfanar da Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan a kotu bisa tuhume-tuhume shida na ɓata suna a ƙarƙashin Dokar Laifuffukan Intanet
- An zarge ta da cin zarafin Godswill Akpabio da Yahaya Bello, amma ta musanta dukkanin tuhume-tuhumen a gaban babbar kotun tarayya
- Magoya baya da ƙungiyoyin mata sun soki gwamnati, suna zargin ana ƙoƙarin rufe bakin sanatar ne, da nuna damuwa kan tsarin shari'ar
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - An gurfanar da Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan, mai wakiltar Kogi ta Tsakiya a majalisar dattawa, a gaban babbar kotun tarayya da ke Abuja.
An gurfanar da 'yar majalisar dattawan ne a ranar Litinin kan tuhume-tuhume shida a ƙarƙashin Dokar Laifuffukan Intanet ta Najeriya.

Source: Twitter
An sake gurfanar da Sanata Natasha Akpoti
Ana zargin Sanata Natasha ta ɓata sunan shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio, da tsohon gwamnan Kogi, Yahaya Bello, a cewar rahoton The Cable.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An rahoto cewa Sanata Natasha ta isa babbar kotun tarayya ta Abuja tare da mijinta, Emmanuel Uduaghan; Aisha Yesufu; da magoya bayanta.
A yayin da aka karanta mata tuhume-tuhumen da ake yi mata, Sanata Natasha ta musanta dukkanin tuhume-tuhumen shida a gaban Mai Shari’a Mohammed Umar.
An gabatar da sababbin tuhume-tuhumen ne a ƙarƙashin dokar hana laifuffuka da ba da kariya ta intanet.
Tuhume-tuhumen, da aka shigar, sun samo asali ne daga kalaman da aka ce Natasha ta yi a tsakanin 1 ga Afrilu zuwa 14 ga Afrilu, 2025, a lokacin da take hira da hira da Channels TV.
An taba gurfanar da Natasha kan tuhume-tuhume 3
A yayin hirar, an ce Natasha ta zargi Akpabio da Bello da kulla makircin kashe ta, wanda ya saɓa wa sashe na 24(1)(b) da 24(2)(c) na dokar.
Wannan ya biyo bayan shari'ar tuhume-tuhume uku na ɓata suna da ake yi wa Sanata Natasha a gaban Mai Shari'a Chizoba Orji na babbar kotun Abuja, inda aka gurfanar da ita a ranar 19 ga Yuni, 2025.
An zargi Natasha da alaƙanta Akpabio da safarar sassan jikin dan Adam a shari'ar kisan Iniubong Umoren a ranar 27 ga Maris, 2025, da kuma jawabinta na ranar 3 ga Afrilu, 2025.

Source: Facebook
Yesufu da kungiyoyi sun caccaki gwamnati
Kotun ta bayar da belin Natasha a kan N50m tare da kawo wanda zai tsaya mata, da ke da kadara a Abuja, tare da dage shari'ar zuwa 23 ga Satumba, 2025.
Masana shari'a sun soki gwamnatin tarayya saboda shigar da tuhume-tuhume kusan iri ɗaya a kotuna biyu, suna mai nuna damuwa kan 'rarraba kotunan' don cin zarafin Sanata Natasha.
Magoya bayan Natasha irin su Yesufu da ƙungiyoyin mata kamar Womanifesto sun yi Allah wadai da tuhume-tuhumen da kuma zargin cewa ana ƙoƙarin rufe bakin sanatar ne.
Akpabio: Sanata Natasha ta saki sabon bidiyo
A wani labarin, mun ruwaito cewa, Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan, ta tona asirin yadda ake gudanar da wasu ayyuka cikin rashin gaskiya a majalisar dattawa.
A cewarta, ta fahimci cewa "rahoton ayyukan kwamitoci" yana da wata ma'ana ta daban a Majalisar ne kawai bayan da ta gabatar da nata rahoton.
Sanatar ta zargi shugaban majalisar, Godswill Akpabio, da karɓar kuɗi daga kwamitoci a kai a kai, wanda ta ce yana nuna rashin gaskiya da rashin tsabta a tafiyar da harkokin majalisa.
Asali: Legit.ng

