Wata Sabuwa: Ɗan Ƙasar Isra'ila Ya Yanke Jiki Ya Faɗi a Otel ɗin Abuja, Ya Mutu
- Wani ɗan ƙasar Isra'ila, Avi Warshaviak, ya rasu a ranar 28 ga Yuni, 2025, bayan ya fadi a Otel ɗin Corinthia Villa da ke Garki, Abuja
- Likitoci sun tabbatar da mutuwar Avi Warshaviak a babban asibitin Asokoro, amma har yanzu ba a san musabbabin mutuwarsa ba
- 'Yan sanda sun fara bincike tare da tuntuɓar ofishin jakadancin Isra'ila don ba da goyon bayan diflomasiyya da zurfafa bincike
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - A ranar 28 ga Yunin, 2025, wani ɗan ƙasar Isra'ila, Avi Warshaviak, ya rasu bayan ya yanke jiki ya fadi a Otel ɗin Corinthia Villa da ke yankin Garki a Abuja.
Avi Warshaviak yana tare da matarsa lokacin da ya kamu da rashin lafiya mai tsanani a lokaci guda, da misalin karfe 9:51 na safiyar ranar.

Source: Getty Images
Ɗan ƙasar Isra'ila ya mutu a Abuja
Rahoton da Zagazola Makama ya wallafa a shafinsa na X ya nuna cewa an tabbatar da mutuwar Avi Warshaviak a babban asibitin Asokoro.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Har yanzu ba a bayyana musabbabin rashin lafiyarsa da ta yi ajalinsa ba, amma ana sa ran samun karin bayani idan aka kammala bincike.
Babban jami'in tsaro na otel ɗin, Okorie Emmanuel, ya kai rahoton faruwar lamarin ga hedikwatar rundunar 'yan sanda ta Garki da misalin karfe 11:23 na safe.
'Yan sanda sun ziyarci otel ɗin da asibitin, inda suka tattara bayanai yayin da aka rahoto cewa an kai gawar Warshaviak zuwa ɗakin ajiye gawarwaki na asibitin don a binciken musabbabin mutuwarsa.
An tuntubi ofishin jakadancin Isra'ila
Hukumomi suna ƙoƙarin tuntuɓar ofishin jakadancin Isra'ila a Najeriya, wanda ke a 12 Mary Slessor, Asokoro, don gudanar da matakan diflomasiyya da kuma sanar da waɗanda abin ya shafa.
Ofishin jakadancin, wanda za a iya samunsa a 9-460-5541 ko info@abuja.mfa.gov.il, yana iya ba da taimako wajen bincike tare da jigilar gawar zuwa Isra'ila a irin wannan yanayi, inji rahoton.
Babu wani rahoto na kunbiya-kunbiya a mutuwar, amma ana sa ran za a gudanar da bincike kan gawar domin gano dalilin mutuwar Warshaviak.

Source: Twitter
An kashe ƴan ƙasar Isra'ila a Amurka
Lamarin ya ja hankali sosai saboda la'akari da kasar da Warshaviak ya fito, musamman a idan aka kalli abubuwan da suka faru a kwanan nan da suka shafi ƴan ƙasar Isra'ila a wasu sassan duniya.
A watan Mayu 2025, aka kashe ma'aikatan ofishin jakadancin Isra'ila biyu a Washington, D.C., a cewar wani rahoton BBC.
Duk da cewa kisan da aka yi a Amurka ba shi da alaƙa da mutuwar Warshaviak, amma yana nuna yadda lamarin ya yi zafi game da ƴan ƙasar Isra'ila a ƙasashen waje.
Bam ya tarwatse da sojojin Isra'ila
A wani labarin, mun ruwaito cewa, Isra'ila ta sanar da mutuwar sojojinta bakwai a Zirin Gaza bayan wani bam mai karfi ya tarwatse a motar da suke ciki.
Harin da Hamas ta ɗauki alhakinsa ya zama ɗaya daga cikin mafi muni ga sojojin Isra'ila a rikicin Gaza tun bayan barkewar fadan a 2023.
Hukumar sojin Isra'ila ta ruwaito cewa, akalla sojojinta 860 suka mutu tun bayan barkewar yaƙinta da Gaza, yayin da dubunnai suka jikkata.
Asali: Legit.ng


