Najeriya Ta girgiza: Tinubu da Atiku Sun Yi Jimamin Rasuwar Aminu Dantata

Najeriya Ta girgiza: Tinubu da Atiku Sun Yi Jimamin Rasuwar Aminu Dantata

  • Shugaba Bola Tinubu ya bayyana rasuwar Alhaji Aminu Dantata a matsayin babban rashi ga ƙasa, yana mai yabon gudummawar da ya bayar
  • Dantata ya rasu yana da shekara 94, kuma ya kasance ɗaya daga cikin manyan ’yan kasuwa masu taimakon al'umma a Najeriya
  • Atiku Abubakar ya bayyana Dantata a matsayin mutum mai kokarin kawo cigaba tare da mika ta’aziyya ga iyalansa da al’ummar Kano

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - A safiyar Asabar, 28 ga Yuni, 2025, Najeriya ta yi babban rashi da rasuwar ɗaya daga cikin dattawan ƙasa da shahararren ɗan kasuwa, Aminu Alhassan Dantata.

Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu da tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, sun bayyana jimaminsu kan wannan babban rashi na Alhaji Aminu Alhassan Dantata.

Kara karanta wannan

Tinubu ya sake ɗauko mutumin Buhari, ya ba shi babban muƙami a gwamnatinsa

Atiku da Atiku na gaisawa da Dantata
Atiku da Atiku na gaisawa da Dantata. Hoto: Atiku Abubakar|Bayo Onanuga
Source: Facebook

Shugaba Tinubu ya yabi gudunmawar da Dantata ya bayar ga ci gaban tattalin arziki da walwalar al’umma a sakon da Abdulaziz Abdulaziz ya wallafa a Facebook.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Dantata ya kasance mai sha'awar tallafawa al’umma a bangaren ilimi da inganta lafiya, tare da kasancewa jagora a harkar kasuwanci da shugabanci na gari.

Tinubu: “Mun rasa jarumin tattalin arziki”

A cikin sanarwar da mai ba shugaban ƙasa shawara kan harkokin yada labarai, Bayo Onanuga, ya fitar, Shugaba Tinubu ya bayyana cewa Najeriya ta yi babban rashi da rasuwar Alhaji Dantata.

Shugaban ya ce Dantata ba wai kawai babban ɗan kasuwa ba ne, har ma dattijo ne da ya kasance ginshikin zaman lafiya da cigaba a ƙasar.

Ya kara da cewa:

“Za mu ci gaba da tunawa da Alhaji Dantata saboda hazakarsa, juriyarsa, da sadaukarwarsa ga haɗin kan ƙasa ta hanyar harkokin kasuwanci da ayyukan jin ƙai."

Kara karanta wannan

Shekarar Hijira: Sarkin Musulmi ya yi magana kan rashin tsaro, yakin Iran da Isra'ila

Atiku: 'Ba za a manta da Dantata ba'

Tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, ya bayyana Dantata a matsayin jigo na ƙarshe daga cikin shuwagabannin da suka bunkasa ƙasa da riƙo da gaskiya.

A wata sanarwa da ya fitar X, Atiku ya ce:

“Alhaji Dantata ya kasance jigon zaman lafiya da tsari mai nagarta ga al’umma.
"Ta hanyar yin ayyukan alheri da jagoranci mai ma’ana, ya kafa tarihi a cikin zuciyar al’ummar Najeriya.”

Atiku ya mika ta’aziyyarsa ga iyalan Dantata, fadar masarautar Kano da kuma daukacin al’ummar Najeriya, yana mai roƙon Allah ya jikansa da rahama da ya karɓe shi cikin Aljannatul Firdaus.

Atiku ya yi ta'aziyyar rasuwar Dantata
Atiku ya yi ta'aziyyar rasuwar Dantata. Hoto: Hassan Mohammed
Source: Twitter

Rasuwar Alhaji Aminu Dantata ta janyo martani daga manyan ’yan siyasa da shugabanni daga sassa daban-daban na ƙasa, inda kowa ke yaba rayuwarsa da gudummawar da ya bayar.

Aminu Dantata ya taba fatan cikawa da imani

A wani rahoton, kun ji cewa Alhaji Aminu Dantata ya taba bayyana burinsa a rayuwa a shekara biyu da suka wuce.

Kara karanta wannan

An samu karin masu son a sauya Kashim, kungiyar APC na son Tinubu ya dauko Dogara

Dantata ya bayyana cewa yawanci mutanen da ya saba da su sun rasu kuma abin da yake fata shi ne cikawa da imani.

Dan kasuwar ya fadi haka ne yayin da mataimakin shugaban kasa, Sanata Kashim Shettima ya ziyarce shi a jihar Kano.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng